← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 84

Sashe 68

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya ta zaunar da ita ta fayyace mata komi dalla dalla akan auren da Safwan ya yi ba tare da saninta ba, sannan ta sanar da ita alfanun kaita Abujar da ta sa aka yi don kawai itama ta san minene rayuwa, Dije tasha kuka saboda kishin auren da ta ji ya yi, amman sannu a hankali Hajiya tana ta tausarta tare da nuna mata cewa ita ɗin tana da damar dawo da Mijinta hannunta don ba'a fita da komi ba, sannan ne hankalinta ya ɗan kwanta ta ji sanyi a ranta ta saki jikinta, sai dai duk lokacin da ta tuna da wata mace a tare da shi sai ta yi kuka a ɓoye.

Hajiya Mama ta saki jiki ta gyarewa Dijen Baffah ɗakinta tamkar kowace yarinya mai gata a wurin iyayenta, itama kanta ta fara gyarata ciki da bayanta lungu da saƙonta, don takanas ta nemo wata Mata ta dinka tsima Dijen tun tana jin daɗin karamcin har ta kai ta fara nuna gajiyawarta, dole Hajiya ta ce a dakatar da komi sannan aka koma gyara mata jiki Dilka halawa duka ba wanda ba'a yi mata ba, jikinta ya dawo smuth har wani sheƙi yake yi, ga fatarta hutu yasa ta murje ta cire baƙin ta zama chocolate color, ga gashinta Kuma da kullum yake ƙara cika masha ALLAH, shi ma ba ƙaramin gyara ya ke sha ba a hannun Matar, Fiddo kanta ba Dijen ta burgeta saboda ganin yanda gaba ɗaya ta sauya tamkar ba ƴar ƙauyen da ta sani ba, saboda ta zanzare ta zama wayayyi ƴar boko musamman yanzu da Safwan ya ƙara buɗe mata idanuwa da salon Soyayyarshi, amman duk da hakan ba wata magana mai tsawo da ke haɗasu, saboda ita kanta a yanzu jinta take yi dai dai da kowa, musamman idan ta tuno da ita ɓangaren Amarya take shiyasa ma ko kaɗan bata shiga shirgin Fiddon matuƙar ba dolen dole ce ta janyo ba.

Ana gobe su Safwan za su da wo ne Hajiya ta saka Aunty Ummi da su Surayya da sauran wasu ƴan uwa suka yi wa Dijen rakiya gidan angonta Safwan, zuciyarta cike da farin cikin ganin wannan rana mai cike da ɗinbin tarihi a rayuwarta, saboda tsabar murnar ganin muhallinta har da kukan farin ciki Dijen ta yi, musamman da ta kalli ko'ina sama da ƙasa gabas da yamma Kudu da Arewa taga uwar dukiyar da aka narka mata, ta yi sha'awar ina ma ace Inna da Baffah'nta da ƙawayenta su ma su zo su ga muhallinta, ta ruƙunkume Aunty Ummi sai kuka take cisga, Fiddo kam sai wani yatsine yatsine take yi zuciyarta cike da jin haushin kwashe masu dukiya da Hajiyar ta yi ta zube a ɗakin Dijen, a ranta ta ƙara tabbatar da cewa lalle ba ƙaramin asiri su Baffah su ka yi masu ba musamman ita da SAFWAN ɗin.

Surayya tana dariya zuciyarta cike da jin daɗi ta yi mata raɗa a kunne sai ga Dije ta sunne kai cike da kunya tana dariya, saboda cewar da ta yi

"Ba wani kuka yarinya gobe iwar haka har kin mance da mu kina ta Mijinki"

Haka suka tasata da wasa har ta ware tana mayarwa Surayya suna gidan har dare sannan aka barta da Husnah da wata dattijuwar da zata riƙa yi mata hidima, haka ta kwana cikin farin cikin dawowar Angonta masoyinta kuma Malaminta Muhammad Safwanu JABB'I YOLA.

Ayyururui Amarya ta ango🥳

Akafta😝

D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Ruwan sharhin da kuke ta bugawa akan book ɗin nan ba ƙaramin daɗi yake sakani ba, saboda haka ku ci gaba da fafatawa ni ma in ci gaba da sambaɗo maku labarai😉😂*

*Lamba ta 63*

Tunda sassafe Surayya ta zo suka shiga kitchen sunata hidimar ɗora abincin tarbon baƙi kala kala, ko da sha biyu na rana ta yi duk sun kammala abunda ake buƙata, Dije ta je ta sullo wankan da sai da ta ɓata lokaci sosai wajen wanke ko'ina lungu da saƙo na jikinta, tare da ɗimama kanta da turarukan wanka masu daɗin ƙamshi, waɗanda a hankali har sun fara bin jikinta saboda yanda take yawan amfani da su akai akai tun dawowarta Abuja.

Bayan ta yi SALLAHr azahar ne Surayya ta zauna ta tsara mata kwalliya cikin tsari irin na wayayyun yan birni, kafin ka ce me sai ga Dijen Baffah ta fito sharr! Abunta cikin wata rantsattsiyar shadda golden color har sheƙin maiƙo take yi, ga ɗinkin da aka watsawa shaddar na stone work shuwari stone sai walwalniya suke yi ta ko'ina idan ta motsa, sannan ga danƙareriyar sarƙarta ta gold da ta ƙara ƙawata kwalliyar, wadda Hajiya ta bata a matsayin kyautar suruka lokacin da za ta zuwa gidan mijinta, ta sha manyan awarwaro da agogo tare da Zoben azurfan da ke maƙale a yatsanta na biyu, wanda ya ƙara fito mata da zarazaran dogayen yatsunta da suka sha ƙunshin jan lalle masha ALLAH.

Dijen Baffah ta yi kyau iya kyau kamar ka saceta ka tsere saboda wankan ya hau jikinta sosai ya zauna, suka fito harabar gidan sai ɗaukar photuna suke yi ita da su Surayya da Husnah, Fiddo kam latsar wayarta kawai take yi saboda fushin da take yi na tilastata da Hajiya Mama ta yi akan sai ta zo gidan, don ta so ta yi zamanta acen gida tunda dole a cen ne zasu fara zuwa su ga Hajiyar sannan su yo nan gidan.

Shiyasa tunda ta zo ba wanda ta shiga sha'aninshi sai sabgoginta ta ke ita kaɗai, yanda ta share kowa haka duk cikinsu kowa ya shareta suna ta harkokinsu.

****

Malam Safwanu kam suna fitowa jirgi ya ja numfashi ya shaƙi iskan ƙasarshi ta Nageria da ƙarfi tare da lumshe ido ya kallo Amaryarshi da ke gefenshi cike da wani salon da shi kaɗai yasan ma'anar kallon, ganin haka ta ƙara maƙale hannunshi da take riƙe da shi tare da ɗora kanta a kafaɗarshi tana murmushin itama, don on ready ko da suka sauko direba yana airport ɗin yana jiran saukarsu, shiyasa ba tare da ɓata lokaci ba ya kwasosu suka nufo unguwarsu Hajiya Mama domin su fara gaisawa kafin su je cen gidan nasu, Zee haka kawai ta tsinci kanta da faɗuwar gaba tare da jin kwatakwata bata son zuwa gidansu Hajiya Mamar, saboda tunaninta ya tafi ne akan cewa Dijen tana gidan, sai dai har aka gama gaisawa da juna cikin farin ciki da ɗoki tare da murnar ganin juna bata hango ko mai kama da Dijen Baffahn ba, taji daɗi sosai a ranta saboda tunaninta har lokacin tana cen Makarantar da aka ce tana yi, shiyasa ta saki jiki sai wasar baki take yi anata gaggaisawa kafin su yi sallama da juna su fito gidan, tare da rakiyarsu Hajiyar da Aunty Ummi da yaranta da wasu ma'aikata mata da suka biyosu suna yi masu addu'ar sauka lafiya, Safwan ya kalli Hajiyar bakinshi yana rawa saboda son tambayarta da ya ke yi akan alƙawarin da ta yi masa, cikin dariya Aunty Ummi da ta fahimceshi ta yi saurin faɗin

"Mun kai maka tana cen kai take jira"

Zee da ke mota tana wasar baki ba shiri ta ji ƙirjinta ya buga, duk da ce wa bata gano ma'anar inda maganar ta dosa ba amman ta yi wasiwasin cewa

_"Anya ba wannan mayyar yarinyar ba ce ake magana a kanta ba kuwa?"_

Sai gata da haɗe fuska tana dariyar yaƙe har suka bar gidan, cike da tsananin farin da jin daɗi Safwan ya riƙo hannunta ya ce

"Hajjaju ayi murna mun dawo ƙasarmu ta gado, sai hankali ya kwanta ga ki kusa da Daddynki da kullum kike ta faɗin kin matsu ki ganshi, tsorona ɗaya shine kada ace gulmata ce ake zumuɗin kai wa?"

ZEE ta yi dariyar yaƙe ba tare da ta ce komi ba, saboda faɗuwar gabanta da ya tsananta bugawa cikin sauri da sauri, har suka je bakin kantamin Gate ɗin gidan nasu bata ji natsuwa ta zo mata ba, hankalinta ya fara ta shi ne lokacin da Direban da ya ɗaukosu ya ke ta buga horn wani bayan wani alamun sanarwar zuwansu.

Ai kuwa kafin ma su je parking space ya ajiye motar sai ga su Surayya da su Husnah tare da Ruma ƙawar zee da wasu ƴan'uwanta biyu aguje sun fito, su Surayya daga sashen Khadijar suna ihun murnar dawowarsu, yayin da su Ruma suka fito daga nata sashen cike farin ciki, gaban Zee ya ƙire ya faɗi ba shiri ta yi saurin fitowa tana ƙarewa gidan kallon yanda aka ƙawatashi da sabon fenti, sannan ta dawo da kallonta ga su Surayya da suka maƙalkale Safwan suna murnar ganinshi, su Ruma suka ƙaraso wurinta cike da murna suna yi masu sannu da zuwa, Fiddo ta saki Safwan ta nufo Zee inda ta wani haɗe rai tana yi mata wani mugun kallo, ba shiri Fiddo ta sha jinin jikinta tare da wayancewa da dannar wayar da ke hannunta.

Cen sai ga wani taku da ya ja hankalinsu duka tare da shaƙo wani daddaɗan ƙamshin da iska ya kwaso ya shaƙawa Zee cikin hanci tamkar da gayya cikin lamarin, ta yi saurin kallon inda take jin sautin takun takalmin sai gata da dafe ƙirji ba shiri, cikin matsanancin faɗuwar gaba tare da dakan luguden da zuciyarta ta ke yi ne ta yi mutuwar tsaye, Dukansu suka ƙurawa Dijen kallo musamman ita da ta kafeta da ido ƙur har ta ƙaraso wurinta, cikin sigar duniyanci Dijen ta rungume Zee fuskarta ɗauke da fara'a ta ce

"Oyoyo Ƙanwata sannunku da zuwa da fatar kun iso lafiya"
Ta ƙare maganar tare da fesheta da wani sabon murmushin da Zee ta kasa gano ko na minene, sannan Dijen ta saketa ta nufi Safwan ɗin da tunda ya ƙyalla idonshi akanta gaba ɗaya ya susuce, yanda ya ke kallonta cikin shauƙin sonta da ke fisgarshi haka ita ma Zee ta bi ta da kallon mamaki, tare da su Ruma da suma ta zamo masu tv saboda kallo.

Dije kam tana zuwa ta yi saurin maƙaloshi tare da yin tsalle ta kai masa kiss a kumatu sannan ta faɗa jikinshi ta ruƙunƙumeshi sosai cikin wani tsantsar farin cikin ganinshi tana faɗin
Chapter 68 · 0% Book details