← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 84

Sashe 23

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safwan ya ce "to ai a ranar ne take sanar dani wannan magana, har ma ta rok'eni ta ce da Ni don ALLAH ka da in fad'a har sai bayan sun mutun ita da Angonta, Ni kuma ganin zata je ta yi aika aika yasa lokacin da shi Balan ya zo neman Abokina ban ja da tsauri ba na amince a d'aura da Ni, saboda haka ina b'ukatar a bani Matata yanzu mu kama hanyar garinmu saboda mu yi saurin isa gida tare da Iyayena da suka yo tattaki tun daga Yola har wannan Gari domin kawai su karb'a mani aurenta"

Baffah ya mike cikin wata sabuwar rud'ewa yace,. "Ni fa kam ba fa zan lamunta da aje man da 'ya ko'ina ba, shiyasa tun farko naki amincewa da auren Abokinka, ashe ban tsira ba na yi gudun gara ne na fad'awa zago"

Ya k'are maganar cikin share wasu hawayen tashin hankalin rabuwa Dijenshi, cikin sanyin jiki Safwan ya kalli Dije da ke tsaye gaba d'aya ta rasa ma abun cewa saboda tsabar gaskiyar da ta yi mata yawa, sai canke canke ta ke yi wai ko dai da gaske tana da aljanun bata sani ba??don ita daga Balan har Safwan d'in bata san ta yi makamanciyar magana irin haka da su ba.

Cikin d'aga murya Safwan yace,. ,"Ke!!"

Ta yi saurin dawowa daga tunanin da ta lula tare da Kai kallonta gareshi, ba kunya Safwan ya rik'o hannunta suka yi nesa kad'an da mutane, sannan ya ja ya tsaya yana k'are mata kallo cikin mere yace

"To bari kiji ni taimakonki zan yi idan munje in sakaki Makarantar secondary har ki zama babbar Likita, idan kuma ba zaki so ba ki fad'a yanzu sai in barki tare da Mahaifinki ya aura maki duk wanda yake so, tunda ke kin kasa hango irin taimakon da zan yi maki bale har ki shawo Kan Mahaifinki ya aminta da auren, bale har ki nuna masa ke zaki aureni kuma za ki bini garinmu duk in da nake ko don cikar burinki na zama babbar Likita"

Dije ta washe baki tace,. "Da gaske Kai ma zaka sakani Makarantar likitocin???"

Safwan ya ce "Eh amman idan har kin amince da aljanunki sun fad'i cewa sai sun kasheki sai sun kashe Bala, sannan kuma idan kin amince za ki bini garinmu"

Dije ta yi saurin kallon hannunta da ya rik'a tace,. "Zan bika amman ya Zan yi da cikin da ka yi mani yanzun nan?"

🤣🤣🤣sai kunzo suna Dije ta samu ciki🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️

Akafta😝

D/AUTA CE🤝🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*

*Lamba ta 24*

Safwan ya zaro ido waje yace,. "Ci me...??"

Dije ta bata fuska ta bar wajen tana ta yarfa hannun alamun k'yama ta nufi wurin Baffanta tace,. "Ka kwantar da hankalinka Baffah duk bayan kwana biyu Ni zan dinga zuwa ina dubaku kaji?"

Ta k'are maganar tare da langab'e kai, Baffahn ya yi mata wani kallo sannan yace,. "Za ki yi man shiru ko sai na mazgeki?? k'iri k'iri kin sa komi ya lalace muna saboda bak'in sakarcinki, to ni Kinga tafiyata idan kin tashi ki bisu ku je bangon duniya ma in kina so"

Yana kare fad'ar maganar ya mike fuuu! Yana kakkab'e riga ya nufi hanyar Gida, Maigarin ya kalli Dijen yace

"Kin amince zaki bi Mijinki?"

Dije ta d'aga kai tana yarfa hannunta da Safwan ya rik'e fuskarta a yamutse hawaye suna sauka tana saka d'ayan hannu tana sharewa, Maigarin yace

"Alhmdllh"

Sannan ya kalli IYAYEN Safwan yace,.

"Ku yi hakuri bayin ALLAH daga yanzu zuwa gobe za mu shawo kan matsalar, insha ALLAHu tun da sassafe sai ku kama hanya,saboda haka na wakilici MALAM Sanda na amice idan kun tashi ku je da Dije amman da rakiyar mutum Uku zuwa hudu ta gefenmu, saboda mu ga muhallinku kuma mu san inda za'a kai 'yarmu Dije"

Gaba d'aya suka amince da hakan, Maigarin ya kalli Bala ya ce, "Kai kuma sai ka nemi matar da duk kake so a garin nan ka aura tunda har hakan ta riga da ta kasance"

K'anen Mahaifin Bala ya fito da kud'i ya nufi wurin Baban Ladiyo ya ajiye kud'i tare da rusunawa yace,. "A matsayina na k'anen Mahaifin Bala ina nemarwa Bala auren yarka Ladiyo, idan ka amince yanzun nan sai a shafa fatiha kowa ya shaida"

Baban Ladiyo ya daburce ya kalli sauran d'inbin jama'ar da ke wajen yace,

"Ni Malam Shehu na amince da na baiwa Bala auren 'yata Ladiyo jama'a ku
sheda"

Ladiyo ta zaro ido tare da barin wajen aguje ta nufi gida Mutane sai dariya suke yi mata, daga nan ba b'ata lokaci aka rarraba goro cikin dan kankanin lokaci aka d'aura auren Ladiyo da Bala, Baffah Kuma aka kai k'arshe akan za'a kwaso masa kayan d'akin Dije da aka jera gidan Bala a dawo masa da abunshi.

Sannan cikin mutuntawa Maigarin ya sa aka shigar da Iyayen Safwan d'akinsu Safwaan d'in, tare da yi masu tarba da abinci mai rai da lafiya wanda Safwan ya sa aka tanadar masu tun kafin su shigo garin.

Bayan sun kimtsa ne Safwan ya yi masu jagora har babban birnin garin ya sama masu masauki sannan ya juyo ya dawo k'auyen.

Dije kam cikin firgici ta koma gida tana yarfa hannu saboda ganin take yi ta hakan ne macizan zasu zube ba za su yi nasarar shiga jikinta su taru ba balle cikinta ya yi k'ato, su Jummala suka biyota d'ii! a baya sunata jin ina ma su ne suka sami irin wannan damar, ta auren mutum d'anboko irin Safwan ga shi fari mai kyau da shi.

Shigarta Gidan ke da wuya ta fara jiyo sautin Baffanta da ya ke ta zuba fad'a cikin d'aga murya, jiki a sanyaye ta isa d'akin nashi tare da rakubewa gefe tace

"Baffahna don ALLAH ka yi hak'uri ka barni in je birnin nan, ka ga idan na yi kud'i na zama likita shikenan zan zo in ta fi da kai mu zauna da ku kai da Inna inda nake"

Baffah ya maka mata wata Uwar harara da jajayen idanuwanshi yace,. "Ke dad'ina da ke sakarci shikenan tunda ya jaki gefe ya karanta Maki k'arya tare da yi maki wayon ya cusa maki ra'ayin biyarshi Ni ma hakan za ki yi man kenan ko?, To bari kiji aure dai an riga da d'aura ba kuma yanda Zan yi in kwanceshi da hannuna amman ki sani ba zaki tab'a biyarshi ba, na fi son abarman ke da igiyar auren saman kanki a gabana har k'arshe duniya aga in.........."

"Da ko baka ji dad'i ba WALLAHI don wannan abin kunya ne ka ke so ka janyowa zuri'armu, saboda haka matuk'ar ina raye Ni ba za'a yi haka ina kallo ba"

Maganar tsohuwa Inna Gambo ce ta katsewa Baffah zancen da yake yi, ta k'araso cikin d'akin tare da dogara sandarta Inna ta yi saurin shimfida mata tabarma ta zauna, Dije ta ja jiki ta isa wurinta ta fad'a jikinta ta fashe da kuka wiwi, Inna Gambo ta shafo kanta tace

"Daina kuka ke ma zaki je ki yi aurenki kamar yanda kowace mace take yi a gidan Mijinta"

Sannan ta d'ago da kanta ta kalli Inna da ke ajiye mata ruwa a sabon kwanon sha tace,. "Ku bar ruwanku bana sha tunda har kuke so ku hana abunda ALLAH ya k'addara, idan ba shirme ba wa ya isa ya ja da hukuncin ALLAH?? Yanzu ku ba ku gano cewa shi ALLAH ba'a yi masa dabara ba?? Kun hanata auren wancen sai gashi ba zato Wannan d'in kuma ya zama ashe shine Mijin, to gargadi na k'arshe gareka Sanda ka kiyayi yin ganganci da abunda ALLAH ya riga da ya tsara a rayuwar 'yarku, don daga Kai har ita Hasiya babu wanda yasan hikimar abunda ALLAH yake nufi da hakan, saboda haka ka bar Dije ta bi Mijinta ku bita da addu'ar fatan zaman lafiya, don sau da yawa abunda baka so shine alkhairinka abunda Kuma kake so sai ka ga ba'a cen alkhairin yake ba, don ba zaka gano hakan ba har sai ka bi diddigi ka sami abun ta k'arfin tsiya sannan ne daga baya zaka gano kuskuren da ka tafka, yo in banda rashin hankali irin naka Sanda ka dubi fad'in garin nan kaf! amman ace 'yarka d'aya ta tab'a samun wannan nasarar auren mutanen birni, ba ka ganin hakan ma wata baiwa ce???, To ka ajiye komi ka fuskanci gaskiya ka gano alkhairin da ke gabanka da sannu a hankali zaka gano manufar yin hakan"

Baffah ya yi saurin share guntayen hawayenshi da suka cika masa ido yace,. "Ki yi hak'uri Inna na amince ALLAH yasa shine alkhairin kamar yanda kika fad'a, amman kam Dole ne in je inga inda za'a kaiman 'yata ko a ina ne ko"

Dije ta mik'e daga jikin Inna Gambo tace,. "WALLAHI Baffah shi ma ya ce zai sakani Makaranta a cen birnin har in zama likitar"

Baffah ya mike tsaye zuciyarshi cike da k'una ya fice don baya son ya furta wani abun da yayar Mahaifiyarshi da ta rage kaf cikin dangin iyayenshi taga ya yi mata rashin kunya, Dije ta bishi da kallo ta sake komawa jikin Gambo tace

"Ni dai Gambo na fasa zuwa birnin tunda Baffahna baya so"

Gambon tace,. "Ko shi ba so ne ba ya yi ba rabuwa da ke ne baya so, musamman da aka ce garin Mijin naki nesa ne sosai"

Dije ta yi saurin fad'in cewa,. "To ai duk bayan sati biyu Sai in dinga zuwa ganinKu ke Gambo"

Inna Gambon ta yi dariya tace,. "Ai ko shekara shekara kike zuwa kin yi sauri ballantana sati biyu"

Dije ta yi saurin mik'ewa tace,. "Ai Ni kam ko wata bazan bari ayi ba Gambo, kuka zan ta yi masu sai an kawoni na ganku WALLAHI "
Chapter 23 · 0% Book details