Sashe 66
Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya ta yi shiru sannan ta ce "zan baka numbar khadija amman da sharaɗin bazaka tambayeta inda take ba har sai ka jira na sanar da kai da kaina, kuma ko da ka gano daga baya ba zaka ga laifin wadda take wurinta ba don Ni na bata khadija da hannuna"
Cikin zumuɗi ya ce "bani numbar kawai Hajiyarmu wannan duk mai sauƙi ne in dai har na sami number'rta"
Ba ɓata lokaci Hajiyar ta saka Fiddo ta yi masa sending number'r ta whassapp cike da zumuɗi ya yi Saving ɗinta a cikin wayarshi sannan ya danna mata kira.
Dije kam kasancewar bata nan tana school saboda lokaci ba ɗaya ba, kuma ga wayar ma a kashe take shiyasa ya yi kira ya kai hamsin amman bai sameta ba, cike da jin zafin hakan da takaici ya yi kwanciyarshi akan kujera ya ƙi zuwa wurin Zee da tunda suka yi aure basu taɓa raba wurin kwanciya ba sai ranar, haka wanibacci mara daɗi ya fisgeshi mai ɗauke da mafalkin khadijar saboda tunaninta ne a zuciyarshi har baccin ya yi awon gaba da shi.
Zee cikin bacci ta shafo gadon ta ji wayam ba kamar kullum yanda ta saba shigewa jikinshi tana shagwaɓa ba, ta yi saurin buɗe idonta tare da kaiwa kan gadon kallo sai gata da miƙewa zaune ba shiri, cikin mamakin sababbin halayen da ya tsiro mata ta sauko gadon ta fito falon, in da ta hangoshi kwance da alamu ma baccin yake yi, nan take wani kuka ya zo mata ta janyo ƙafafuwanta ta ƙaraso bakin kujerar ta yi duƙuso, sannan ta ɗora kanta saman ƙirjinshi ta fara kuka ƙasa ƙasa, cikin bacci ya jiyo sautin kukanta ba shiri ya buɗe ido tare da shafo kanta da ke saman jikinshi, ya yi shiru yana sauraren kukan nata ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba, ganin ta ƙi daina kukan ne ya yi dubarar cire kanta ya miƙe zai bar wajen ta yi saurin riƙo ƙafarshi ta ce
"Ka kasheni kawai tunda har ba zaka iya cewa da ni in yi haƙuri in daina kukan ba"
Safwan ya fisge ƙafarshi ya koma ɗakinsu ya yi kwanciyarshi, Zee ta biyoshi cikin fushi ta hau gadon tare da ciyo kwalarshi daga kwancen ta ce
"WALLAHI tun da ba wukaƙantatta ka ganni ba ka yi kaɗan ka wulaƙantani akan wata matsiyaciya"
Kalmarta ta ƙarshe ba ƙaramin baƙanta masa rai ta yi ba, amman ya yi mata shiru tana ta surutanta na cin zarafi gareshi ga kuma Dijenshi, sai da ya ga renin hankalin nata zai yi yawa ne ya yi saurin miƙewa zaune da nufin kai mata wani wawan mari, cikin tsoro ta kwarma ihu tare da sakinshi ta maƙe jikin gadon tana kyarmar tsoro, cike da takaici ya kalleta ya tabbatarwa kanshi idan ya biyewa zuciyarshi ba ƙaramin duka zai yi mata ba, kuma a yanayin jikinta ba ƙaramar illah zai yi mata ba idan har ya ce kullum ya saki ƙwanji ya yi ta jibgarta, shiyasa ya nunata da hannu ya ce
"Ki kiyayi kawo man ƙananan rashin kunya matuƙar kina son jikinki ya tsira da dukana, idan kuma kin fi son in yi ta jibgarki a banza to ki ci gaba da nuna man kalar taki rashin kunya"
Yana ƙare faɗar maganar ya gyara kwanciyarshi ya kwanta abunshi zuciyarshi cike da ƙuncin rashin samun Dijen da kuma takaicin rashin kunyar da Zee take son yi masa,wadda ko kaɗan ba ya jin zai iya ɗaukar mata wannan halin renin da take son kawo masa.
Ganin ya yi fushi da yawa ne ta janyo jiki ta faɗa jikinshi tana share hawayenta ta ce
"To ni dai ka yi haƙuri ai kai ne ka janyo komi muna zamanmu lafiya"
Ya saka hannu ya tureta ta sake maƙaleshi tana yi masa wani salon da ta san zata samo kanshi, amman duk da ya ji abun har cikin jikinshi a hakan ya mazge ya nuna bai ma san me take yi ba, ganin haka yasa ta marairece tana ba shi haƙuri cikin muryar kuka tare da yi masa kalamai masu nuna karayarta a zahiri, sannan ta samo kanshi amman tare da alƙawalin ba zata sake yi masa irin hakan ba, itama ta roƙeshi duk abunda zai yi da Dijen ya yi a waje amman da ya dawo gida lokacinta ne, akan hakan suka shirya yarjejeniya har ta ciyo kanshi suka lula duniyar ma'aurata, duk da cikinsu kowane zuciyarshi ba daɗi amman hakan bai hanasu gamsar da juna ba.
****
Dije kam itama a ƙagauce ta dawo saboda tunanin sahibul ƙalbinta don ba kiran da bata yi masa ba amman wayarshi ta ƙi shiga, ta hau online ta yi ta bulayin jiranshi nan ma bai hau ba, ta yi ta ajiye masa saƙo ya fi goma na damuwa da rashin jinshi amman bata ga ya duba ba, dole ta haƙura ta kwanta, da safe ma cikin sanyin jiki ta yi komi ta nufi makaranta ba kuzari saboda rashin jinshi da bata yi ba, shiyasa yanzun tana dawowa ko Uniform bata cire ba ta ɗauko wayar ta kunna, abun haushi har lokacin bata ga ya duba massages ɗin da ta tura masa ba, dole ta ajiye wayar ta cire kayanta ta shiga wanka.
Da marece sakaliya suna harabar gidan ita da su Husnah da sauran yaran gidan suna shan iska ne kiranshi ya shigo wayar, ta yi saurin komawa ɗakinta ta rufe sannan ta ɗauki kiran da ya zama na uku zuwa huɗu bata ɗauka ba, cike da jin daɗin ɗaukar da ya ji ta yi yace
"Plss! Khadijah me na yi ake son horani da wannan babban horon?"
Cikin ƙasa da murya ta ce "wane horo?"
Ya ce "ga shi nan mana ana ta yi man kala kala, plss ki daina kashe waya bana son in kiraki in ji ta a kashe kin ji??"
Ta ce "tom".
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "kina a ina yanzu haka kuma ke kaɗai ce ko kuwa??"
Cikin daburcewa ta ce
"A'inah nake?" Ya ce "Eh ina nufin a ɗaki ko falo ko kuma kitchen Ko karatu ki ke yi ne?"
Ta ce "a'a ina ɗaki kwance kawai na ke kuma ni kaɗai ba kowa"
Ya yi saurin faɗin
"We'll idan na ce ki yi man wani abu zaki iya yi?"
Ta yi shiru sannan ta ce "eh"
Ya ce "ok tom Ina son ki tuɓe all ki ɗaukar mani pic's ɗinki Kamar guda goma ko fi haka, amman da sharaɗin duk kika zo cire wani abun sai kiñyi man pic a hakan kafin ki cire wani, tukunna ma menene a jikinki?"
Dije da jikinta ya ɗauki rawa ta yi shiru sai da ya yi tambayar sau uku sannan ta ce "riga da siket ne na atamfa"
Ya ce "ok tom oya fara ɗaukar pic ɗin a haka sannan ki cire ɗankwali shima ki ɗauki pic haka zaki yi ta yi har sai kin gama cirewa all sannan ki yi man na ƙarshen wanda shi ne nafi buƙata akan kowane, na baki minti goma kacal idan kin kammala zan kiraki"
Dije ta yi shiru tare da sauke wayar a kunnenta, jikinta sai rawa yake yi saboda tsoro da kunyar wannan abun da yake son ta aikata, har minti goman ta cika ya sake kira bata ko motsa daga inda take ba, shiyasa ya yi ta kira bata ɗauka ba wani bayan wani haka ya yi ta kira tana kallon wayar amman ta kasa taɓa ta, ƙarshe ma kashe wayar ta yi all zuciyarta cike da jin haushin me ma yasa ta bashi fuskar da har zai zo mata da irin wannan fetsara, ta yi kwance tana ta nazarin huɗubar da Inna ta yi mata akan duk abunda ya nema wajenta ta yi masa matuƙar ba saɓon Allah a ciki, cikin sanyin jiki ta buɗa wayar ta kira Sis Aysha da ta ke hardace da numbarta da ta ba su tun makaranta, lokacin da ta taɓa zuwar masu Visiting ita da Hannatu bayan ta ƙare makarantar.
Kasancewar suna communication da juna ne yasa ta kirata tana shiga kira ɗaya biyu ta ɗauka, bayan sun gaisa cike da jin nauyi ta ce da ita zata turo mata text sai ta duba don ALLAH ta bata amsar da ya dace, minti biyu a tsakani ta gama rubuta text ɗin ta tura mata, sai ga reply ya shigo mata akan ta yi masa duk abunda yake buƙata tunda mijinta ne ba wani cen daban ba.
Cike da jin nauyi ta yi duk abunda ya umurceta sannan ta gama ta tura masa su ta whassapp duks sannan tura masa text kamar haka
"Ga saƙon cen na tura idan ka hau online zaka gani"
Tana ƙare tura masa ta kashe wayar all sannan ta sake kimtsa jikinta ta fito suka ci gaba da sha'aninsu ita da yaran gidan, har dare bata kunna wayar ba sai da ta zo kwanciya ne ta buɗa saboda ta ga Ni Ko ya duba, aikuwa buɗe wayar ke da wuya sai ga kiranshi yana shigowa a wayar, ba shiri ta dafe goshi sannan ta ɗaga wayar zuciyarta cike da jin nauyinshi, amman sai ga shi dole yasa ta ware saboda kalaman ƙaunar da yake ta zazzage mata a cikin kunne suna sauka cikin gangar jikinta, inda cikin lokaci ƙanƙani suka tsintsi kansu cikin wani sabon yanayin buƙatuwa da junansu, akan hakan ya kirata video call suka ci gaba da shan soyayyarsu hankali kwance duk da Dijen ba wani sakin jiki take yi da shi ba.