Sashe 43
Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan an watse taron ne wani ya biyo Dije har gida saboda tun a cen wajen ta ɗauki hankalinshi sosai, yana biye da komi nata har suka dawo gidan, suna ƙoƙarin kwasar wasu kaya ne a bayan boot ya yi mata sallama.
Ba shiri ta ɗago tana ƙare masa kallo sama da ƙasa sannan ta amsa masa sallamar a yangance, cike da jin daɗi ya yi wani tsadadden murmushi yace
"Khadijah ko?" tayi saurin zaro ido waje tace
"Ni? ko dai wata Khadijar?"
Matashin saurayin yace, "ke dai tawa khadijar"
Dije ta zaro Ido waje ta kinkimi kayan da zata ɗauka ta yi cikin gida don ita sam ma bata kula da Safwan da ke zaune harabar gidan yana chat da Zee ba, Amman shi tun daga nesa ya ƙura mata kallo har ta shige, sai dai kuma ganin wannan matashin saurayin ya bita da kallo ne yasa ya yi saurin miƙewa ya soka wayar aljihu ya nufo wurinshi, wanda kafin ma ya isa sai ga Dije da Fiddo sun zo kwasar wasu kayan, Saurayin ya sake nufar Dijen yana faɗin
"Haba Khadijah ki tsaya ki saurareni mana, WALLAHi takanas wannan zuwan da na yi a nan donki kawai na zo"
Ganin Safwan a wurin yasa ta yi saurin washe baki tace, "ALLAH sarki ka yi haƙuri daman na je ne in ajiye kayan in dawo, to ya kake dafatar ka zo lafiya?"
Cike da mamaki Safwan da Fiddo suka bita da kallo, Fiddo ta yi saurin faɗin
"Malam ina zaka kai zunubin fira da matar aure?"
Saurayin ya zaro ido waje zai yi magana Dije ta yi saurin faɗin,
"No! no! Share da ita wasa ce take yi maka dubanni da kyau, kai kanka ai kasan banyi kama da matan aure ba ko?"
Fiddo zata sake yin magana Safwan ya yi mata alamu da ta yi shiru, dole tayi gum ba shiri saboda bala'in tsoronshi da take yi , Dan Saurayin kam ya bi Dije da wani shu'umin kallo sama da ƙasa ita ko sai wani girgizar jiki take yi tana fesa masa wani murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarshi, sai dai ɗagowar da zai yi a ƙoƙarinshi na son mayar mata da martanin kallonta Karaf yaji saukar naushi a fuskarshi, kafin ka ce me ya fara lallasuwa a hannun Malam Safwan, don kuwa sai da ya ci nasarar haɗa masa jini da majina, da ƙyar aka ƙwaceshi a hannunshi don saboda baƙar zuciya irin tashi duk tambayar da ake yi akan me ya yi masa ƙanzil bai iya furtawa ba, hasali ma shigewa ya yi ɗakinshi ya dantse yana kuncinshi shi kaɗai.
Dije kam zuciyarta fes ta kwashi sauran kayan ta yi cikin gida,inda ta taradda Fiddo tana gayawa Hajiya abinda Dijen ta yi wanda har ta janyo aka yi faɗan.
Hajiya ta yi murmushinta mai cike da ma'anoni tace da Dijen kawai ta daina yin irin wannan wautar saboda shi aure ba'a wasa da shi, amman bayan haka ba wani faɗa ko jan kunne da ta sake yi mata, Fiddo kam ganin ba wani mummunan matakin da Hajiyar ta ɗauka akanta yasa ta ci alwashi a ranta na cewa
_"sai na zuga Yaya Safwan ya jibgi shegiya kafin ya koma tunda ita Hajiyar mutanen ƙauyen sun shanyeta bata ganin laifin wannan munafukar ƴar tasu"_
Haka Safwan ya kwana cikin kuncin Dije kam ko a jikinta asali ma yi ta yi kamar ma batasan ta yi wani laifi ba, ko da safiya ta waye aka fara hidimar yin kamun Amarya wanda mutane da yawa sun ci buri a kanshi ciki kuwa har da Dijen Baffah, don kuwa tun da sassafe suka je gidan lalle tare da Amarya, bayan an ƙare ne suka halarci wajen gyaran gashi sai ga Dijen Baffah ta fito shar tamkar wata sabuwar Amaryar, masha ALLAH da ita gwanin burgewa bayan sun dawo gida ne saboda ɗakinsu mutane sun yi yawa ta yi ɗakin Hajiya domin ta shirya, saboda lokaci yana so ya ƙure masu saboda daɗewar da suka yi a wajen saloon ɗin.
Cikin sauri ta tuɓe ta shige wanka a gaggauce ta fito da guntun towel ɗinta iya cinya amman a hakan da shi take yin tsalle tana goge dumbujen gashinta da ya sami ruwa ta gefe ɗaya, ba tare da ta damu da gudun shigowar wani ba saboda baƙar wautarta, sai ko gashi ta yi wani tsalle ta saka gefen towel ɗin tana goge bayan kunnuwanta, wanda hakan ya yi dai dai da shigowar Safwan, cikin rawar jikin ta gyara sai ga guntun towel ɗin ya suɓuce ya faɗi ƙasa.
Ba shiri ya dafe kai tare da zaro ido waje saboda abunda ya gani ya janyo masa wani abu a zuciya tamkar bugun guduma, cikin sauri ta yi wata kuwwa tare da kwasar towel ɗin ta koma toilet aguje ta dantse tana rufe fuska alamun jin nauyin abunda ya faru, makyarkyatar tsoron hukuncin da zai yanke mata, tare da tsananin jin haushin kanta akan abinda ya faru don kada ya ce zai faɗawa wani ko ya rena mata hankali, daman cen ba da wata ƙima yake kallonta ba bale yanzu da ya ganta irin ganin da kowa na duniya bai taɓa yi mata irinshi ba sai shi.
SAFWAN kam wani sabon tashin hankali ne ya ziyarceshi, dafe da goshi ya fice ya nufi ɗakinshi inda yake jin wani masifar ciyon kai tamkar ya rabe masa biyu saboda tsabar saran da yake yi masa.
Cikin zafin nama ya jawo jakarshi ta tafiya da ya zo da ita ya fiddo wasu tablets ya afa a baki ya kora da ruwa sannan ya kwanta shiru yana nazari, tare da ƙoƙarin kawar da gizon da halittar Dijen take yi masa a ido, sai duk wani motsi nashi abun ya ke kallo a ido ya kasa goguwa akan hasken gilashin idonshi, cike da jin haushi ya ɗauko wayarshi ya fito harabar gidan ya zauna yana waya da Zee, inda take sanar da shi cewa gobe Alhamis zata zo insha ALLAHu.
Suna cikin wayar ne ya fara hango mata suna fitowa kowace da shirinta har ma an fara kwasar wasu ana kaisu inda za'a yi taron kamun.
Ya ci gaba da wayarshi yana yi yana kallon ta ina zai hango Dijen, sai dai duk iya nacinshi bai hango ko mai kama da ita ba, ya kasa haƙuri ya mike ya nufi cikin gidan sai dai tun kafin ya isa cikin babban falon ya hango bayanta wata ƙawar Surry tana ɗaura mata ɗankwali, wanda ba tantama zuciyarshi ta bashi cewa itace don izuwa yanzu ya fara hardace tsarin surar jikinta.
Fiddo fito da shirinta tana hangoshi ta nufo wurinshi tana gayar da shi cikin ladabi tace
"Big bros yaushe Auntyn zata zo ne?"
Idonshi akan Dijen yana kallon bayanta yace,. "sai gobe zata zo amman ki ce da waccen yarinyar kada ta kuskura ta fita gidan nan bada izinana ba"
Yana gama faɗar maganar ya fice ya faɗa Motarshi ya fisgeta cikin zafin nama ya bar gidan aguje, cike da jin daɗi Fiddo ta nufi wurin Dijen tana wata yatsina tace
"To ke kinji ya ce kada ki kuskura ki fita gidan nan ba tare da izininshi ba"
Cikin tsananin faɗuwar gaba Dije ta zaro ido waje tace
"Inji waye?"
Fiddo ta yi mata wani kallon uku saura kwabo tace
"Wanda yake da ikon hanaki fitar idan kuma bai isa da ke ba ki je ƙofa a buɗe take"
Tana ƙare maganar ta fice abunta fuuu tare da wasu ƙawayenta tana yatsine yaysinen ƙara turawa Dije haushi, Dije kam cike da tashin hankali ta fisge kanta daga ɗaurin ɗankwalin da ake yi mata ta nufi wurin Hajiya Mama, inda ta taradda ɗakin a cike fam da wasu yan uwansu, cikin sauri ta dawo ta makure tana sharar ƙwallah a gabanta mutane suke ta ficewa zuwa Kamun, har abokan ango suka zo ɗaukar Surayya ganin tana kuka ne yasa tace da ita ta daina kuka bari ta je ta faɗowa Hajiyarsu, sai dai Surayya abokanta suka matsa mata ba shiri ta bisu saboda jiranta da ake yi.
Duk mai niyyar zuwa wurin kamun ya tafi amman Dije tana makure tana kuka ba tare da Hajiya ma ta sani ba, har sai da wata ta ganta ta je ta sanar da Hajiyar sannan ta zo tana tambayar abunda ya gabata zuwa kamun.
Ba ɓata lokaci Dije ta sanar da ita saƙon da da barwa Fiddo ta faɗa mata, aiko take ran Hajiyar ya ɓace ta fara faɗa tare da danna masa kira, tace da shi duk inda yake ya yi gaggawar dawowa gida ya ɗauki Dije ya kaita wajen kamun da kanshi, sannan ta jaddada masa cewa minti biyar ta bashi ya zo ya tafi da ita, tace da ita ta je ta sake gyara fuskarta kafin ya zo.
Jinjina ga Hajiyarmu ta mutunci👍🏻
Akafta😍
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*SPECIAL THANKS FOR YOU MY OMEESHER, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKI HAR GADON BACCINKI, HAƘIƘA MARYAM OMEE KE ƊIN TA DABAN CE A WURINA,KI SANI INA YINKI HAR ABADAN ABADE, ALLAH YA BAR ZUMUNCINMU HAR ALJANNAH, ALLAH YA KAREKI DA SHARRIN MUTUM DA NA ALJAN DA DUK WANI ABU MAI CUTARWA A DORON DUNIYA, UBANGIJI YA ƘARA DAFA LAMURRANKI YA ƘARA KAWO MAKI HASKE CIKIN RAYUWARKI, TABBAS NI DA KE AKWAI ƘAUNA IRINTA FISABILILLAH.*
*Lamba ta 44*
Cike da jin daɗi Dije ta koma ɗakinsu ta wanke fuskarta sama sama a gurguje, saboda kwalliyar da aka yi mata tana nan raɗam, ƙara gyarata kawai ta yi tare da sassaita ɗaurin ɗankwalin sai gata ta fito shar! da ita masha ALLAH, idonta kawai zaka kalla ka gano kukan da ta sha saboda jan da suka yi, amman a hakan ma ta fito ɗagwas ɗagwas abunta, ta ƙara feshe jikinta da turaruka ta ɗauki jakarta ta fito falo, zamanta bai kai na minti huɗu ba sai ga sallamarshi ya shigo yana wani ɓata fuska yana cin magani, ba tare da ya ma kalli inda take ba ya nufi ɗakin Hajiya Mama, daga nan inda take tana jiyo shi yana faɗin