← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 84

Sashe 45

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fiddo kam daɗi kawai take ji saboda ganin Safwan ya fara koya mata hankali, don yanayin Dijen ya nuna ƙarara akwai abun takaicin da ya ƙumsa mata, Hajiya ma kanta ganin yanayin Dijen yasa ta jata gefe tana yi mata faɗa akan ta daina yi masa kuka idan ya yi mata wani abu, ta nuna masa bata ji zafi ba ta hakan ne zai gano kuskurenshi har ya fahimci bai kyauta ba, cikin kwantar da murya ta samu ta shawo kan Dijen, duk da Dijen taso ta sanar da ita abunda ya yi mata amman tana jin kunyar ace ta faɗi wannan abun kunyar wani ya ji, sai dai tasha alwashin duk ya sake kwatsnta mata wannan iskancin ita ko sai ta faɗawa Hajiyar komi.

Safwan kam ALLAH ne kawai ya kawoshi gida saboda rikitaccen yanayin da ya faɗa, wanda shi kanshi ya yi danasanin biye wa son zuciyarshi da ya yi, gashi zai janyowa kanshi baƙauyiyar yarinyar ta ga damarshi a banza a wofi, yaci alwashin ba zai sake kulata ba kuma zai yi ƙoƙarin auren Zainab kafin ma ya kammala karatun, sai suyi zamansu a cen kawai har sai sun gama karatunsu sun huta sannan ya dawo gida.

😝😝😝😝😝uhum

Akafta😍

D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*COMMENTERS ina matuƙar alfakhari da ku, saboda jajircewarku wajen daɗaɗan Comments naku ba dare ba rana,, Mmn Irfaan taki gaisuwa ta musamman ce,, ƴargata mmn Sultan ina yabawa ƙoƙarinki a kullum,, Hauwa Zubair ina yinki sosai tawajena,, Mun Sayyid sannu da ƙoƙari, Sa'ar Bukar Allah ja da kwananki,, Daughter Rufaida siffanta matsayinki a wurina abu ne mai girma, Maryam Omee bakina ba zai gaji wajen gode maki ba, saboda comments ɗinki yana ƙara mani ƙarfin gwiwa sosai, Ummu Afrah (Goribatyna) zumuncinmu daban ne,,,wai wai abun da da yawa fa aka ce mutuwa ta shigo kasuwa, Mutanen Dije idan nace zan ta lissafoku tabbas zan ƙare wannan page kaf ba tare da na gama zayyanoku ba, saboda haka mu haɗu a next Page's sannu a hnkl zamu game😉.*

*Lamba ta 45*

A ranar haka ya kwana yana ta murƙususunshi shi kaɗai cikin ɗaki ba wanda ma yasan me yake ciki, don kuwa yanda yaga dare haka ya ga safiya ko da safiya ta waye gaba ɗaya ya rafke ido sun faɗa sai karen hancishi da ya ƙara tsawo.

Ranar Alhamis ɗin itace ranar da ta kama za'a yi mother's day wanda za'a yi a wani katafaren hall da aka Ƙawata, don Hajiya Mama ma da ita za'a je wannan bikin, shiyasa shiri ake ta ko'ina su Dije sai kaiwa da komowa ake yi anata zirga zirga, Safwan da ke ɗaki yanata kuncinshi ganin Hajiya Mama tana ta sabgar bikinta ko damuwa da ta jishi ma bata yi ba, duk da kuma ta ji shiru bata ganshi ba tun safe har azahar, ko abun break ɗin da aka kai masa ko taɓawa bai yi ba yana nan yanda aka kawo shi ajiye, cike da takaici ya fito ɗakinshi yana wani muzurai ya yafito Fiddo zata wuce, cikin sauri ta ƙaraso wajenshi tana faɗin

"Big bros me ke damunka naga kamar ma baka da lafiya?"

Ya wani basar da zancen yace "kice da yarinyar nan ta kawo mani tea zan fita yanzu kafin in dawo, sannan kayan break ɗin da ke ɗakina a kwashe su duka a fito da su"

Yana ƙare faɗa ya juya Fiddo ta yi saurin faɗin

"Big bros ko dai in haɗo maka da kaina ne? WALLAHi wannan yarinyar ba abunda ta iya sai shirme"

Ba tare da ya juyo ba yace, "ki je ki sanar da ita"

Fiddo ta yi wani yatsine ta ce, "Ni na rasa me ma ya janyo ka kwasowa kanka wannan ƴar dajin, haka kawai ta zo ta janyo maka hawan jini da ƙurciyarka, duk matan duniyar nan ka rasa macen aure sai ita don bala'i, da class ɗinka ka lalace a kanta wannan abun kunyar da me ya yi kama?, Mitssss!"

Ta buga wani uban tsaki ta yi cikin gidan ranta a ɓace, maimakon ta sanarwa da Dijen saƙonshi ta yi wajen Hajiya Mama ta ce

"Yau fa bros baya jin daɗi Hajiyarmu, yanzu haka break ɗin safe da aka kai masa yace a fito da shi bai taɓa ba, yanzu haka tea kawai yace a haɗo masa kafin ya dawo"

Hajiya ta yi shiru sannan tace "to ki je ki cewa Khadijah ta haɗa masa ta kai masa ALLAH ya bashi lafiya"

Tana ƙare faɗar hakan ta ci gaba da sabgoginta Fiddo ta fito cike da jin haushi ta nufi wurin Dijen tana sanar da ita, wai don ta cusa mata haushi ta ce da Surayya

"Aunty Surry yau fa muna da babbar baƙuwa daga Gombe Amaryar yaya Safwan zata zo"

Surayya ta kalli Dije da ke ƙoƙarin fita ɗakin ta janyo kunnen Fiddo tace,. "WALLAHi Hajiya Mama ta ji ki sai kin san baki ragawa kanki ba, ko ranar ba naji tana yi maki kashedi akan hakan ba?"

Fiddo ta ɓata fuska tace, "to ni miye laifina a ciki don na taya yayana son abunda yake so?, Shikenan sai ace kowa baya son zaɓinshi sai wannan bagidajiyar?, Ku kanku ai kunsan cewa ba ajinshi bace amman kuka rufe gaskiya kuna goya mata baya"

Surayya ta yi mata wani mere tace, "Ni rashin hankalinki Fiddo mamaki yake bani WALLAHi, shin da mu da shi wa ya kawo Khadijah gidan nan? Hajiya ko Ni? To ki buɗe kunnuwanki da kyau kiji da ace yaya Safwan baya sonta WALLAHi da ba zai taɓa amincewa ya aureta ba, saboda haka ki ajiye haukarki a gefe ki bar Mata da Mijinta su huta, saboda ke da kanki watarana zaki bada labarin irin son da yake yi mata WALLAHi, don ko wannan auren da yace zai yi, zai yi shi ne kawai amman ba wai don baya son khadija ba, kuma ma yanzu idan ba makiyin ALLAH ba wa zai ga khadija a yanzu yace bata dace da shi ba?"

Fiddo ta yi saurin faɗin, "sai kuma ni nan don WALLAHi ko kaɗan ma ba mahaɗa don kinsan ya yi mata zarra sosai"

Surry ta watsa mata wata harara tace, "to ai ki je kiyi ta yi kar ki fasa"

Haka suka yi ta sa'insa a tsakaninsu har abun ya so ya zamar masu faɗa sai da ƴanmatan da ke ɗakin suka shiga tsakaninsu, Dije kam cike da faɗuwar gaba ta kammala haɗa masa komi a wani ƙaramin tire, ta nufi ɗakinshi gabanta sai faɗuwa yake yi sai dai ganin ɗakin ba kowa ne yasa hankalinta ya kwanta, ta yi saurin ajiyewa ta zo zata fita kenan ta ji ƙarar buɗewar toilet ɗinshi, ta yi saurin ficewa ya ɗaga murya a hankali yace

"wannan kayan fa wa kika barwa su?"

Dije ta dawo jikinta yana rawa ta ɗauki ƙaton tiren ta zo zata fita yace

"Ki je ki dawo ina jiranki"

Ta fice ko waigowa bata yi ba saboda tsananin tsoronshi da take ji, ya bi bayanta da kallo jiki a mace ya zauna ya yi tagumi yana nazarin abubuwan da suka sha masa kai a zuciya, yana nan zaune har ta dawo ya yi saurin cire tagumin ya kalleta sama da ƙasa ya maka mata harara tare da zaro ido yace

"Ni kike so in zuba da kaina ko kuwa?"

Dije da ke tsaye tana wasa da yatsunta ta yi saurin duƙawa ta ɗauki ƙaramin flaks ɗin ta fara tsiyaya masa tea ɗin cikin cup, ta miƙo masa ba tare da ta kalleshi ba jin shiru bai karɓa ba yasa ta ɗago kanta ta kalleshi, sai ko caraf ta yi arba da kallon da yake yiwa ƙirjinta da ya fito cikin wuyan rigarta ba tare da ta sani ba wajen ƙoƙarin zuba masa tea ɗin, ta yi saurin ajiye tean cikin firgici ta miƙe tsaye tana gyara zaman rigarta zata fice, caraf ya riƙo hannunta da jajayen idanuwanshi ya yi jarumtar faɗin

"Magana zan yi da ke fa"

Dije ta waigo cike da mamakin jin muryarshi a tausashe ta ƙwace hannunta tare da gyara tsayuwarta ta rungume hannuwa tana wani cin magani, cikin ko in kula ya ɗauki kofin tean ya kurɓa sannan ya ajiye ya kalleta yace

"Zama zaki yi ba tsaye zaki yi man a kai ba"

Dije ta zauna kan kujerar nesa kaɗan da shi ba tare da tace ƙanzil ba, ya maka mata wata harara yace

"Au tsaranki ne ni kenan da zan zauna kan kujera ke ma ki zauna?"

Dije ta yi kamar ba zata sauka ba cikin fushi ya ce "ba da ke nake magana ba ne?"

Ta sauko da sauri tana gunguni ƙasa ƙasa ya bi bakinta da kallo tare da ƙara haɗe fuska yace,. "Ni kike zagi?"

Ta yi saurin kallonshi ta murguɗa masa baki tace,. "Idan ba zaka faɗi maganarka ba ni tafiya zanyi"

Ya yi mata wani kallo yace, "Ok to ko zaki gwada tafiyar ne?"

Dije ta yi masa wani kallon reni duk da tana jin tsoronshi haka ta miƙe da nufin fitar, ya yi saurin miƙewa ya sawa ɗakin key ya zare ya ƙaraso gabanta ya tsaya yana zuƙar shayin yana kallonta har ya gama ya miƙa mata kofin ta ƙi karɓa, ya saka ƙafarshi ya take ƙafarta da ƙarfi tare da rungumota da hannu ɗaya ya matse mata gefen ciki da ƙarfi, sai gata da fasa wata ƙara saboda azabar da ta ziyarceta ba shiri, ta yi saurin karɓar kofin amman yaƙi bata damar ta ajiye kamar yanda yake so, cikin sigar mugunta ya saka ɗayan hannunshi ya ɗago fuskarta daf da tashi, yana ƙare mata kallon ido cikin ido sannan ya yi wani shu'umin murmushi yace

"Ni zaki kawowa ƙananun rashin kunyar da kika saba yi ko? To wannan karon da kanki zaki gano cewa ni ba sa'ar wasarki bane, idan kin ajiye rashin mutuncin kin tsira don zaki taimaki kanki, idan kuma kika ce zaki yi jayayya da ni to ke ce a wahale"

Dije ta yi saurin fisge kanta tana yi masa wani kallo ranta a matuƙar ɓace tace, "ba nace kada ka sake taɓa jikina ba ne? to WALLAHi wannan karon sai na faɗawa Hajiya duk abunda kake yi man"
Chapter 45 · 0% Book details