← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 84

Sashe 3

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bafaden ya shafo kanshi da yasha mola sol! sol! yace, "Ranka ya dad'e ai ya koma da kanshi ma gashi a saman wuyan ina jinshi"

DIJE ta mike tsaye cikin zabura ta katsa masa wata uwar harara da idanuwanta da suka jajawur! Tace

"Wa ya Gaya maka kanka ne a sama to bari ka ji ku kuke ganinshi kamar Kai irin naku to wannan Yar karamar dabbarmu ce dake bacci a saman kanka, naka kan yana cen bangon duniya bakin kogin zumburbur an fara had'a kayan dafuwarshi da ka yi sake nan da safiya zaka rasa ranka da an jefashi cikin tunkunyar dafuwar"

Bafaden ya zabura dafe kan yace

"A cire man dabbar a maidoman kaina don ALLAH ka taimakeni"

Dije ta kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya sannan ta yi shiru tana tare da Kara kunnenta a iska kamar mai sauraren wani abu sai cen tace,. "Ranka ya dad'e Sarki gani nan zuwa yanzu a yi man afuwa yanzu zan kawo maka"

Tana k'are surutan tace, "Babana Sarkin aljanu yace da Ni in tattaroku yanzun nan dukanku mu had'u a bakin Ruwa ayi shari'ar a cen"

Kowa ya gwalalo Ido waje Aiko cikin sauri ta fara fad'in

"Ya zajisu ya zurmukus banbaradusa ya zamburkusadduna ya......."

Kafin kace me duk wuri ya hautsine da k'ura saboda dan neman gudun famfalakin da mutane suke yi, Bafade dafe da kanshi yana gudu yana fad'in

"Ki tashi daga baccin nan don girman ALLAH ki dauko mani kaina, tun kafin a fara dafuwarshi a bangon duniya"

Ganin mutane da yawa sun watse sai Yan gani kasheni ciki kuwa har da Maigari da Liman sannan da Baffanta da ke nesa da su yana haki, ta k'ara keta kuwwa tace

"Ku saurareni zamu tafi amman ko harara aka yiwa god'iyarmu Dije sai mun dawo tare da gayyar rundunar Yan uwana aljanu, mun tafi Sarkin fadawa ga kanka Nan gobe ka k'ara dan gidan marasa tausayi amman ka sani za mu zo mu tafi da kai da ka kuskura ka fito fitsarin dare, mun tafi zo muje ke kuma sarkin bacci"

Sai kawai aka ga Dije ta fad'i yaraf tana fisge fisge tana wani Abu da kai ta gwalo Ido sai cen ta yi luf kamar Mai bacci.

Liman ya sake tofa mata addu'ar ya fara Kiran sunanta, Dije ta yi wukil da Ido d'aya suna had'a Ido da Liman ta zabura ta mike zaune tace

"Don Allah ka yi hak'uri WALLAHI da gaske naga Kura Ni da su Ladiyo, a tambayesu aji ai ko su zasu fadi gaskiya don ba Ni kad'ai na ganta ba har dasu, a gaban idona taci mutum biyar a farkon gari"

Maigarin yayi shiru yana nazari sannan yace,. "Ai kinci sa'a komi ya wuce tunda an wankeki tashi kije gida amman kar ki sake zuwa daji debo ciyawa"

Dije ta zaro Ido tace

"Na shiga Uku ita akuyar tawa me zata ci idan na daina fita daji?"

Maigarin ya yi Yar dariya yace

"Ni Zan sa akawo maki Ciyawar kullum ki dinga bata saboda baki da isashiyar lafiya tashi kije gida ki kwanta ki huta ALLAH ya baki lafiya"

Dije ta washe baki tace,. " Harda dussa?"

Yace "har da ita tafi gidan kawai"

Dije ta Mik'e tana tsallen jin dad'i tace

"Na gode Maigari ALLAH ya ja da nisan bacci kuma ya baka lafiya ya tsare gaba kuma yasa kar ka mance watarana kaki aikowa"

Maigari sai Ameeen yake fad'i don a matse yake da ta bar wurin tun kafin shima yayi sanadin abunda zai janyo ta k'ara kassarashi.

Dije ta nufi wajen Baffahnta tana dariya tace, "Na huta da zuwa Daji akuyata zata sami ciyawa kullum"

Baffah ya fisgo hannunta suka nufi gida, Mutane da sun hangota su yi ta darewa suna gudu Dije kam sai tsallen cin nasara take yi, Liman kam binta yayi da kallo yayi dariya don shi tsaf ya gano ba wani aljani da ke kanta tsabar iya shege ne ke damunta, amman ko ba komi ya jinjina mata tunda har ta samowa kanta hanyar kwatar kai, daga wannan gangamin jidalin data hadowa mutane a cikin gari.

Akafta😅

D/AUTA CE✍🏻

*💣DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*WAI! WAI! WAI RIGIJI GABJI WANI KAYA SAI AMALI LALLE DIJE K'ARANGIYA TAYI FARIN JINI BA KAD'AN BA INA GODIYA SOSAI MASOYA BOOK D'IN ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU A DUK INDA KUKE👍🏻*

*Lamba ta 4*

Ko da suka je gida suka taradda Inna tana tankaden garin masara tana yi tana sharar hawaye, Dije da gudu ta isa wurinta ta fad'a jikinta har sai da tiren garin yayi tsalle rabi ya zube rabi ciki, Inna ta saka hannu ta Kai mata wani mugun dunku a baya har sai da ta gantsara, a zabure Dije ta mike tana sosa wajen tana zunburo Baki alamar taji haushin dukan, Inna ta nunata da dan yatsa tace

"WALLAHI ki fita idona in rufe Dije na fara gajiya da rashin hankalinki, ke kenan kullum janyowa kanki abunda za'a saka ki a bakin duniya muma ki ja muna zagi a gari, to bari kiji WALLAHI kwanan nan zan sa Delu ta tafi dake birni kamar yanda kullum take rokata akan in bata ke ta kaiki aikatau, kije cen ki had'u da masu horaki da kyau tunda Ni kin renani"

Dije ta fara dire diren kafa tana kuka tana fadin, "ai WALLAHI Inna ko an kaini sai na dawo don ban zuwa birni a yanke mani Kai, Ni dai kiyi hak'uri don ALLAH na yi maki rantsuwa idan na sake ki dakeni"

Inna ta yi banza da ita ta makure jikin gina tana zunburar Baki tana mui mui da Baki tana sharar hawaye, sai ga Baffah ya fito bayi yana fad'in

"Wai ke Hasiya me yasa kullum kike tsangwamar yarinyar nan, to WALLAHI ahir dinki wannan karon don kuwa Dije dan sarkin aljanu ne a saman kanta, yanzu haka shi ya zo ya hana a d'auki mataki kanta Kan abunda ta aikata, kuma yayi gargadin ko harara wani yayi mata za su dawo su sake hargitsa garin nan, idan ke kinga ke zaki iya taron aradu da ka to karki fasa"

Ya kalli Dije yace

"Tafi ki dibi ruwa ki yi wanka ko da zakiji dad'in jikinki akan wannan sukuwar hawan dokin da aljanu suka yi akanki"

INNA Hasiya ta rik'e baki tace, "yanzu Kai Malam har ka yarda da shirmen Dije? Lalle kam, to Ni dai ina baka shawara WALLAHI ka daina goya mata baya tana k'ara zama girtsatstsa, don wannan shirmen nata ba zai hanani jibgarta ba idan tayi laifi ko da ko tsamiya ce akanta Ni babu ruwana"

Baffah zai shiga dakinshi ya waigo yace, "Kurar da kike tsoron zuwanta garin nan to ko nan gidan ma zata dira idan ta zo wannan karon, sai ki je kiyi gaggawar yin rame a karkashin gadonki kinga idan ta zo sai ki shige kawai, don kuwa ba fashi zaki janyo fushin Dan Sarkin aljanu"

Yana K'are maganar ya shige d'aki abunshi domin a matse yake da yada hakarkarinshi ya huta ya samu natsuwarshi ta dawo.

Dije ta dibi ruwa cike fam da farin bokin fenti ta kinkimeshi tana nishi ta yi bayi tana ta gunguni, don taci alwashin sai ta debe haushinta da ruwan gidan don kuwa sai ta yi wacakarta son ranta dasu tunda Innar ta yi mata fad'a.

Gashi sai sun zagaya bayan gidan suka debo ruwan ga wata rijiyar k'ofar gidansu Ladiyo kawarta, ta yi wankanta mai cike da barna sannan ta fito tana rawar sanyi daga ita sai siket a k'irji tana tsallen sanyi, Inna ta kalleta tace

"In dai takamarki mugunta kanki zaki yiwa in mura ta kamaki sai ki bidi mai ce maki sannu, sannan ruwa ma idan sun k'are ai kece zaki debosu don kinfi kowa sanin halin yayanki"

Dije ta zunburo Baki tace,. "WALLAHI Inna kar ki janyo fushin murkustus barakus bn muruddika, yanzu ya sanar dani in fad'a maki suna jin nauyinki don ke kika haifeni sunce in sanar dake daga yau kar ki koma yiman fad'a, da kyar na basu hakuri suka ce sun yafe amman kar a k'ara "

INNA ta rik'e baki tace

"Au abun har ya kai cen? To ki fad'a masu ba k'ari ba har da k'are k'are sai na yi idan sun tashi su yi kuli kulin kubura dani"

Kafin Dije ta yi magana sai ga Usmanu ya shigo Dije tana ganinshi ta yi sum sum ta sassada ta shige dakin Inna kudum, Usmanu ya bita da harara yace

"Wai Inna yaushe yarinyar zata yi hankali ne? Yanzu abunda ta janyo kenan a garin nan? WALLAHI taci sa'a bani nan da sai na kakkaryata bak'ar jidalalla, sannan wannan siket d'in da na hanata sakawa ta fito tsakar gida dashi hakanan shi kad'ai bata bari, to duk abunda na yi wa yarinyar cen Inna kar ki ga laifina tunda ta nuna cewa ban isa ba, to Ni sai na nuna mata na fita kangarewa"

INNA tace "Halin Dije sai ita abita da addu'a kawai ko za'a ci nasarar abun, amman duka yau aka Saba?"

Baffah ya fito yana saka talkaminshi yace

"Ka dai yi a hankali in har ba so kake yi garin nan ya dawo toka ba, don kuwa Dije ba ita kad'ai bace idan ka janyo aka maidaka dan duk'usurun bak'in jakki ko bunsuru shikenan Kai ka janyowa kanka"

Ya fice abinshi Usmanu yaso yayi dariya ya mazge ya nufi randar ruwa Yana lek'awa ya hango ba komi duka tukanen duk ta kwashe ta yi wanka, aiko ya fara kwalla mata kira sai gata da kwandon kayan kwalliyarta tana shafa jar hodarta, cike da bacin ran da ke kwance akan fuskarshi yace

"Uban mi kike cikin Gidan da ba zaki je ki debo ruwa ba?"

Dije ta zunburo Baki tace,. "Yanzu na fito wanka fa Yaya sannan ace inje in debo ruwa? lalle ma!"

Usmanu yayo kanta zai daketa ta yi bayan Inna ta b'oye, cikin gargadi yace da ita WALLAHI muddin bata debo ruwan nan ba sai jikinta ya gaya mata yau.

A gurguje ta gama dige digen bak'in kwallinta ta danbara janbakinta ja fam da Baki sannan ta fisgi bokitin karfensu ta fita tana gunguni.
Chapter 3 · 0% Book details