Sashe 44
Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Don Allah Hajiyarmu ki bar yarinyar nan renani take so ta yi fa, kuma ke kin zo kina goya mata baya ta je ta yi abunda bai dace acen, ki barni da ita don ALLAH ɗazu fa a gaban kowa ta nuna cewa ita bata da aure to a hakan za'a dinga barinta tana shiga ko'ina duk inda taso?"
Hajiya Mama ta maka masa wata jar harara tace, "to Ina ruwanka don tace bata da aure? Auren ne da ita to? ka ga Safwan kar fa ka nemi takura man yarinya, ka barta ta yi abunda take so don kai ma an barka ka je ka yi abunda kake so ko?, To itama tana da ƴanci abarta ta sakata ta wala tunda kai baka so ALLAH zai bata rabonta a gaba, kuma umurni na baka ka ɗauketa yanzu ka je ka kaita cikin ƴan uwanta"
Tana ƙare faɗar haka ta koma ɗaki abunta ta barshi a tsaye zuciyarshi kamar ta tarwatse saboda baƙin cikin da kalaman Hajiya suka sakashi, ya fito fuu yayi waje Dije ta bishi da kallo ganin bai ce da ita ta taso ba yasa ta ƙi binshi, amman sai ga ƙarar tada Motarshi tare da uban horn da ta ji ya fara bugawa iya karfinshi wani bayan wani, cikin sauri ta miƙe ta fito ba tare da ma ta damu da yawan horn ɗin ba ta fara tafiyarta a yangace tana wani basarwa itama fuskarta a haɗe, cike da masifar jin haushinta ya yo kanta da motar kamar zai kaɗeta, amman kasancewar itama zuciyarta a wuya take ko ɗar bata ji ba, asalima tsaye ta yi tana kallon gefe tare da riƙe ƙugu tana girgizar ƙafa, a zuciye ya fito cikin masifa ya ɗaga hannu da nufin sharara mata mari, kallon da ta yi masa yasa ya yi saurin dunƙule hannunshi, sai dai ya yi jarumtar nunata da yatsa yace
"Don kin ga Hajiya tana ɗauke maki shine zaki kawo man ƙananan iskanci ko?, To WALLAHi da kin cikani ɗaukarki zan yi in mayar da ke garinku, don ni aure zanyi bazan juri zama gwauro ba akanki baƙar baƙauyiyar banza, wawuya kawai wadda bata san darajar aure ba in banda ƙaddara ma ni me zai sa in rasa matar da zan aura sai ke?"
Ya nunata a wulaƙance sama da ƙasa sannan ya buga wani uban tsaki ya juya ya shige motarshi tare da rufo ƙofar da ƙarfin bala'i, ganin ko motsi ta kasa yi illa kallonshi da take yi fuskarta a haɗe tana wassafa irin abunda zata yi masa ta huce, yasa ya leƙo da kanshi yace
"WALLAHI idan baki zo ba tafiyata zan yi sai dai aga laifina"
Dije ta yi masa wani mugun kallo sannan ta tako ta buɗe bayan motar ta zauna itama ta jawo Kofar da ƙarfi har sai da tayi ƙara tace garam!, Ba shiri ya waigo baya yace
"Uban wa kika ajiye ya zamo direbanki?"
Ta yi banza da shi ya sake maimaita maganar nan ma ta sake yin banza da shi illa gefe da take kallo tana wani cin magani, aiko a zafafe ya fito ya buɗe murfin ya fisgota iya karfinshi sai gata da faɗowa jikinshi, ba kunya ya saka hannu ya rungumota gaba ɗaya tsantsan don ya kasa controlling ɗin kanshi, cikin zafin nama ta tureshi tare da nunashi da hannu tace
"Babban gangancin da zaka yi kenan a rayuwa ka ce zaka taɓa jikina, don WALLAHi sai na nuna maka cewa Dijen ce dai wadda ka sani ba wata ba, haka ma zan banbance maka tsakanin Khadijah da Dije, idan kuma kana musu ka sake taɓa wani sashe na jikina ka gani, ko an gaya maka cewa ni ƴar iska ce kamar matsiyaciyar budurwar da zaka aura?"
Ta buga masa wani uban tsaki ta buɗe gaban seat ta zauna ta wani hakimce tana wani faɗi tana bajewa,, madadin ya ji ta ɓata masa rai sai kawai ya tuntsure da wata dariyar mugunta, ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba ya faɗa motar ya ja da ƙarfi yana tafiya yana shafa gemunshi yana murmushi, kasancewar Dije ba wani sanin garin ta yi ba shiyasa bata gane inda yake bi da ita ba, har sai da suka kai wani katafaren gida wanda tun daga bakin Gate ɗin gidan zaka gano ba ƙaramar nera aka kasa wajen haɗashi ba, maigadi ya yi saurin wangale masa Gate ɗin yana faɗin
"Sannu da zuwa ranka ya daɗe"
Safwan yana amsawa cikin isa kamar ba shi bane ya ke ta faman murmushi ba, cikin faɗuwar gaba Dije ta yi saurin kai kallonta gareshi ta kalli gidan tace
"Ba fa nan ake kamun ba, me ya kawomu nan kuma??"
Ya yi banza da ita ya fice ya karɓi key hannun Maigadin ya leƙo da kanshi saitinta yace,
"Zaki fito ko sai na fito da ke?"
Dije ta ɓoye firgicinta da take ciki tace
"Idan ka ga na fito to ka kaini inda Hajiyarmu ta ce ka kaini ne"
Ya ce "ok to jirani Bari in zo minti biyu"
Ta murguɗa masa baki tare da bin bayanshi da kallo har ya buɗe wata ƙofa da ta kasance gefe ɗaya na farkon shigowa gidan, ya shiga minti biyu zuwa uku sai gashi ya fito tana ganinshi ta wani juya kanta gefe tana cin magani, yana zuwa ya buɗe motar ya riƙo hannunta ta fisge ya sake janyo hannunta da ƙarfi ta riƙe kujera tana faɗin
"Ba nace kada ka koma taɓani ba? Zaka sakeni ko sai na janyo abunda gaba ɗaya unguwar nan zata taru akanka?"
Ba tare da ya damu da zancenta ba ya janyota gaba ɗaya jikinshi tana tureshi yana ƙara maƙaleta ya janyota iya ƙarfinshi tana tirjiya amman sai da ya shiga da ita cikin gidan, cikin tsoro Dije tace
"Ni dai tsaya mu fahimci juna WALLAHi ba a nan ake bukin ba don ALLAH ka kaini inda ake yi"
Ta ƙare maganar cikin kuka saboda ganinta da ta yi har ƙuryar wani ɗaki ya yada ita akan ƙatuwar katifar da ke shimfiɗe cikin ɗakin, tsoronta ya ƙaru ne lokacin da taga yana rufe ɗakin da key, cikin firgici tace
"Don girman ALLAH ka yi haƙuri WALLAHi ni ba ƴar iska ba ce"
Safwan ya waigo yana wata dariya yace
"To Ni da ke waye ɗan'isakan a cikinmu?"
Ta yi saurin faɗin
"Ni ce, Ni ce WALLAHi"
Ya ƙumshe dariyarshi yace,. "To ai ko yanzu zamu gwada ƙwanji irin na ƴan'iskan ai kin iya ko?"
Ta yi saurin girgiza kai tana matsar ƙwallah ganin ya fara cire riga ne ya sa Dije shiga cikin wani mugun tsoro ta zaro ido waje cikin kuka tace
"Ni Dije yau me nake shirin gani ne?"
Safwan ya mazge ya fisgota ta faɗo jikinshi ya fara yunƙurin zuge mata zif ta yi saurin riƙe hannunshi tana kuka tace
"Ka ji tsoron Allah kada ka ci amanar iyayena don kaga basu garin nan"
Safwan ya fisge hannunshi cikin jajayen idanuwanshi ya kalleta ido cikin ido yace,. "Kika kuskura na sake jin wata magana ta fito bakinki sai kinyi danasanin furta ta"
Dije ta yi saurin rufe bakinta tana toshe kukan da zai fito saboda tsabar tsoron da ya bata amman bata daina zubar hawayen kukanta ba, saboda tana ji tana gani ya zuge zif ɗin rigarta tare da zura hannunshi ta ciki, tashin hankalinta bai ƙaru ba har sai da ta ji inda hannunshi ya sauka, ta yi wata zabura tana ƙanƙame jiki tana faɗin
"Ka tausaya man don ALLAH wallahi Ni ba ƴar iska bace kai ma sheda ne don ALLAH kada lalaceni"
Safwan kam laushin dukiyar fulaninta da yaji a hannunshi yasa shi ɗimaucewa, cikin wata siriryar murya yace
"Ba wani abu zanyi maki ba amman WALLAHi idan kika sake yiman gardama sai kin nemi mai ƙwatarki hannuna"
Dije tana kuka tace
"Ka ceci rayuwata WALLAHi Baffahna ya ji wannan labari kasheni kawai zai yi ba zai barni da raina ba, kada ka janyo abunda zai sa Inna ta tsine man in bi duniya don ALLAH"
Cike da jin haushin magiyar da take yi ya mayar da rigarshi ya buɗe ɗakin a fusace ya fice, cikin sauri ta mayar da zif ɗinta ta ɗauki gyalenta ta fice jikinta sai rawa yake yi, sai dai ganinshi duƙe jikin motar ya dafe kai yasa ta ji jikinta ya yi sanyi, amman a hakan ta buɗe seat ɗin gaba ta zauna tana share hawayenta, sai da ya ɗauki lokaci sannan ya shiga ya tada motar suka fice gidan Maigadin yana yi masa ALLAH ya tsare amman ko kallonshi bai yi ba.
Kai tsaye wajen kamun ya nufa da ita yana ajiyeta bakin Gate ɗin ya juya abunshi ko kallonta bai sake yi ba, Dije ta bi motar da kallo cike da mamakin abunda ya sauyashi lokaci ɗaya, cikin sanyin jiki ta ja ƙafafuwanta ta shiga wurin kamun.
Har aka gama kamun bata da wata natsuwa yaƙe kawai take yi saboda abunda Safwan ya yi mata yasa taji zama garin gaba ɗaya ya fita kanta, don ko ƙudin da ta tanada don ta yi liƙi haka ta koma da su gida ko nera bata liƙa ba, asali ma gaba ɗaya komi ta ji ya fita ranta har sai da Surayya ta fahimci halin da take ciki, cikin damuwa ta ke tambayarta me aka yi taganta so silent haka? me Yaya Safwan ɗin ya yi mata? Dije kam iyakaci tace ba komi ƙarshe ma sai kuka ta fashe da shi, Surayya ta yi ta bata haƙuri don jikinta ya bata cewa wataƙila ko dukanta ya yi saboda ta gaya mata cewa Hajiya ta matsa masa dole shiyasa ya kawotan.