Sashe 42
Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya ta ce da shi kafin ya bar ƙasar ya je makarantarsu Dije ya ganota, amman don kada ma ta gano ba zuwan zai yi ba ya nuna mata cewa zai je har da cewa ta kawo saƙo, aikam sai ga shi saƙon ma da ta bada akaiwa Dijen aika mata ya yi shi ya fece, zuciyarshi cike da mugun jin haushinta saboda shiga rayuwarshi da ta yi, uwa uba yanzu da ta sanadinta aka hanashi yin abunda yake so, don shi bai ma san da wane kalar idon zai kalli Zee ya sanar da ita cewa wai yana da mata, kuma matar ma irin Dije ai wannan ma shi idan ta sani ya zubarwa da kanshi aji, shiyasa ya ci alwashin ba zai taɓa bari tasan da wannan mummunar maganar ba, har sai idan an ɗaura masu auren da ita idan ta zo ta gani da kanta ta ji da kunnuwanta, akan haka ya tsayu suka ci gaba da zuƙar soyayyarsu hankali kwance, duk da kuma wani gefen na zuciyarshi cike yake da fargabar Zee ta san da labarin kafin aurensu.
***
A cen ƙauyensu Dijen kuma anyi auren Usmanu da Hansai, Dijen ma ta je amman kwananta biyu ta dawo Yola saboda a lokaci ana cikin karatu ne excuse ne aka ɗaukar mata, ƙawayenta kuma su Jummala da Ladiyo ma masha ALLAH zamansu lafiya, sun ajiye shirmen yarinya sun fuskanci zaman aurensu, sai dai Balan Duduwa da kullum tsimayi yake yi zuwan ranar da Dijen zata aiko masa da zakkar, shiyasa lokacin da ma ta zo bikin Usmanu yake ta rawar jiki akan bata wani girma na musamman, ganin hakan yasa ta sake yi masa wata kyautar duk da cewa a lokacin itama buƙace take da kuɗin saboda guntayen matsalolin hidamar auren Usmanun, don ba ƙaramar hidima aka yi ba saboda ko ɗakin Hansai shafe yake fess da broking tyles, Mutane sai zuwa gani ake yi ana sontin sulɓinshi, don kaf garin ɗakinta ne kaɗai da tyles ɗin don Inna cewa ta yi ta haƙura bata so ita kam ta yafe.
*****
Kwanaki suna tafiya makonni su zo su wuce, wata ya wuce shekara ta zo wasa wasa sai ga shekara biyu an laƙumeta ba tare da an tantance ba, bikin Surayya ya zo sai hada hadar bikin ake yi bangaroran biyu, waton gidan ango da na Amarya saboda daman cen angon ne ake jira ya kammala ginin gidanshi, Alhmdllh kuma ya kammala masha ALLAH yanzu haka saura sati biyu ayi auren nasu, Safwan ma kanshi saura shekararshi ɗaya ya kammala karatun da ya je yi ya dawo gida, ayi aurenshi da masoyiyarshi Zainab wadda a yanzu yake jin akan sonta ba gudu ba ja da baya.
Dijen Baffah ma a lokacin tana J.a.s.s 3 zasu yi j.l.c su wuce s.s 1, a lokacin idan kika ga Dijen Baffah ba zaki ce itace ba, saboda yanda maƙerin ƴanmata ya fara ƙereta ta ko'ina ta cike masha ALLAH, kwanciyar hankalin da ta samu ya fito jikinta ya haskaka mata fatarta, don a duba ɗaya zaka gano tsantsar kyawon halittar da ALLAH ya yi mata, uwa uba ga kyawon fuskarta da ya fito ɗas cikin doguwar fuskarta, ga gashinta ya ƙara cika da tsawo saboda gyaran da yake samu sosai, Hajiya Mama kanta idan ta kalli Dije sai ta ji takaicin rashin sanin ciyon kan da Safwan ya nuna akan Dijen, saboda ganin yanda komai da ake so mace ta mallaka na siffar jikin Dije ALLAH ya wadata da abunta, sai dai kawai don ita ɗin tana baƙa amman kuma yanzu baƙin ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, asali ma shine ya ƙara banbantata da sauran mata, don fatarta ta murje luwai luwai ta washe gwanin burgewa, ga ƙirjinta cike fam da dukiyar Fulani kuma a tsaye suke ƙyam! ba alamun zasu ranƙwafa a gaba, saboda girkin kwarya ne da su sun cika fam kuma sun baje a ƙirjinta, duk da ba wai sun gama girman bane amman a hakan ma sai sambarka.
Ana saura kwana takwas bikin Surayya ne su Dije suka kammala zana jarabawar j.l.cn tasu, cike da farin ciki da jin daɗi suka baro makarantar tana ɗokin zuwanta gidan saboda shagalin bikin Surayyar da zasu yi.
Aiko tana dawowa suka ci gaba da shirye shiryensu tare da abokan Surryn yan jami'a, don Surry ta kammala degree ɗinta na farko cikin nasara ba tare da samun matsala ba, Fiddo ce ta yi candy a lokacin.
Ana cikin hidimar ne gaba ɗaya suna babban falo sunata tsare tsarensu ne Safwan ya kira Fiddo, cike da tsananin jin daɗi ta cire wayar daga caji ta ɗauka tana faɗin
"Oyoyo big bros don ALLAH ka zo cikin lokaci plss kasan fa kai ne idonmu"
A cen gefenshi ya ce
"Kada ki ji komi zan zo har ma da Auntynki itama zata zo bikin kuma wajenki zata sauka"
Fiddo ta yi wani tsallen jin daɗi sai dai suna haɗa ido da Dije ta maka mata harara tace,. "Kada ka ji komi big bros bani ita mu gaisa idan kuna kusa"
Zee ta karɓa cike da jin daɗin ganin yanda ƙanwarshi ke sonta tace, "Sannu Sis ki tanadi masaukina insha ALLAHu da ni za'a sha shagalin bikin Surry ki zuba idon ganina kinji"
Fiddo ta yi saurin faɗin "kina da babban masauki big Aunty fatana kawai ALLAH ya kawoku lafiya"
Safwan ya karɓa yace
"Ina Surryn?"
Fiddo ta yi wajen Surry ta miƙa mata wayar cike da jin daɗi ta ce
"Amaryar Yaya Safwan ma zata zo bikin wayyo daɗi"
Diirim! dum! Ba shiri kirjin Dije ya buga, cikin son jin gaskiyar abunda kunnuwanta suka jiye mata aranta tace
_"Amarya? Wace Amarya kuma?..."_
Tunaninta ya katse ne lokacin da Surry ta kara mata wayar a kunne cikin sassauta murya tace, "Yaya Safwan ne"
Gaban Dije ya ƙire ya faɗi ba shiri cikin ɗimaucewa ta ji wani kuka ya zo mata ba tare da ta tantance ba, saboda maimakon ta ji muryar Safwan ɗin sai jin ta yi Zee tana cewa
"Ina fatar zaku tarybeni a matsayin Matar yayanku, kuma ku ɗauki cewa tamkar ma an ɗaura na shigo familynku"
Cikin sauri Dije ta saki wayar ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinsu, saboda zuwan wani dunƙulallen abu a ƙirjinta, wanda ya janyo ta kasa juriya bale ta haƙura da kukan bazatan da ya zo mata.
Gareku reader's shin minene wannan abun da ya ziyarci zuciyar Dijen Baffah????????😢
Akafta🤞🏻
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Domin farin cikinku kawai mutanena😅*
*Lamba ta 43*
Dije dunƙule kan gado tana kuka ta ji an dafa kanta cikin sauri ta goge hawayenta ta ɗago fuskata, aiko caraf ta yi ido huɗu da Hajiya Mama fuskarta ƙumshe da damuwa, ta yi jarumtar washe bakinta guntayen hawayenta da suka maƙale suka faɗo, cikin basarwa tace
"Me aka yi maki Hajiyata?"
Hajiya ta sake dafa kanta ta shafo dogon gashinta tace,. "Naji komi Surayya ta faɗa man ki yi haƙuri ki barni da shi ai zai zo garin ya sameni ina jiranshi"
Dije ta yi saurin faɗin
"Ki ƙyaleshi kawai Hajiya Ni na haƙura da duk abunda ALLAH ya ƙaddaro man, haka kuma ma zan yi biyayya ga duk abunda kika umurceni"
Hajiya Mama cike da jin daɗin canjin da Dijen ta samu a wurinsu tace,. "Ki yi ƙoƙari ki nuna masa cewa fa ke ma mace ce duk runtsi kada ki bada wata ƙofa da shi ko yarinyar zasu renaki"
Dije ta ɗaga kanta alamun gamsuwa Hajiyar ta riƙo hannunta tace, " saki jikinki ki koma ku je kuci gaba da shirye shiryenku, ki yi kamar daman cen komai bai faru ba"
Sai da tasata ta je toilet ta wanko fuskarta sannan suka fito tare.
Haka aka ci gaba da hada hadar tare da Dijen duk da zuciyarta ba daɗi amman hakan bai hanata nuna annushuwa kan fuskarta ba, sai dai kuma Fiddo tasha jinin jikinta saboda faɗan da Hajiya Mama ta yi mata akan abinda ta yi a gaban Dijen, duk da ta ci alwashin bazata fasa nuna ƙaunar budurwar Safwan ba ko don Dijen ta ji haushi.
Ana saura kwana huɗu bikin ne Safwan ya diro Nageria tare da budurwarshi, sai dai ita ta yi garinsu sai taga gida sannan ta zo bikin daga baya, a ranar da ya diro gidan da marece za'a je yin wani event mai suna tea party, duka Amarya da ƙawayenta da ma ita kanta Dijen da Fiddo duka sunyi shigar wani yadi milk da kalar cofee, kowacensu ta sha makeup irin na classic ladys masha ALLAH gwanin burgewa, har sun shishiga motoci ne aka manta da agogon Amarya akan stool ɗakinsu, shine Dijen ta fito ta koma cikin sauri da nufin ta ɗauko ta dawo ana jiranta su tafi.
Ta ɗauko agogon ta fito kenan a tsakiyar babban falon suka yi karo har tana ƙoƙarin faɗuwa, cikin sauri ya riƙota ta faɗo jikinshi tare da riƙeta ƙam ƙam don kar ta faɗin, jikinta yana ɓari ta yi saurin kai kallonta gareshi saboda turaren da ta ji ya tabbatar mata da cewa shi ne, ido cikin ido suka kalli juna dukansu a lokaci ɗaya gabansu ya faɗi ras! ras!, Cikin sauri ya saketa duk da bai tabbatar da cewa ita ɗin ce ko ba ita ba, itama kanta ta aro wata jarumta ta yi kamar ma bata taɓa ganinshi ba ta duƙa ta ɗauki agogon da faɗi ta fara taku a hankali cikin wani salon da ita kanta batasan ta iya irinshi ba ta fice, Safwan ya bi bayanta da kallo har ta ɓacewa ganinshi amman bai daina kallon ƙofar ba, cikin wani hargitsatstsen yanayi ya ja jakarshi ya nufi ɗakin Hajiya Mama, don gidan shiru saboda mutane da yawa sun tafi partyn.
Dije kam har ta shiga motar suka tafi ƙirjinta bai daina bugawa ba, saboda ganin bazatan da ta yi masa duk da daman cen tasan da zuwan nashi a ranar.
Sun gudanar da bikinsu masha ALLAH ansha rawa Amarya da Angonta sun gwangwaje tare da abokan ta da yan uwa da abokan arziƙi, Dije ma ba'a barta a baya baya bayan photunan da aka sha kala kala kowace da kalar nata salo ba ƙarya.