← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 84

Sashe 34

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ku tafi da ruhinta ga mu nan zuwa ku je ku je fa yanzu a fara dafuwar tarugu da tattasai duka a saka kar a saka gishiri a saka sugar ihu wayyo ALLAHna WALLAHI sai mun kashe duk wanda ya sake taɓa muna goɗiya"

Tana ƙare faɗar haka ta yi ɗif sai yawu take fitowa a bakinta tana furzarwa suna sauka kan fuskarta tana gurnani, ganin haka yasa wasu Prefect suka nufi ƴar'uwarsu suna zuba mata ruwa ta farfaɗo amman duk da hakan jinin da ke fita cikin kanta yasa ya sake bugeta ta tafi luuuu suka rirriƙeta suna kiran sunanta, inda wasu kuma suka nufi Dijen anata ƙoƙarin talallabarta tana ihu tana botsarewa.

Kai tsaye wasu da yawa suma aljanunsu suka fara tashi kafin ka ce me Makarantar ta hautsine da tashe tashen aljanu, sai yarinya tana tsaye sai dai aga ta heta kuwwa ta faɗi ƙasa tana sambatu aiko makaranta ta rikice ko ta ina sai ihu ake yi.

Ana cikin hakan sai ga wani Malami da vice principal sun shigo bakin Gate ɗin Hostel ɗinsu saboda labari yaje garesu cewa makarantar ba lafiya, sai ko gashi sun taradda abunda ya firgitasu agurguje aka ɗauki Prefect ɗin mai suna Rukayya aka nufi clinic da ita don har lokacin cikin mayen bugun jinin take sai mashalo take yi, Dije kam malamin yasa aka kawo masa ruwa a kofi yayi mata addu'a ya tofa mata ta yi firgigit ta miƙe kamar wata mahaukaciya sabon kamu tana waige waigen faɗin

"A ina nake? me ya kawoni nan? don Allah Aunty kiyi haƙuri WALLAHI ba da gangan na zubar da ruwan ba, don ALLAH ki yi haƙuri kar ki dakeni"

Wasu daga cikin Ɗaliban da ke tsaitsaye suna kallonta suka fara faɗin

"Ai na faɗa maku baƙaƙen aljanune da ita kuka ƙi yarda ai to yanzu dai gaskiya ta fito"

Hannatu tana kuka ta ratso students ɗin ta zo gaban Dijen ta tsaya tace

"Khadijah sannu"

Dije ta waiga ta kalli Hannatu tace,. "Me ya kawoni nan Hannatu??"

Malamin ya ƙura mata kallo yana nazarinta, sannan ya sa aka ta yiwa sauran masu aljanun addu'a suna tashi ɗaya bayan ɗaya, bayan komi ya lafa ya dawo wurin Dijen ya tambayeta minene asalin abunda ya haɗata da Ruƙayya, Dije ta zaro ido tace

"Wace Ruƙayya?? Ni fa banyi faɗa da kowa ba". Yace ba kiyi faɗa ba kika ji mata rauni har kika tsige mata tsoro ɗaya? Gashi a sanadin hakan kin janyo ta suma zaki faɗa ko sai na saitaki yanzu?"

Dije ta fashe da kuka tace,. "Ni fa WALLAHI Malam ba wanda nayi faɗa da shi ka tambayi Hannatu ka ji"

Malamin ya kalli Hannatu yace, "Au kenan da ke aka haɗu aka jiwa yarinyar mutane ciyo ko?"

Hannatu ta fara rantsuwar ita kam bada ita ba a tambayi kowa zai faɗa, daga nan ta yi bayanin yanda duk abun ya faru, Malamin yasa
wasu Prefects ɗin su rubuto masa sunan Dijen da duk wanda aka yi abun gabanshi tun farko, yace da su su kawo masa su gobe idan an tashi assembly, sannan aka kori kowa ya watse Dije ta miƙe da ƙyar suka nufi Hostel ɗinsu, don ranar kam gaba ɗaya labarin ake ta yi duk faɗin school ɗin inda wasu da yawa sunji daɗin abunda aka yiwa Rukayya saboda muguntarta, sai tsiraru ne suka ji tausayinta tare da jin haushin abunda Dijen ta yi mata cikin bainar nasi, yayin da wasu da yawa suka fara jin tsoron Dijen don gudun kada su ma ta yi masu abunda ta yiwa senior Ruƙayya.

Dije dai kam duk da ta yi mugunta amman hakan bai hanata jin tsoron makarantar ba, saboda tashe tashen aljanun da ta ga ana ta yi ranar ya firgitata sosai, musamman da dare ya yi ta kasa bacci har kowa yayi bacci ita ido ƙyamas zuciyarta cike da jin tsoro, aiko tana kwanarsu kwance kan gado ta ji takun tafiya ƙwass! Ƙwass! Ana tafiya da talkami ƴan'tsini ana karkaɗa awarwaro suna ƙara kuma direct wajen gadon da take kwance aka nufo, cikin tsananin firgici da tashin hankali ta sha jinin jikinta sai kawai ta ji an fisgi gadon da take an jijjigashi da ƙarfin tsiya, ana walili da gadon kamar fanka tare da ita anata zagaye ana faɗin

"Ba ke bace kike ƙarya da mu ba to gamu munzo me kike soooooo! me zamu yi makiiiiiii!"

Dije saboda tsabar tashin hankali sai addu'a take zubawa fili, sai dai kam in ta kamo wannan ta suɓuce ta saketa ta sake kamo wata haka ta dinga yi har ta ji anyi jifa da ita tun daga kan gadon har tsakiyar dogon ɗakin nasu, ba shiri ta ƙwallah wata arniyar ƙara tana faɗin

"Wallahi na daina bazan sake ba na tuba ku yafe mani wayyo Baffahna"

Tana cikin surutan ne ta ji an dafata ta zabura da sauri za ta zuba da gudu taji muryar Hannatu tana faɗin

"Ni ce Khadijah lafiya kike wannan uban ihun cikin daren nan?"

Dije ta tsurawa Hannatu kallo tuno abunda taji da kunnuwanta yasa ta ruƙunƙumeta tana faɗin

"WALLAHI mu bar makarantar nan aljanu ne da ita kasheni zasu yi Ni dai gida za'a kaini bazan zauna ba wayyo ALLAHna WALLAHI na daina bazan sake ba, an kashe kowa mu ne kawai muka yi saura"

Hannatu ta riƙo hannunta tace,. "Kalli ki ga? ga kowa nan lafiya ba abunda ya samemu kema tsoro ne kika ji tashi muje mu kwanta"

Wata senior ta zo ta riƙata ta tashi tsaye ta kaita kwanarta suka kwanta tare tana ta tofeta da addu'o'i saboda ba ƙaramin tausayi ta bata ba.

Aiko tun daga ranar Dije tasha jinin jikinta da lamarin duniya don ko malamin da ya tarasu don yiwa kowa hukunci bata ɓoye ba ta sanar da shi ba wasu aljanu ƙarya ce itace,. Amman kasancewar ganin irin ta'adin da ta yiwa Prefect ɗin yasa ba'a yarda da zancenta ba, an dai yi mata gargaɗi sosai akan kada ta sake in kuma ta sake za'a koreta makarantar bayan anyi mata horo mai tsanani, tsoron hakan yasa Dije ta sha jinin jikinta da kowa.

Ranar da aka yi visiting Hajiya Mama da Surry suka zo mata Visiting tare da uwar siyayya da abinci mai rai da lafiya da suka kawo mata, bayan zuƙa zuƙan namomin da aka soyo mata daban tare da wanda aka tsatstsago mata cikin miyar tumaturin da aka ciko mata wani ƙaton ƙaramin bokiti.

Sun sha fira sosai inda har ta gabatar masu da Hannatu Hajiya Mama ta yi ta murnar ganin Dijen ta fara rage ƙiriniyar da take yi, shiyasa ta yiwa Hannatu kyauta tare da ƙara nuna mata ta dinga fahimtar da Dijen abunda ya dace, da kuka suka rabu Dijen tana ta faɗin ita dai a kaita wurin Baffah'nta ta fasa karatun, da ƙyar Hajiya Mama ta zille mata suka tafi suka barta tana ta kukan ita garinsu take so ta koma ta fasa karatun bata son zama likitar.

Dije a hankali ta fara rage rashin jin nata saboda ita kullum dare da tsoro take kwana matuƙar ba tare da Prefect ɗin nan take ba, shiyasa kacokam ma ta koma kwanarta don tafi jin natsuwa idan tana tare da ita, saboda Senior Aysha ba dai addini ba sannan uwa uba tana da tausayin na ƙasa da ita sosai gata da natsuwa, don kuwa ita ko shirgin sauran ɗalibai bata shiga, iyakacinta karatu tare da zuwa masallaci da kullum jam'i baya wuceta saboda addini ya ratsa jikinta sosai.

Sannu a hankali shaƙuwa ta shiga tsakaninsu har itama Hannatun ta dawo wurinta suka yi zamansu hankali a kwance, idan zata je masallaci tare suke zuwa haka ma abinci bata jin ita senior ce da su take bajewa su ci abinsu, wanki ma itace take yi masu su iyakacinsu ɗaurayewa su shanya, ta kamasu ta kwance masu kansu ta tsantsara masu kitso mai kyau don tana jinsu tamkar ƙannenta na jini, musammam ma dai Dijen da yawan gashinta yasa take ƙara sonta saboda duk ta yi mata kitso sai an dinga zuwa kallonshi.

Gata iya gata Senior Aysha tana nuna masu hakan yasa Dije ta kwantar da hankalinta ta fara jin daɗin zaman makarantar, duk da wasu da yawa ma akan abinda ta yiwa Senior Ruƙayya Yusuf yasa suka daina shige mata da nufin cin zarafinta ko su sakata wani mugun aiki.

Don ko da aka yi hutu Dije ƙaguwa ta yi da ta dawo makaranta saboda mutuncin Senior Aysha da kuma ƙawarta Hannatu.

Watan Dije biyar a Yola da aka yi wani hutun second term Hajiya Mama ta shirya ta da uwayen tsaraba suka nufi ƘIRIU waton garinsu Dijen Baffah ɗiyar Inna Hasiya kanwar Usmanu mijin Hansai.

Ina yinku sosai mutanena😅🤝🏻

Akafta😛

D/AUTA Ce😊

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Ɗaukaka da baiwa ALLAH sai ya baka in ya so, babu Malami ba boka zaka zamo mafifici ko da maƙiyanka basa so, ilimi nagarta ke saka ɗan'adam sahun farko, babba ko ko yaro adalci ke saka ka yo ƙarko, daina hanzari magana jari salonta na ɗauko aha😉duniya rawar ƴanmata na gaba sai ya yo baya, inda lokaci zamani ba shi ɓoye baiwata🥴*

*Lamba ta 36*

Tun daga farkon shiga garin Dije ta fara hango mutanen da ta sani, aiko sai faman murna take yi tana ɗaga masu hannu, kafin kace me yara da abokan Dijen da ƴan makarantar allonsu duka sun biyo motar suna kuwwar faɗin

"Ga Dije, ga Dije, Dijen Baffah ta dawo ƘIRIU"

Direba da ƙyar ya samu wajen da ya raɓa ya yi parking saboda cincirindon yara da matasan ƴanmata har ma da wasu samarin duka, kowa fatanshi ya fara yin ido biyu da Dijen, saboda labarin da suka ji cewa Dijen ta yi aure gidan masu kuɗi.

Aikam itama Dijen cikin ƙaguwa ta ɓalle murfin motar ta fito bakinta a washe tana faɗin,. "Wayyo daɗi gani na dawo garinmu"

Aguje ta zanƙara da gudu ta yi cikin gidansu inda taci karo da Inna rik'e da zane tana ƙoƙarin yafawa yana zarmewa, saboda tsabar saurin taje ta ga Dijenta da taji anata ihun faɗin gata ta zo.
Chapter 34 · 0% Book details