← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 84

Sashe 54

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalinsu a kwance suka kwana saɓanin ita Dijen da ta kwana tana juye juye saboda haushinshi da take ji, uwa uba kuma ɓacin ran da ya nuna ba ƙaramin tsaya masa a rai ya yi ba, har sai da Inna ta tashi zaune tare da yadata da fitila ta kira sunanta, Dije ta yi saurin share hawayenta ta amsa tana sharɓar kukanta, cikin tausayinta Inna tace

"Tashi ki zauna magana zamu yi"

Dije ta yunƙura ta tashi tana ci gaba da goge hawayenta da hularta da ke hannunta, Inna tace

"Ki natsu da kyau ki saurareni Dije, saboda ina son ki fahimci halin Mijinki ku daina samun saɓani da shi,Mijinki ba wai sonki ne baya yi ba halinshi ne hakan saboda ALLAH ya yoshi mutum mai zafi,ki yi ƙoƙari ki karanceshi ki kiyayi abunda kika san zai ɓata masa rai, haka ma ki so abunda kika fahimci yana so ko da ko ke bakya son abun a ranki, kuma ki sani Mijinki yana da ikon taɓa ko'ina na jikinki ba tare da ya yi laifi ba, asali ma har lada ALLAH zai bashi idan yayi abunda kike ganin kamar bai dace ba, ki tallafi kanki da Mijinki Dije ko da ko bayan bamu duniya ki yi ƙoƙari ki samarwa kanki wata daraja mau girma a wurinshi, yanda ko da ya auro wata ba zata fiki da komi a wurinshi ba, don WALLAHi wannan mijin naki da kike gani to kowace mace tana fatar ace ta samu irinshi, amman ke gaki ALLAH ya baki kyauta kina so ki yi wasa damarki"

Dije ta share hawayenta tace, "Inna me yasa kullum baki ganin laifinshi sai nawa? Ko don ban sanar da ke cewa yanzu haka aure zai yi ba da wata abokiyar karatunshi"

Inna ta zaro ido waje
Tace. " aure??"

Dije tace "Aure inna kuma har kashedi yayi mani akan idan na sanar da ita cewa Ni Matarshi ce sai ya yi man mugunta, kuma baki ganta ba ƴargayu da ita harda mota take tuƙawa"

Inna ta yi shiru tana nazari sannan ta ce, "to ke ina ruwanki da motarta tunda dai dake da ita duk ɗaya kuke a wurinshi,don har ma kin fita saboda ke yanzu Matarshi ce ita kuwa budurwarshi ai ko a hakan ma ke matsayinki yafi nata nesa ba kusa ba, saboda haka ki yi ƙoƙari ki danƙe Mijinki a hannu ko da zata shigo daga baya to ke kin riga da kin fita matsayi a wurinshi, saboda haka ki ajiye shirme Dije ki kama Mijinki WALLAHi tun kafin wata mace ta yi maki sakiyar da babu ruwa akanshi, don haka ki bi abunki sau da ƙafa duk abunda yace ki yi idan yace ki bari ki bari sai ki ga a hankali ma ya daina wannan zafin kan da yake yi"

Dije ta yi shiru tana nazari sannan tace, "to ai Ni Inna bama zama yake yi ba ai saboda yanzu haka da an ƙare bikin Surayya zai tafiyarshi to wace biyayya zan yi masa bayan bamu ma tare?"

Inna tace "ko bangon duniya ya je ai dai Mijinki ne ko? Kuma kuma zai dawo kuma zaki yi masa biyayya ko bayan idonshi, saboda haka ki yi ƙoƙari kafin ya koma ya ji daɗin ɗan zaman da zai yi da ke, saboda ko da ya tafi ki barshi da kewarki a zuciyarshi yanda kullum zai yi ta fatar yayi sauri ya kammala karatun nashi ya dawo wajenki, amman idan kika yi sake har ya yi auren baki canza wannan halin naki ba to idan ya je mantawa ma zai yi dake ya yi ta Amaryarshi, ya barki sake da baki anan kina lissafin lokacin dawowarshi, wataƙila ma idan ya ji daɗi sai dai kiji ya ƙara wasu shekaru yace ba yanzu zai dawo ba"

Dije ta yi shiru sannan ta ce "to yanzu idan nayi masa duk abunda yake son zai fasa auren ko kuwa??? "

Inna ta yi saurin faɗin

"Ina ruwanki da aurenshi ya auri matan duniya ma idan zai iya kedai ki bi hanyoyin da duk na sanar da ke ki samu ki samo kanshi, da kinyi haka shikenan kin gama da matsalar wasu mata cen, don shi da kanshi zai bayyanawa matan matsayin da kike da shi a wurinshi, kuma dole ma suma su shiga taitayinsu idan har suna son zaman lafiya tare da shi"

Dije tace "aiko inna sai na ba ki mamaki don kuwa bazan taɓa bari wani ya sake jin tsakanina da shi ba, in dai har hakan shi zai kankaro mani darajata a wurin ƴanmatanshi"

Inna tace "yawwa Dijeta ki gwada hakan da na sanar da ke ke da kanki zaki gano irin nasarar da za'a yi"

Haka Inna ta yi ta ɗorata a hanya har taga Dijen ta fara gyangyaɗi sannan tace su kwanta sai da safe a ci gaba, Dije ta baje tana ta sharar baccinta mai cike da mafalkai iri iri na Safwan da budurwarshi Zee.

Ko da safiya ta waye tun asuba Inna ta ci gaba da bata wasu darussan, Dije kam ta naɗe komi cikin ƙwaƙwalwarta har ALLAH Allah take yi ta fara aiwatar da su idan sun koma cen, fatanta kawai Safwan ɗin ya nunawa Zee irin yanda take da matsayi a wurinshi.

Hhhhhh wasar zata fara kenan😅

Akafta🤪

D/AUTA CE

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*ALHMDLLH MUTANEN ƘARANGIYA BA ABUN DA ZAN CE DA KU SAI GODIYA, SABODA KUN NUNAWA LITTAFIN ƘAUNA FIYE DA YANDA NAYI TUNANI, TSAKANINA DA KU SAI SAMBARKA DA SON SO IRIN NA FISABILILLAH😍 ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU*

*Lamba ta 52*

Ko kafin Safwan ɗin ya zo tuni Dije ta yi wankanta tsaf ta shirya, cikin zuciyarta cike take da ɗokin zuwan na shi saboda ta bashi haƙuri akan abunda ta yi masa, duk da kuma wani sashen na zuciyarta cike yake da jin nauyin haɗuwarta da Hajiya Mama, saboda yanda ta kamo hanya abinta ba tare da ta yi sallama da ita ba, bayan ta gama kammala duk abunda zata yi ne tace da Inna tana so ta je ta yi sallama da Inna Gambo, Inna tace ba inda zata je har sai Mijinta ya zo, ta ɓata fuska tace

"Inna fa sauri zan yi inje in dawo don kada ya zo yace sauri yake yi ba zai bari inje ba"

Inna tace "sai ki lallasheshi ai tunda kina son ya barkin"

Suna cikin wannan diramar ne suka jiyo ihun yara da saukar mota a ƙofar gidan, Dije ta diririce tace

"Kinji ko Inna gashi nan ma har ya zo ban tafi ba"

Inna ta maka mata wata uwar harara ta ce, "da kin je ai da zai ɗaukemu mutanen banza in ya zo bai taradda ke ba.."

Sallamar Usmanu da shi Safwan ɗin ne ya katse maganar Inna ta yi saurin faɗawa ɗaki ta sako hijabi ta fito suna gaisawa, Dije Usmanu yana baza masa tabarma da nufin ya zauna yace

"Ai da ka barta tafiya zamu yi saboda kada mu yi dare sosai kafin mu isa Gombe"

Usmanu ya kalli Inna yace "Ina Baffah su yi sallama to don naga baya gidan??"

Inna tace "yanzu nan zaka ganshi don bai daɗe da fita ba"

Usmanu ya baza tabarmar Safwan ya zauna yana kallon Dije dake zaune saman turmi tana yankan akaifa, don tun da ta gayar da shi ta sha jinin jikinta.

Baffah ya shigo cikin sauri yana yi wa Safwan Barka da zuwa bayan sun gaisa ne Baffah ya yafito Dijen ta taso jiki a sanyaye saboda yanda take jin gabanta yana faɗuwa tun lokacin da ta yi ido biyu da Safwan ɗin, saboda wani sihirtaccen kallon da ya jefeta da shi, ba shiri ta yi saurin kawar da idonta, shiyasa ko da ta zo wurin Baffan bata bari sun haɗa ido ba ta zauna gefen Baffan, Baffah ya kalli Safwan yace

"Bakina ba zai gaji ba wajen baka haƙuri akan ƙurciyar Dije, don ALLAH ka ƙara lurar da ita akan duk abunda ka ga ta yi na rashin kyautawa, kai kuma ka ji tsoron Allah ka riƙe matarka Amana, sannan ka yi mata uzuri akan abunda ta aikata a bisa kuskure"

Safwan ya sunkuyar da kanshi yace, "ba komi Baffah insha ALLAHu komi ya wuce kuma ma hakan bazata sake faruwa ba, adai ci gaba da yi muna addu'a kawai saboda addu'arku tana da tasiri sosai garemu"

Cike da jin daɗin zancenshi Baffah ya kalli Dijen yace "ke kuma ki yiwa Mijinki biyayya duk abunda ya ce dake ki yi kar kiyi masa musu ki amince, saboda in yasan abun nan ba mai kyau bane kema kinsan ba zai ce ki aikata ba, don haka yi nayi bari na bari shine halin matayen kirki, saboda haka kiyi ƙoƙari kiyi koyi da halin mahaifiyarki don kin fi kowa sanin yanda take zama dani, saboda haka kema ki koya ki zauna da Mijinki cikin girmamawa, ALLAH ya yi maku albarka ya baku zaman lafiya a cikin zaman aureku"

Daga Dijen har Inna har shi Safwan ɗin da Usmanu da ke tsaye sai "Ameen Ameen" suke faɗi, Inna tace ta je ta ɗauko Hijabinta sabo da ta bar mata, Safwan ya ciro kuɗi a masu dama ya ajiye gaban Baffah sannan ya miƙe, cike da jin daɗi Baffah yace

"Haba haba ai kuma hidimar tayi yawa gaskiya, ka barshi kawai ALLAH ya sa albarka"

Safwan ya nuna sam bazai karɓa ba dole Baffah ya dawo godiya tare da sanya alkhairi, Dije ta shiga ɗaki ta ɗauko Hijabin Innar da ta bata sabo fil,, Usmanu ya ɗauki manshanun da Baffah ya shigo da shi cike da galam ya je ya saka masu a mota tare da taimakon Safwan ɗin da ya bi bayanshi ya buɗe masa Boot ɗin, Dije ta sako hijabin tana ɓata fuska ta nufi sashen Hansai suka yi sallama, sannan ta fito ta kalli Inna tana matsar ƙwallah tace

"Inna yanzu shikenan bazan je inyiwa Gambo sallama ba? Ga shi ma gidan kowa ma baki barni na je ba"

Inna ta ce "ki tambayeshi idan ya amince ku je tare da shi ma sai ya gaisheta"
Chapter 54 · 0% Book details