← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 84

Sashe 64

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Cool down Zee Sani wannan faɗan fa duk mai sauƙi ne idan kin so ki sauƙaƙawa kanki shi, yanzu dai miji a hannunki yake to ki yi iya ƙoƙariinki wajen ƙwamuso abunki ya dawo hannunki, Saboda ke ce amarya mai sabon muhallin shiga har ana ihu musamman idan kina gyara jikinki, to ko uwarshi kika ce kada ya kalla bai isa ya kalleta ba bale wata aba kishiya cen, wadda idan kika so cikin ƙanƙanin lokaci zaki saita mata hanyar zuwa gidan ubanta ba tare da ta shiryawa zuwan ranar ba"

Daga Zee har Ruma suka ƙyalkyale da dariya har da su shewa, ZEE tana dariya tace

"Daɗina da ke ƙawata baki da sanya, WALLAhi tunda har ya tsiro da wannan renin hankalin to Ni kuma sai na nuna masu cewa ba a banza aka haifoni duniya ba"

Haka suka yi ta zuga Zee tana hawa tare da sanar da ita wasu salon kissoshi da bata san da su ba, sannan aka yi masu sha tara ta arziƙi suka tattara yanasu yanasu suka koma Gombe, tare da yi mata fatar zaman lafiya da mijinta.

****

Amarya Zee kam sannu a hankali ta dinga nutse Angonta cikin tafkin kogin ƙaunarta, saboda ko kaɗan bata gajiya da buƙatarshi akan hakan ta sami matsayin da ko kaɗan bata yi tsammani ba, saboda salon kissar da ta mamayeshi da ita wadda ko kaɗan bata nuna masa jin haushinta akan damuwar rashin Dijen da yake yi, illa ma haƙurin da take ba shi duk da har lokacin bata san asalin labarin ba, saboda ta tafi ne kawai a zuwan makarantar da take yi ne baya so a sanadin hakan ta haifar masu da matsala, shiyasa ya shiga irin wannan damuwar ta yi amfani da damarta ta saka shi nanuƙe mata kullum, saboda ba laifi ta tsayu da kyau wajen gyara jikinta a ƙokarinta na son fin kowa a wurinshi.

Bayan sati biyu da aurensu ne suka yi sallama da kowa suka kama hanyarsu ta zuwa London, zuciyar Zee cike da jin daɗin ganin Safwan ɗin ya zama nata ita kaɗai kuma mallakinta, saboda ko kaɗan Hajiya Mama bata nuna cewa sai an tafi da Dijen ba, don ganin yanda Zee take ta rawar kai da Safwan ɗin, kuma ta fi son duk lokacin da Dijen zata dawo gareshi ya zamto itama ta zamo mace dai dai da kowace mace mai ji da kanta, wanda a lokacin ita da kanta zata ƙwaci ƴancinta a hannunshi ba tare da ta nemi taimakon kowa ba.

*****

Dije kam tun tana damuwar rabuwa da su Hajiyar tare da kewar Mijinta har ya zamo ta saki jikinta ta fara zuwa Makarantar da aka sakata ta fara daga class five waton ss 2 wadda ta zamo jeka ka dawo ce kullum da mota ake kaita a dawo da ita, babu inda take zuwa daga gida sai makarantar sai kuma idan zasu je yawon buɗa idanuwa wurin shaƙatawa kala kala ko kuma idan zasu shiga shaguna siyayyarsu ko ta gida, sannu a hankali idon Dijen Baffah ya fara buɗewa ta fara jin kanta itama wata aba ce mai daraja, musamman idan ta ga ta yi wanka ta sade cikin ƴaƴan Aunty Ummin ba wani banbanci sai fari da zasu nuna mata, don idan ma aka ce za'a tantance take yanke za'a ce ta fisu, saboda cikar ƙirjinta da suka ƙara fitowa ɓul ɓul ga kuma hips ɗinta da ya buɗe tare da tudun duwawunta masu gantsarwa da suka turo, don ko hijabi ta saka dole ne ma sai sun fito ballantana tana cikin shigar ƙananan kaya, fatarta ta murje sosai sai sheƙi take yi haka ma jikinta ya mulmule ta ko'ina ba rama.

Ga cima irin ta yangayu da take ci ga zama wuri ɗaya da hutun ya ratsa jikinta, tubarakallah masha ALLAH Dijen Baffah kam, don kuwa duk mai son mace ya ganta ya zo ƙarshen nema.

Duk da jin daɗin da take yi hakan bai hanata yin kewar Mijinta ba, don kuwa lokaci zuwa lokaci tana tsintar kanta cikin wani sabon yanayin buƙatuwa da mijinta, amman dole take ɓoyewa don bata son Aunty Ummi ta ganota, sai ga shi watarana tana dawo wa daga school ta taradda wayar Aunty Ummi tana ta ɓurari soke da caji, ta ɗauka ta nufi ɗakinta bata nan ta dawo ɗakinsu Husnah babbar ƴar Aunty Ummin da nufin ta tambayesu ita, suka sanar da ita ai ta fita wataƙila mantawa ta yi da wayar ta fita ta barta, sai ga kiran ya katse aka sake bugowa Husnah ta karɓi wayar tana ganin numbar ta gano Safwan ne, cikin dariya ta miƙa mata wayar ta ce

"Aunty Khady ki ɗauka mana maybe uzurin babba ne shiyasa ake ta kira"

Kasancewar number ce kawai ba suna shi yasa ta yi saurin ɗauka ba tare da ta ce ƙanzil ba ta ji ya ce

"Plss Aunty Ummi don ALLAH ki tayani roƙon Hajiyarmu ta dawo man da matata WALLAhi a takure nake sosai da rashin sanin inda take, don ALLAH Aunty ki ce ta bani matata WALLAhi buƙace nike da ita kamar in kuwata"

Dije ta yi saurin cire wayar a kunnenta ta goge kwallar da ta sauko mata ta miƙawa Husnah wayar cikin sanyin jiki ta fice ɗakin ta nufi ɗakinta da aka ware mata ita kaɗai, Husnah ta bita da kallon tausayi ta kara wayar a kunnenta saboda maganar da yake ta yi yana kiran sunan Aunty Ummin cikin magiya, cikin wata muryar tausayawa dukansu ta ce

"Auncle Mummy bata nan ta fita idan ta dawo za'a sanar da ita ka kira"

Cike da jin haushinta ya ce, "uban wa ya ce ki ɗauki wayar kin san bata nan?"

Ta yi saurin faɗin

"Sorry Auncle....."

Kittt ya kashe wayar cike da jin haushinta, Husnah ta sauke wayar ta yi shiru tana nazari sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Dijen, sai dai kukan da ta ji tana yi ne yasa ta yi saurin isa wurinta tana faɗin

"Plss Aunty Khady ki yi haƙuri ki yi shiru ki sanar da ni abunda kike wa kuka, Ni kuma insha ALLAHu zan taimakeki ko don ki sami farin ciki"

Da ƙyar ta shawo kanta ta yi shiru sannan Dijen ta miƙe zaune tare da share hawayenta ta ce, "kin yi alƙawalin ba zaki faɗawa kowa ba?"

Husnah ta yi mata kallon tausayi ta ce, "ki faɗa kawai Auntynmu ni nace da ke zan taimakeki in dai hakan zai sakaki farin ciki"

Dije ta ce

"Ya zanyi in dinga communicate da Auncle ɗinku ba tare da ya gano ni ce ba?"

Husnah ta yi shiru sannan tace, "ki bani yau zuwa gobe zan samo maki number'rshi da yake using da ita yanzu, ke kuma sai a buɗa maki whassapp ki dinga yi masa magana a ɓoye amman fa plss kada ki bayyana masa inda kike, har sai lokacin da Hajiya Mama ta sanar da shi da kanta, don WALLAhi Mummy tasan da Ni a wannan lamarin kinsan zan ci Ubana ne a hannunta"

Dije cike da jin daɗi tace "na amince My Husny don ALLAH ki taimakeni WALLAHI da kinyi man haka kin gama man komi don sai naji daɗi sosai, kuma kin ga ke ma ai zaki sami lada"

Husnah tana dariya ta ce "ai naji haushin da wayar Mummy take da security na fingerprint WALLAhi da yanzun nan zamu samota"

Dije ta dafe goshi tace

"Ai shiyasa ma kika ga bana taɓa wayar Aunty saboda ba abunda zaka iya yi da ita idan ma ka ɗauka"

Haka suka yi ta shawarwarinsu har dare lokacin da Aunty Ummi ta yi bacci, sannan Husnah ta je ta lallaɓa ta saka yatsanta da ta yi lock ɗin da shi ta cire securityn, sannan ta yi saurin shiga wayar ta ɗauki number'r Safwan a wayarta ta ajiye wayar ta fito cikin sanɗa, sannan ta dawo wurin Dijen da ke ta tsumayin jiran fitowarta, kai tsaye ta bata numbar ta yi saving a wayarta, sannan ta nuna mata duk yanda zata yi da yanda zata shiga da fice cikin whassapp ɗin, sannan ta yi mata sai da safe ta shige ɗakinsu.

Dije kam cike da tsananin farin ciki ta shige nata ɗakin ta dantse, sannan ta haye gado cike da murna ta fara shiga contacts list ɗinta sai ga number'r Safwan ta fito raɗam tare da hotonshi da ke dp, inda ya sha ƙananun kaya sun fito da kyaunshi sosai sai dai ƴar ramar da ya yi, amman duk da hakan sajenshi da ɗan ƙaramin gemunshi sun ƙawata fuskarshi gwanin burgewa, ya fito bafulataninshi na usuli mai cikar zati tare da tarin kamala da ke tattare da fuskarshi.

Dije ta yi zooming hoton sosai tana shafo fuskar sannan ta kai bakinta ga hoton ta yi mai kiss ba shiri ta rufe fuskarta tana dariya alamun jin kunya, sannan ta shiga ta fara yi masa sallama, aka yi dace yana online amman bai kula da ita ba ma balai ya duba yaga ko wace ce, saboda ganin baƙuwar number Kuma daga Nigeria, don in da sabo ya Saba da gayyar mata da maza masu son cuso kansu gareshi ta ƙarfin tsiya, shiyasa bai cika damuwa ma da ire irensu idan ya gani ba, Dije kam ganin bai amsa ba yasa ta sake turo masa emoji na kuka mai ɗauke da ƙwalla kamar haka😢ta sake ce wa

_Salam!_

Amman nan ma shiru cike da jin haushi ta shiga gallery ta Ciro wani pic ɗinta Wanda daga ita sai guntuwar t.shirt baƙa ba ɗankwali sai dai ta yi cropping ɗinshi ta cire fuskarta ta bar ƙirjinta kawai tare da jelar gashinta da ta sauko a kafaɗunta har gaban ƙirjinta, sai da ta tabbatar da hoton ya shiga sannan ta yi offline zuciyarta cike da jin daɗin ganin photonshi.

Dijen Baffah banda jan rai hwa🙄

Akafta😝

D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Na gode sosai da addu'o'inku gareni i luv u all my guys💋*

*Lamba ta 60*
Chapter 64 · 0% Book details