← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 84

Sashe 39

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gambo tace "To yanzu ki adana tambayarki kar ki yi ta da kowa sai Mijinki idan har ALLAH ya dawo da shi lafiya, kar ki mance ki tambayeshi ki ji menene kwanan Auren?, Insha ALLAHu da kanshi zai warware maki zare da abawa, don na tabbata shi yasan me hakan yake nufi, amman fa kar ki sake ki tambayi kowa sai shi kin ji ko?"

Dije ta ɗaga kai cikin rashin fahimtar inda ta dosa, amman har dare bata daina tunanin kalmar kwanan Auren ba, in ta canko wannan ta canko wancen har ta gaji ta jefar duka, duk da ta so ace ta tambayi Inna Hasiya amman da ta tuno da gargaɗin da Gambo ta yi mata sai ta fasa.

Tun cikin daren ranar Inna ta fara haɗa wainar farar shinkafar da Usmanu ya siyo daga birni, madadin Geron da Baffah ya ce ayi da shi.

Aiko tun da sassafe ta fara tuyar wainar Dije tana tayata har suka gama, aka bi gida gida da wainar ana rabawa mutane sai sambarka suke yi, don ko Maigarin sai da aka cika masa ƙaton kwano da waina da miya har da manshanu aka kai masa gida yana ta godiya.

Mutane sai shigowa suke yi ana yi wa Dije Barka da zuwa ana yi wa su Inna godiyar tsaraba, duk da wasu da yawa ma gulma ce take kawosu don su ganewa idonsu yanda Dijen ta koma, sai dai yanda take ta gayar da su ne a mutunce yasa suka fara ajiye gulmarsu, don mafi akasarin masu shigowar sun jinjina yanda Dijen take gayar da su cikin ladabin da basu santa da shi ba, uwa uba yanda suka ga jikinta ya murje kyawonta ya ƙara fitowa duk da take baƙar fata.

Kwanan Dije biyar a garin sai ga Abinci Garbati da kanshi ya yi sallama har ƙofar gidansu Dijen ya kawowa Dije inji Jummala, mamaki fal ranta daga ita har Inna saboda ta bata labarin abunda ya faru tsakaninsu, don ma tsabar renin hankali har da cewa wai don ALLAH ta je Jummala tana son ganinta, Dije tana ganin Inna ta shige bayi ta yi ficewa ta kira yaron da Garbati ya baiwa ya kawo mata abincin har ya yi nisa, ta miƙa masa tace ya je yace da shi bata so ai ita ba mayunwaciya ba ce.

Yaron ya karɓa ya tafi ta tsaya soron tana jiran dawowarshi don kada ma Inna ta ji ta yi faɗan me yasa ta mayar, aiko madadin ta ga yaron sai ga shi ta ji sallamar Garbati, ta yi saurin fitowa ta tsaya gaban Garbatin ta riƙe ƙugu tana girgiza ƙafa tace

"Yawwa daman ai kai nike jira abincin me ne ka kawo man? ance maka ina da yunwa ne ko kuwa??"

Garbati ya marairece fuska ya ce,. "Nasan nayi maki abunda bai kamata ba amman don ALLAH ki yi haƙuri, WALLAHi naji daɗin zuwanki wurin Jummala kin ga yanzu zamanmu muke yi lami lafiya, WALLAHi na gode sosai da ƙoƙarinki ALLAH ya biyaki da gidan Aljannah"

Dije dole ta ajiye makaman rashin kunyar da ta tanadar masa tace,. ,"Na yafe amman ku bar abincinku na gode"

Tana ƙare faɗar haka ta koma gida abunta, Garbati bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake nemo yaro ya ƙara aika mata da abincin sannan ya tafiyarshi, zuciyarshi cike da jin haushin mummunar fassarar da ya yi mata.

Dama ka bani idan bata so ni ina ci😔

Akafta😆

D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*AM BACK MY FAN'S😉*

*Lamba ta 40*

Shigar yaron ya yi dai dai da fitowar Inna daga bayi, cike da mamaki ta bi Dije da kallo har yaron ya ajiye kwanon abincin ya fice, Inna zata yi magana Dije ta yi saurin faɗin

"Mayar masa da abincinsu na yi shine ya dawo da shi"

Inna ta ɓata fuska tace,. "Ba'a mayar da hannun kyauta baya ko baza ki ciki ba sai ki kyautar ya fi da ace ki maida"

Dije ta miƙe tsaye tana dariya tace,. "Bale ma zan ci ai abincin Jummala ne don haka zan ci inji in ta iya girkin"

Inna ta maka mata harara tace,. "Au kina ma so amman shine kika mayar? to ALLAH ya kyauta amman ko ba yanzu ki daina mayar da hannun kyauta don wannan yana daga cikin aikin sheɗan"

Dije tana wanke hannunta tace "insha ALLAHU Inna bazan sake ba, yanzun ma don ya gano naji haushin abunda ya yi mani ne"

Dije ta zauna ta fara cin abincin tana yi tana rawa da kai tace "Inna ko ashe da gaske Jummala ta iya girkin"

Inna ta yi banza da ita kamar bata ji ta ba har sai da ta gama sannan tace da ita, "Shin wai ke kin fara koyon abincin ƴan'birnin ko kuwa har yanzu irin namu ne kawai kika iya? "

Dije tana lashe hannunta tace, "Ni fa Inna Makaranta nike zuwa kuma a cen ma muke kwana har sai anyi hutu nake dawowa gidan, kuma idan na dawo Hajiya bata bari in yi wani aikin wahala, cewa take yi wai in huta kafin in ƙara girma sai a fara koya man girkin"

Inna ta yi shiru sannan tace,. "Idan kin koma ki dinga shiga cikin masu dafuwar abincin gidan kina kallon yanda suke girkinsu, ko da tace ki zauna ki huta ki ce da ita ke kina son ki iya kinji ko? Sannan ita kanta ki dinga share mata ɗakinta kina gyarashi tsaf tsaf yanda kika ga ana yi mata"

Dije ta ɓata fuska tace, "To ai tana da mai yi mata gyaran ɗaki, har ma da bayinta duk akwai masu wankewa kullum"

Inna tace,. "To idan kin koma ki karɓi komi ki dinga yi mata da kanki, girkin ma ki shiga cikin masu girkawa kuna yi tare don ki ga yanda ake yi"

Dije ta turo baki tace "Don Allah Inna ki bari kawai Surry ta koya man, tunda naga itama watarana tana shiga ta yi girkin idan saurayinta zai zo fira, sai dai kuma su fa da wata ƙatuwar akwati suke sanwa a kai, baki ganshi ba da murhun ɗora girki ya kai shida ko bakwai fa, to ni har yanzu ban ma san ta yanda ake kunna abun ba, saboda da wutar lantarki ma naga ana aiki da shi"

Inna tace "To ki dinga koya kinji kinga abincinsu daban da namu, idan baki iya ba sam ba zaki ji daɗin zama cikinsu ba, kuma kinga Mijinki ɗan gayu ne yana buƙatar ace komi kin iya irin nasu, idan kuma ya ga baki iya komi ba sai ya auro wata matar wadda ta iya abubuwa irin nasu, kin ga shikenan sai ta karɓe mijin ta barki sake da baki tunda baki iya komi ba"

Dije ta yi shiru sannan tace,. "Ai ni Inna ko don renin hankalinshi ma dole in koya kafin ya dawo, amman fa gaskiya in yace zai auro wata bayan ni yasin sai naci Uban ko ma wacece inna"

Inna ta zaro ido waje tace, "saboda mi? Ko ance maki ke kaɗai ce ALLAH ya halastawa ya zauna da ke? To kul kar in fara jin wannan shirmen gareki, don jikina yana bani yanda yake ɗan birnin nan ba zai zauna da ke ke kaɗai ba matuƙar ba kin iya komi na yan birnin ba, don haka idan har baki son ya ga wata ya sake aurowa to ki natsu da kyau ke ma ki zama yar gayu kamar su, ki dinga wanka kamar yanda suke yi, ki iya girki irin nasu, ki iya kwalliya irin ta su ke tafiya ma idan kin so zaki iya maidata irin tasu, saboda kawai ki zamo dai dai da mutanensu don kawai ki ƙwatowa kanki ƴanci, ki rage yawan surutu da faɗi ba'a tambayeki ba, ki zamo shiru shiru sannan ki dinga komi cikin natsuwa ba rawar jiki ko ƙiriniyar da kika saba yi anan ba, sannan kar ki yi wasa da ibada kamar yanda kika koya tun nan gidan, idan ma da hali ki dinga yin azuminki na Litinin da Alhamis don samun nutsuwar zuciya"

Dije ta yi shiru tana ta wassafa duk abubuwan da Inna ta faɗa a ranta, sai cen ta yi ajiyar zuciya tace

"Ai Inna na fara koyar wasu abubuwa, kinga ko kwalliyar garinmu da nake yi acen yanzu duk na daina yi, saboda Surry tace in ina yi mutane zasu gano cewa wai daga ƙauye na fito su rena ni"

Inna tace,. ,"To ki yi ƙoƙari ki yi ta koyar abubuwa irin nasu kafin Mijinki ya dawo, saboda kawai idan ya zo ki yi masa bazata don na tabbata ba ƙaramin so yake yi maki ba, tunda har ya aureki a yanda ya ganki bayan akwai ƴanmata da yawa a cen birnin, amman duk ya tsallake kowa ya aureki"

Dije ta cire tagumin da ta yi tace, "Ni WALLAHI sai in ga shi baya sona ma kamar Malam Lawi, don yafi sona da shi nesa ba kusa ba, don dai shi baki ga yanda yake ta hantarata ba komi na yi ya yi ta gwasaleni yana katsa man tsawa, watarana ma har dukana yake yi fa"

Inna ta yi saurin faɗin,"Ni kaina da na haifeki ai idan kika kaini bango watarana ina dukanki ko kin manta ne?, To shikenan don kinyi laifi na dokeki sai ace ban sonki? Saboda haka idan kina son ki ƙwato ƴancinki gareshi to ki zama mace kamar sauran matan garinsu kafin ya dawo, in da hali ma har ki fisu natsuwa da kamun kai har ma da gayun gaba ɗaya, ke ko ki ga yanda zai dawo yana lallaɓaki don gaban kowa baya shayin nunaki matuƙar kika zama yanda yake so, sannan kika zamo dai dai da yanda na lissafo maki, amman idan kina wannan shirmen me zai hana ya jibgeki ko?, tunda ke kanki kinsan kunnuwanki ba jin magana suke yi ba"
Chapter 39 · 0% Book details