← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 84

Sashe 55

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dije ta fito Inna da Hansai da Baffah suka biyo bayanta suna yi mata ALLAH ya kiyaye hanya, sai da Baffah da kanshi yace da shi don ALLAH ya biya da ita ta yi sallama da Inna Gambon, cike da jin daɗi ta shige motar tana yi masu bye bye suna yi mata har suka bar ƙofar gidan, kai tsaye Safwan ya nufi gidan Maigari bayan sun gaisa sama sama ya yi masu alkhairi suka nufi gidan Duduwa tana nuna masa hanya, yara suka biyosu buuuu! A baya suna yi masu Allah ya tsare.

Bayan sun gaggaisa da Gambon ne itama ya yi mata alkhairi sannan ya fita, cikin barkwanci ta dinga tsokanar Dijen, sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko wani abu a gorar lacasera tace ta sha rabi ta ajiye rabi daga baya ta shanye, Dije tana dariya ta kwankwaɗe abun duka ta yasar da gorar tana goge baki tace

"Haka kawai ki saka man wata doka cen marar tushe?, To yanzu dai na shanye sai inga kuma wani fi'ilin da za'a yi man"

Ta ƙare maganar tana dariya, Gambo riƙe da baki tace

"Ni ai tausayinki nake ji shiyasa kika ji nace ki raba biyu, saboda takanas na dafa maki shi da hannuna dalilin da yasa na yi ta aiken ki zo mu yi sallama, amman tunda ke jaruma ce ALLAH ya baki ikon jurewa"

Dije tana dariya tace

"Na shiga uku Gambo me yake sakawa ne???"

Gambo ta ce "idan kun zo kwanciyar auren zaki gane da kanki"

Dije ta ƙyalƙyale da dariya tace "Oh Ni Dije ai ke Gambo ni ba wata kwanciyar aure da nike tsoro, tunda asali ma Ni ba a ɗaki ɗaya muke kwana ba balle har ayi kwanciyar"

Gambo ta maka mata wata uwar harara ta ce, "to wannan karon WALLAHi kika gudo sai munyi maki bankaɗa a garin nan"

Dije zata yi magana taji horn ɗin motar da ƙarfi, ta fito tana dariya Gambo ta biyota a baya har wurin motar, in da suka taradda Balan Duduwa tsaye da Safwan suna magana, sai zuba fadanci yake yi yana godiya, wanda ba'a raba ɗaya biyu akan kamar ma kyauta ce Safwan ɗin ya yi masa yake godiya, Gambo tace da Dijen

"Kada dai ki mance ki tambayeshi abunda kika taɓa tambayata ko kin mance in tuna maki?"

Dije ta bud'e motar ta shiga ta zauna tana dariya tace,, "ai kuma yanzu wannan ya wuce Gambo tunda wadda ma aka yi abun kanta yanzu har ta mance da ma an taɓa yimata laifin, to ni kuma miye nawa na bin diddigi yanzu? ALLAH dai ya bamu haƙuri dukanmu"

Gambo tace "Ameen amman ya kamata kema ki tambayeshi saboda akwai ƙaruwa a ciki idan kin sani"

Dije tace "Tom naji Ni dai matsa kada mu tureki ki yi kuka"

Gambo ta dungure mata kai tace "kece dai wadda zaki yi kukan amman nikam me zai haɗani da kuka yanzu?? Sai dai kuma in na farin ciki idan ina da rabon ganin yaran da zaki haifowa"

Haka suka rabu Dije tana ta ƙyalƙyala dariya suka baro ƙofar gidan suka kama hanyar fitowa garin, Safwan yana kallonta sai dariya take yi ita kaɗai, sai cen kuma ta fara matsar ƙwallah cike da mamaki yace

"Kukan fa?"

Tace "WALLAHi kamar kada in baro garinmu gashi ma kowa banje gidanshi ba tunda na zo"

Safwan ya yi murmushi yace, "to ai gara da baki je ba saboda kada zunubin ya yi maki yawa, kin zo ba izinin miji kuma ki kwashi ƙafafuwa ki fara bin gidaje, ai sai ki janyo Mala'iku su yi ta aikin rubuta yawan zunubinki"

Dije ta share hawayenta tace, "ai dai yanzu ka yafe man ko?"

Ya yi yar dariya yace, "na yafe amman Ni ma zan fanshe wahalar da aka sakani, sannan Ni ma in nemi yafiyarki idan na fahimci abun zai janyo man aljanun tekun banbaradusa"

Dije ta yi saurin kallonshi tare da rufe bakinta tana dariya tace, "WALLAHi ba ruwana in har su mulƙutus baraƙus suka jiyoka, don tsaf zasu iya yin langaɓu da kanka a bakin tekun bangon duniya"

Ba shiri Safwan ya yi dariya saboda ba ƙaramar dariya ta bashi ba, amman ya waske yana yi a hankali don maganar da ta yi ce tasa ya tuno da labarin da wani ɗan Maigarin ya bashi nata, lokacin da ta yi ƙaryar aljanu a ƙofar gidan Maigari, musamman abunda ta yi wa Bafade ba ƙaramar dariya yake bashi ba idan ya tuna.

Ganin kamar dariyar taƙi ƙarewa ne saboda murmushin kawai yake yi yana dariyar a hankali, shi yasa ta ɓata fuska tace

"Wai yau kai ne kake dariya haka? Daman kana da fara'a shine kullum kake faman haɗe fuska??"

Safwan ya ci gaba da dariyarshi ba tare da yace da ita komi ba, itama ta yi shiru tana kallon gefen titi har suka shiga babban birnin garinsu Dijen, har sun wuce wani wuri ya dawo baya yana kallon bakin titin yace

"Ga mutuniyarki cen ta fito ko yau bazaki ci ƙosan ba? Ga wani abu cen ma tana suya da alamu shima zai yi daɗi"

Dije ta kai kallonta ga mai soya ƙosan dake bakin titi tace, "me ye abun da take soyawar? ba doya da ƙwai ba ce nake hangowa?? "

Safwan ya gimtse dariyarshi yace, "itace jirani bari in zo"

Ya fice Dije ta bishi da kallo tace, "Ni da ma ka barsu don ko ka saya ba ci zanyi ba ma"

Tana kallonshi har ya dawo da ledodin ya buɗe gefen da take ya ɗora a saman cinyarta, ta yi saurin zabura saboda ruwan team ɗin da suka zubar mata a jiki, sannan ya rufe ya zagayo ya shiga ya tada motar, ta bishi da kallo tare da ɓata fuska tace

"Me nayi maka da zaka ƙonani da tea??"

Yana kallon gabashi yace, "ke fa na siyowa duka ko baki so?"

Dije ta ɗauki kayan ta ajiye a bayan seat tace , "Ni bana sha'awar cin komi a ƙoshe nake"

Yace "ok to tunda kin ƙoshi Ni ki bani zan ci ai"

Ta yi saurin kallonshi tace, "da gaske kake yi zaka iya ci?"

Ya waigo ya kalleta yace, "to me zai hana yana da wani abun ne?"

Ta yi saurin faɗin "a'a"

Yace "to oya a fara bani ga bakin nawa yana jira"

Dije cike da mamakinshi ta ce "me zaka fara ci a ciki"

Ya ce "abunda kika san kin fara ci farkon lokacin da muka fara siyen irinsu"

Dije ta yi saurin kallonshi tace "ƙosai shi za'a baka?"

Ya ce "Yes! In jira ko rowa za'a yimani ne in haƙura?"

Ta sauke tagumin da ta yi tace, "ALLAH ya baka haƙuri ai abun bai kai cen ba, don kare da kuɗinshi ba za'a hana shi shan rubutun malam ba"

Ya yi saurin kallonta yace "au haka ne?"

Tace "eh kam yanda kowa ya siya ya sha haka shima za'a bashi tunda har da kuɗinshi a aljihu"

Ya yi shiru sannan yace, "nyc! Kice haka abun yake? to in fa shi malamin yaki siyar masa fa kuma bayan ya karɓe masa kuɗin?"

Ta yi saurin faɗin

"Bama zai ƙi siyarwa ba tunda dai ba kyauta aka ce ya bayar ba, sai da aka bashi kuɗi ya karɓa aiko ya zama dole ya bada ko yana so ko baya so"

Ya yi saurin faɗin "woww! Ki ce Ni nawa shan rubutun zai zo man cikin ruwan sanyi"

Tace "tabbas amman ka gwada ka ga in har kana shakku a maganata"

Ya yi saurin kallonta tare da yin wata siririyar dariya yace, "hmmm! ALLAH ya bani sa'a to"

Tace "Ameen"

Hmmmm nima dai nace Ameen ɗin don tsuntsun da ya ja ruwa ..............😝ku ƙarasa mata ni dai na yi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️

Not edited

Akafta😹

D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Sai kun yi haƙuri dani kwana biyun nan saboda uzurora da suka sha kaina, amman insha ALLAHu zan ƙoƙarta in yi maku ko ba yawa, sai dai ina son ku yi man uzuri idan kuka jini shiru ba ba daga gareni bane kamawa ta yi*

*Lamba ta 53*

Haka ya buɗe baki tana ta bashi ƙosan yana ci yana tuƙinshi hankali kwance yana jin kanshi cikin wani sabon nishaɗi, don ko tea ɗin ba ƙyama ba wata damuwa ya karɓa ya dinga shan abunshi, ƙarshe ma itama sai da ya tilasta mata ta ci kaɗan sannan ta buge tana ta bacci abunta, don kuwa tun tana kallon gefen titin tana ta wassfa kunya zata ji idan ta je wurin Hajiya Mama, don sai yanzu take hango rashin dacewar abunda ta aikata, saboda ƙiri ƙiri ta haramtawa kanta tsayawa ayi bikin Surayya da ita, tana cikin tunanin ne taji wata muguwar kasala ta sauko mata a jiki, sai gata da jera hamma kala kala Safwan dai sai tuƙinshi yake yi yana kallonta ta gefen ido har baccin ya yi awon gaba da ita.

Tun daga babban birnin garinsu take ta sharara bacci mai shegen nauyi har ta kwashi kusan awa biyar bata falka ba, shima tun yana ganin baccin gajiya ne take yi har ya fara tsarguwa da baccin nata, dole da suka je wani gari ya sauka ya tada ita cikin mayen baccin suka ci abinci suka yi salloli sannan suka sake ɗibar hanya.

Tafiya tana miƙawa ta ci gaba da baccinta har suka kai Gombe bata san sun kai ba, saboda misalin sha biyun dare ne har da wasu mintuna sama suka shiga garin, daman yasa anyi masu booking ɗin wani hotel suka sauka da nufin da safe su kama hanyarsu ta zuwa Yola.
Chapter 55 · 0% Book details