← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 84

Sashe 35

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna cin karo Inna ta zaro ido cike da mamakin ganin Dijen tare da buɗe baki saboda tsabar farin ciki ta ma rasa me zata faɗa, Dije kam tsalle ta yi ta ruƙunƙumeta tana faɗin

"Wayyo ALLAHna daɗi kasheni gani ga Innata, yi huhu ina Baffahna ALLAH yasa yana gida"

Ta saki Inna ta yi cikin gidan aguje sai dai dole ta ci ƙaton birki saboda ganin ɗakin Baffahn a rufe, cike da jin haushi ta ɓata fuska ta nufo Inna da ke ƙoƙarin dawowa cikin gidan tana faɗin

"Bari inje in dubo Baffahna Inna idan mutanen sun shigo ki basu ruwa kafin ina dawo"

Inna ta yi saurin faɗin

"Au! Ki ce ba tare da mijin kaɗai kuka zo ba? To ki jira mana yana ƙofar gidan Maigari yanzu a je a kirashi ai tunda......"

Maganar ta maƙale ne saboda ganin yara sunata shigowa da buhuhunan shinkafa tare da sauran kwalaye, Inna ta bi yaran da kallo riƙe da baki zuciyarta cike da tsantsar farin ciki, sai ga sallamar su Hajiya Mama da su surry, da sauri Inna ta juya tare da washe baki cikin rawar jiki ta nufi ɗaki ta ɗauko sabuwar tabarmar ta shimfiɗa masu a kofar ɗakinta da yake share fess! Da shi, tana tambayarsu ya hanya tare da yi masu barka da zuwa, cikin sauri ta je ta ɗebo masu ruwa ga tulunta mai shegen sanyi cikin babban kwanon sha sabo dal, tayi masu farau faraun fura ta miƙa masu sannan ta dinga taimakawa yaran da har lokacin basu daina shigowa da kayan tsarabarba.

Dije kam tana samu ta fice ta nufi ƙofar gidan Maigarin ƙawayenta su Lanti da Hansai da Mune suka biyota kowa yana ƙoƙarin ya dai samu ya riƙa hannunta, ita ko sai wasar baki takeyi tana faɗin

"Hansai da Lanti kuna nan ku har yanzu baku yi auren ba ashe? Ina Jummala ko anyi mata auren?"

Mune tayi caraf tace,

"Ko sati biyu ba'ayi ba da aurenta ai, sai dai kam ko jiya da naje na isketa sai kuka take yi, ke baki ma sani ba tun ranar da aka kaita ta gudo cikin dare ta dawo gida, wai ita bazata kwana da Garbati ba tunda ɗan'iska ne"

Dije ta yi saurin faɗin

"To faɗi ba'a tambayeki ba, wai ke Mune har yanzu baki daina gulmar taki ba?, To ke yaushe za'ayi maki auren ne?, Amman dai Ni dai WALLAHI ina baki shawara ki daina yawan gulma nan kada watarana ki janyowa kanki a lakaɗa maki shegen dukan tsiya"

Mune ta yi shiru zuciyarta a cunkushe tace, "Ai gaskiya ce na faɗa WALLAHI ki ma tambayi su Hansai ki ji in nayi ƙarya"

Dije tace "Ni dai fa bance kinyi ƙarya ba amman na ce ki rage yawan surutunki na tsiya da baƙar gulmarki da kika saba, don Ni dai WALLAHI banga laifin Jummala ba haka kawai a kaika wajen Namiji ace ku kwana ɗaki ɗaya, don kawai salon ya lalataka azo daga baya ana faɗin ka zama ɗan'iska"

Hansai ta ƙyalƙyale da dariya tace,. "Cafɗi Ni ma fa wai an kusa aurena da Usmanu, amman Ni dai yasin har na matsu ayi a ƙare saboda nasan shi Usmanu ba ɗan'iska bane, Jummala dai kam sai haƙuri tunda Garbatin ya riga da ya tanbaɗe sai neman shiriya"

Lanti kam da tunda ake ta surutun bata ce komi ba, cikin sanyin jiki ta sauke ajiyar zuciya tace

"Ni WALLAHI har ma tsoro auren yake bani musamman yanda Jummala take ta kuka duk dare sai ta gudo Gidansu ana maidata, ni na rasa me ma Garbatin yake yi mata da har take jin tsoronshi"

Cikin tsananin tsusayin Jummalar Dije tace
"wai ina Ladiyo ita dai ai suna zaman lafiyarsu ko?"

Mune ta yi saurin faɗin "cabɗi ai billahillazi ko jiya sai da na taraddasu suna ta kokawa Duduwa tana rabasu suka ƙi bari, Bala sai zagin Ladiyo yake yi wai sai ta biyashi kuɗinshi da ta sata"

Dije da suke tafiyar a hankali suna firar ba shiri ta ja ta tsaya, cikin sabon ɓacin rai ta ce

"Wai kunsan wani abu kuwa??"

Dukansu suka ce "A'a"

Ta dafa kafaɗar mune tace,. "Na dafeki da alkhairi yau halinki zai yi man rana ko da ko ban biya kwandala ba, karkaɗe kunnenki da kyau kiji Mune Bala dai ashe kuɗi Malaminmu ya bashi shiyasa ya janye zancen aurenmu da shi aka ɗaura da Malam Safwan, ashe daman cen ba son ALLAh da Manzonsa ya ke yi man ba, don haka ki je ki yi ta yamaɗiɗi da wannan zance Mune na baki kyauta, kar ki yi sanya ina son kafatanin wannan garin kowa ma ya san da wannan sirrin da Balan Duduwa ya rufe lokacin aurena dashi, ki bankaɗe komi ƙawata kinji? Tunda har shi ya zama baƙin zalamammen banza kwaɗayayye"

Ba Mune da Dijen ta ke baiwa labarin ba har su Lanti sai da suka jinjina irin abunda Bala ya aikata, Dije zata sake yin magana kenan ta hango Baffah'nta da yake ta sauri tun daga nesa Bakinshi a washe, wanda ko tantama babu akan cewa labarin zuwan Dijen ne ya kai gareshi, aiko aguje ta zanƙara da gudu ta nufeshi tana faɗin

"Wayyo Baffahna Oyoyo Oyoyo wallahi nayi missing ɗinka"

Tana zuwa ta faɗa jikinshi, shi ma cike da tsananin jin daɗin ganinta yace

"Baƙin birni sannunku da zuwa yanzu nake ji ashe ko da gaske Dijengalata ce ta zo ganina"

Ya riƙo hannunta suka nufi gidan sai tsalle take yi tana wasar baki tana murna, su Lanti suka bi su a baya Hansai kam ta doje ta yi gida saboda kunyar surukuta da take yi da Inna Hasiya.

Ko da suka shiga sun taradda Hajiya Mama da su Surry cikin ɗakin Inna sun gama SALLAH, Inna ko sai haɗa wuta take yi tana jefa masu ɗanwaken da ta gama kwaɓashi a gaggauce, don kawai ta sami abun tarbar baƙinsu da shi saboda ita dambun gero ne ta yi tana ganin idan ta basu ƙila ba za su iya ci ba.

Baffah ya isa ƙofar ɗakin cikin farin ciki yayi masu sallama, sai da suka amsa sannan ya shiga yana yi masu sannu da zuwa tare da tambayarsu ya hanya?.

Cikin mutunta juna suka gaggaisa sannan ya fito Dije ta biyoshi a baya tana faɗin

"Baffah banga yaya Usmanu ba"

Ya waigo zuciyarshi fess yace

"Tun da safe ya je birni cin kasuwa kinsan yanzu a cen yake kasa kayan koli yana sai dawa tun lokacin da muka dawo garin Mijinki"

Dije ta washe baki tace,. "ALLAH sarki yaya Usman ashe an kara sanin ciyon kai"

Inna da take dakan toshshi ta goge fuskarta da jiɓin da feso mata tace,.

"Saura k'iris ma ya rage ayi aurenshi kinga shikenan kun zama ɗaya ba zancen wani gori bale har nan gaba ki ɗauka cewa ke ce yayarshi tunda kina ganin kin rigashi aure"

Baffah ya maka mata harara yace, "ko yau aka yi auren ai dai na Dije ne aka fara yi, don haka a daina yi muna wani feleƙe tunda har mu mun riga da mun yi ɗin ai kuma mun wuce wurin"

Dije ta washe baki tace,. "Shiyasa kullum sai nayi mafalkinka Baffahna saboda duk garin nan kafi kowa sona"

Mama Hajiya da ke ɗaki tana ji yo su ta yi murmushinsu na manya zuciyarta cike da sha'awar ahalin sabida barkwancinsu da kusan rabi duk Dijen garesu ta gado, uwa uba ma sun burgeta saboda ganin yanda suke nagartattun ma'aurata masu son farantawa junansu cikin barkwanci.

Fiddo kam sai yatsine yatsine take yi tana ƙarewa ɗakin Inna kallo, Hajiya Mama tana yi tana yi mata kashedi da ido amman duk da haka sai ta fakaici idonta ta yi guntun tsaki.

Baffah ya koma waje inda aka shimfiɗawa Direban tabarma gindin wani iccen dake ƙofar gidan, yana shan iska, ya zauna suka sake gaisawa a tsanake.

Dije ta nufi wurin Inna ta karɓi taɓaryar tana daka toshshin su Lanti suka karɓe suna daka mata, suna ci gaba firarsu ta yaushe gamo.

Bayan Inna ta kammala ɗan'waken ta zubawa Hajiya Mama ga sabon kwanon Samira, su Surry ma kowace da sabon kwanonta haka ma Direban da suka zo da shi, Dije kam dambun geron ta ɗauko ta fara ci Surry ta ce ta zo su ci ta ji don k'amshin dambun sai kai mata yakeyi a hanci, duk da ko shi kanshi ɗan'waken ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, aiko tana guma lomar dambun ta yi saurin faɗin

"Uh! uh! uhm!"

Sai data haɗye sannan ta ce "cabɗi ashe Khadijah da wayo kika so ki yi man wannan abu da daɗin gaske yake yasin"

Sai ci take yi abunta babu ƙyama cikinsu Dijen da Lanti da Mune da suka fara ci tare, Inna da su ko sai faman dariya suke yi mata da ma suka cenye Inna ta ƙaro masu sannan Baffah ya shigo da ledar ruwan sanyi har suraci suke yi, tare da lemuka irin na ƴan'birni da ya bada aka siyo masu babban garin da ke kusa da su.

Fiddo kam zurum ta yi tana kallon kwanon abincin ta kasa ci, Hajiya Mama da ke ɗakin Inna tana cin abincinta hankalin kwance, ta kalleta tace

"Ke ba zaki ci abincin ba ne??

Fiddo ta turo baki ta ce

"Gaskiya Ni bazan iya cinshi ba ku dai ku ci idan mun fita wannan ƙauyen sai a siyo man wani abu sai in ci"

Hajiya Mama ta wulla mata wata ƙatuwar harara ta ce

"WALLAHI muddin baki ci ba to har mu koma gida bazaki ci komi ba"

Fiddo cikin tsananin ɓacin rai ta ɗauki cokali ta ɗauko ɗan'waken cikin ƙyama ta kai bakinta, sai gashi yayi mata bazata don kuwa wani daɗi ne ya ziyarci halshenta, ta haɗiye ta ƙara kai wata loma Hajiya Mama tana kallonta ta gefen ido, aiko kafin ka ce me har ta kusa tayar da kwanon ɗan'waken, don kuwa har da su cire ɗankwali tana ƴar waƙa tana rawa da kai.

Ni dai kar ki cenye ki raga man fiddo☹️

Kuyi hkr dani kwana biyu na shiga rububi ne😆

Akafta🧐

D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
Chapter 35 · 0% Book details