← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 84

Sashe 72

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu zame ko'ina ba sai wata haɗɗaɗiyar Restaurant yasa aka yi mata odar abinci kala kala, Dije ta ƙi ci ta ce dole sai dai su ci tare, ba don ya so ba ta dinga ciyar da shi yana ci itama yana bata tana ci har suka yi ƙat! Sannan ya biya Bill suka nufi wata plazar suka sissiyo kayan tanɗe tanɗensu da maƙulashe sannan suka dawo gidan, duk da a ƙoshe su ke amman hakan bai hanasu sake cin gasashiyar kazar da suka siyo ba, tare da korawa da abun sanyaya maƙoshi, bayan sun kammale ne suka je suka yi wanka suka kwanta, duk da hannunshi da ke ciyo bai hanashi sakin jiki ya sake angwancewa da matarshi ba, saboda a yanda yake ji ko kaɗan ba zai iya haƙura da ita ba a wannan lokacin, haka suka raba dare suna farantawa juna har sai da ita kanta ta ji tausayinshi saboda yanda yake ta shan shagalinshi ba tare da ya yi duba da ciyon da ke hannunshi ba.

Ko da safiya ta waye Dukansu cikin farin ciki da ƙarin ƙaunar junansu suka ta shi, bayan sun yi break ma haka suka sake komawa cikin duniyar ma'auratan sannan dukansu bacci mai ƙarfi ya yi awon gaba da su.

Kiran wayar da ake ta yi masa wani bayan wani ne yasa ya yi saurin falkawa daga nannauyan baccin da ya ke yi, cikin yin wani uban tsaki tare da jin haushin da bai sakata a silent ba, ya miƙe ya ɗauko wayar ganin baƙin numbobi barkatai yasa ya yi saurin zaunawa, sai ga wani kiran ya sake shigowa da sauri ya ɗaga, sai ga wani ƙanen mahaifin Zee yana sanar da shi gasu cikin gidanshi sun zo suna son yin magana da shi.

Cikin jin haushi ya kalli Dijen da ke ta baccinta hankali kwance, ya yi wani murmushin jin daɗi saboda ni'imar da ya kwasa a jikinta, ya yi mata wani kiss a iska ya hura mata sannan ya miƙe ya je ya yi wanka ya saka doguwar jallabiya baƙa ya ja talkamanshi plat ya fice tare da janyo ƙafa a hankali don kar ta tashi.

Ganin baƙin motoci biyu tare da dattijan mutanen yasa ya shiga cikin natsuwarshi, ya isa wurinsu suka gaisa sannan ya yi masu jagora har sashenshi inda babban falon tarbar baƙinshi ya ke, bayan sun zazzauna ne aka sake gaisawa sannan suka sanar da shi sun zo akan su ji ba'asin abunda ke faruwa, don yanzu haka Mahaifin Zee yana kwance asibiti hawan jininshi ya ta shi, saboda abunda ya ji da kunnenshi da wanda ya saurara a gidan Tv..

Saboda ƙarin jawabin da su Ruma suka zo masu da shi na cewa Zee tana hannun ƴansanda, sannan da labaran da aka gabatar a gidan TV dangane da case ɗin masu ɗauke da rahotannin tabbatar da faruwar hakan daga bakin Safwan ɗin da kuma su Surayya da Ruma da sauran ƴan'uwanta duka da aka ɗauka, a daren jiya wanda kuma a ranar aka watsashi a gidan television, wanda ya watsu cikin mintuna ƙalilan tamkar tashin bom ta ko'ina labarin ake yi, sai dai ba'a nuna fuskokin kowa ba don Safwan ne da kanshi ya ce kada a bari fuskokinsu su bayyana saboda tsaro, amman duk da hakan labarin ba ƙaramin shiga zuciyar mutane ya yi ba, musamman wanda yasan ita Zee ɗin da su Safwan ɗin su ma, shiyasa mutane suke ta kiranshi don kawai su ji tabbaci wasu kuma don su jajanta masa.

Ba tare da jan wata doguwar magana ba Safwan ya bayyana masu abunda ya sani da wanda ya ji a bakin Surayya da kuma Ruma, sannan ya yi masu jagora har falonshi na ciki inda aka yi abun wanda har lokacin akwai warin fetur ɗin duk da ya bi iska sosai, cikin sanyin jiki suka dinga bashi haƙuri don sanin da suka yi tabbas Zee bata da gaskiya, sannan suka nemi alfarmar a basu Zee su koma da ita gida saboda Mahaifinta da ke unconscious, ya ce sai dai aje gun Hajiyarshi duk abunda ta ce shikenan, dole suka ɗuru mota suka nufi gidansu Hajiyarmu, bayan an gaisa ne suka fara bata haƙuri kan abunda ya faru sannan suka nemi alfarmar inda hali suna son a janye wannan case don ALLAH kada a bari ya je kotu, ganin girmansu yasa ta ce da su ba komi insha ALLAHu ba za'a je kotu ba indai har itace ta haifi Safwan, cike da jin daɗi suka baro gidan suka nufi Police station ɗin sai dai duk yanda suka so a basu belin Zee hakan bai samu ba, don shi kanshi Safwan ɗin sun nuna masa tunda aiki ya zo hannunsu ko ya janye su bazasu janye ba, don case ɗinta ba ƙaramin case bane bale har a yi gaggawar kasheshi cikin ƙanƙanin lokaci, dole suka haƙura suka koma ba tare da ko ganinta sun sami damar yi ba, don a zahirin gaskiya Zee tana cikin mawuyacin hali saboda yanzu haka tana Asibiti maƙale da oxcegyn saboda azabar da ta sha a hannu ƴansandan.

Tsawon sati biyu dangin Zee suna ta sintiri tsakanin Gombe da Yola akan su samu a kashe case ɗin, da ƙyar suka yi nasarar karɓota a hannunsu bayan uwayen miliyoyin kuɗin da suka narka saboda kawai a kashe case ɗin ba sai ya je kotu ba, don shi Safwan kallonsu kawai ya ke yi saboda shima kanshi da kalar na shi takun a ciki, don gurinshi na son ta gane kuskuren da ta aikata, don har lokacin bai cire takaicin dawo da itan da Hajiya Mama tasa aka yi ba, shiyasa ya nemi alfarmar Hajiyar akan a barta ta je gida har sai ya nemeta, haka ko aka yi sun karɓota aka kaita wurin Hajiyarmu ta bata haƙuri sannan ta baiwa Safwan da Dijen haƙuri suka kwasheta aka nufi Gombe da ita, inda ita kanta ta ji ina ma ace akwai wani garin da zata je ba cen Gomben ba, don tasan muddin ta je cen dole ne ta fuskanci ƙalubale ba kaɗan ba wajen ƴan'uwanta musamman masu goyon bayan Aminu.

To fa sai hkr Zee😊

Akafta🙌🏻

D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆*

*Lamba 66*

Zee durƙushe ƙasa tana kukan fitar hankali gaban gadon da Mahaifinta yake kwance gorar ruwa saƙale a hannunshi, ya yi shiru yana sauraren sautin kukan nata, zuciyarshi cike fal da wata sabuwar damuwa don abunda ta aikata da saƙon da Safwan ya isar masa ba ƙaramin dukan zuciyarshi suka yi ba, duk da ko an sanar da shi cewa ya mayar da ita a matsayin matarshi, amman har wannan lokacin bai dawo cikin natsuwarshi ba, wata ƙanwar Mahaifinta ce mai suna Baabaah Asabe ta katsa mata wata uwar tsawa ta ce

"Zaki ta shi ki bar ɗakin nan ko sai kin iyar da kashe muna ɗan'uwa ne?"

Zee ta miƙe jikinta yana rawa dafe da bakinta tana toshe kukan da yake fitowa tana kallon Daddynta bata son fita, cikin wata sabuwar tsawar Baabah Asabe ta sake cewa

"Ki fita na ce ko sai na fiddaki da ƙarfi ne?"

Zee ta dinga ja da baya tana gunjin kuka za ta fice Daddyn ya ɗaga hannu ya yafitota alamun ta zo wurinshi, da sauri ta dawo jikin gadon ta tsaya tare da riƙe kan gadon tana toshe kukan da ke ta fitowa a bakinta ta ce

"Don Allah Daddy ka yafe mani nasan na yi kuskure ka yafe man......."

Ya riƙo hannunta hawaye suna zuba akan fuskarshi ya ce, "me yasa kika aikata abinda zai janyo muna surutu a bakin mutane?"

Zee ta riƙe hannunshi gam ta durƙushe ƙasa ta ce "plss Daddy ka yafe mani abun kunyar da na janyo maku don ALLAH"

Baabaah Asabe ta fisgota da ƙarfi ta fiddata ɗakin sai da ta yi nesa da ɗakin Daddyn sannan ta wurgar da ita cikin fushi ta ce

"Na ƙara ganinki a ɗakin nan sai na baki mamaki WALLAHI, abun kunya kuma da kike so ayi haƙuri kanshi ke me ya hana ki yi haƙurin a lokacin da kika ji ɓacin ran da ya janyo kika yi wannan rashin hankalin?, Yanzu in Banda ALLAH ya taƙaita wahala kinsan iya adadin rayuka nawa zaki saka cikin ƙunci?? Bayan waɗanda zaki yi sanadin barinsu duniya? Ko ko an faɗa maki cewa idan kin kashesu ke ƙyaleki za'a yi?, To buɗe kunnuwanki da kyau ki ji gidana zaki dawo da zama daga yau har zuwa lokacin da Mijin naki ya ga dama ya nemeki, tunda don kinga Yaya Mani ya sake maki da yawa ne shiyasa kike ganin dai dai kike da kowa, to har abada na gaba yana gaban kuma ba zai taɓa dawowa baya ba, don gashi cen yanzu kin baro mata gidan tana jin daɗinta da mijinta ke kuma ga ki nan kunci zai kasheki tare da Iyayenki, to Ni dai WALLAHI wannan karon bazan zuba mako ido kina yin abunda kika ga dama ba, dole ne a nuna maki cewa ƴa ce ke kuma haifarki aka yi akwai na gaba da ke har gobe"

Tana ƙare faɗar maganar ta koma ɗakin Daddyn inda ta taraddashi sai shar ƙwallah yake yi, da ban baki da lallami ta samu ta shawo kanshi da ƙyar ya yi shiru, cikin nadamar irin damar da ya baiwa Zee a farko yake ta baiwa yar uwarshi haƙuri akan abunda ya aika akan Aminu, don itama tana cikin mutanen da suka yi fushi da shi akan auren sai dai don ance hannunka baya ruɓewa ka yanke ka cire inji hausawa fa, don kam a wannan zamani da muke ciki sau nawa aka yanke hannun aka jefar? ALLAH dai yasa mu fi ƙarfin zuciyarmu.
Chapter 72 · 0% Book details