← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 84

Sashe 48

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar juma'a ranar ce ta kama ta ɗaurin aure kuma ayi walima, haka ranar ce kuma Malam Lawi ya diro garin tare da wani abokinsu da ke cen Gomben, saboda gayyatar da Safwan ɗin ya yi masu, cike da jin daɗin gani junansu kowa yake ta ɗokin ɗan'uwanshi, sai firar yaushe gamo ta ɓarke a tsakaninsu ihunsu kawai ke tashi a ƙofar gidan bayan sun dawo ɗaurin auren.

Kasancewar a harabar filin gidan ne za'a yi walima shiyasa aka kafa rumfuna manya manya aka ƙawataa wurin sosai.

Dije ta fito zata je cen wajen ne idonta ya kai kan malam Lawi, cikin sauri ta zaro ido cike da jin daɗin ganinshi ta nufi wajensu fuskarta a washe take faɗin

"Rai kan ga rai Malam? ashe ina da rabon sake ganinka a duniya?"

Lawi cike da mamaki ya bi ta da kallo tun daga sama har ƙasa saboda ganin yanda gaba ɗaya ta sauya kamannu kamar ba Dijen da ya sani ba, wadda ko a mafalki da siffarta ta ƙauye yake hangota, sai dai kasancewar yasan cewa da da yanzu ba ɗaya ba ne, saboda yanzu igiyoyin aure sun yi masa shamaki da ita, auren ma na Abokinshi Safwan, shiyasa ya wani basar ba tare da wani sakin jiki ba ya ce

"Amarya kinsha ƙamshi ya garin? da fatar kina lafiya?"

Dije ta washe baki cike da jin nauyinshi tace, "Malam saukar yaushe haka babu sanarwa?"

Lawi ya kalli Safwan ya ga yanda gaba ɗaya yanayinshi ya canza ya yi gajeren murmushi yace, "wannan kuma laifin angonki ne tunda shine bai sanar da ke ba"

Dije ta kai kallonta gareshi ta yi ɗan murmushin yaƙe sannan ta ce

"Bari in je in dawo Malam ai da nasan kana nan da tun ɗazu ka sha tarbata"

Lawi ya bita da kallo yana wani murmushi cen kuma me ya tuna ya yi saurin kawar da kanshi a gefe yana wassafa siffarta cikin bular doguwar rigar da ke jikinta, ta yi mata kyau ɗagwasgwas ta zauna a jikinta, ga ɗankwalin rigar da ta yafo gaban kanta gaba ɗaya a buɗe yake har ana hango kwantaccen gashin kanta da yasha gyara ya kwana, ga sajen gashin ma ya kwanta luf luf a gefe da gefen fuskarta, girarta ma cike tafi da gashi gazar gazar da ta ƙara Ƙawata mata fuskar, duk da bata yi wata doguwar kwalliya ba amman yanayin tsarin shigarta ta burgeta sosai.

Daga shi har Safwan sun faɗa tunanin da su kaɗai suka san me suke tunawa, tunaninsu ya katse ne lokacin da Dijen ta dawo tana murmushi tace

"Malam zo mu je falon baƙi ka ci abinci ko?"

Abokinsu da suka zo tare da Lawin ya kalli Dije cikin murmushi yace, "Au Wai abun ƴar wariya ce daman?"

Dije ta waigo tana dariya tace, "yi haƙuri idona ne suka rufe ruf WALLAHi a duk wurin bana hangen kowa sai malamina kawai"

Ba Safwan da maganar ta daka a ƙirji ba har shi kanshi Lawin ba shiri ya waigo, saboda maganarta ba ƙaramin dukan zuciyarshi ta yi ba.

To fa wata sabuwa 😝

Akafta😅

D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*My fans bakina ba zai iya misalta farin cikin da kuka sakani ba, naso in zayyano sunayenku to amman yawanku ya kai ba zan iya lissafoku duka ba, amman na gode 🙏🏻na gode🙏🏻 sosai Alkhairin ALLAH ya kai maku duk inda kuke💃🏻ku daɗe ku yi ƙarko mutanena👍🏻*

*Lamba ta 47*

A harzuƙe ya taso da nufin kai mata duka sai ga motarsu Zee ta kunno kai harabar gidan, cikin sauri ya nufi motar yana washe baki saboda jin daɗin ganinta, Dije ta kai kallonta gareta take wani ɓacin rai ya ziyartota, amman a hakan ta kalli Lawi ta yi wani murumushi tace

"Zo mu je Malam"

Lawi ya yi shiru sannan yace da abokin nasu mai suna Kamal yace, "zo mu je Abokina don wannan tafiyar dole ne a buƙaci rakiyarka"

Kamal kam sai kallon motarsu Zee yake yi mamaki fal ranshi yace da Lawi, "Abokina baka gane wannan yarinyar ba ne?"

Lawi ya kai kallonshi ga motar inda Safwan da Zee suke tsaye jikin motar suna fira kowanensu cikin farin cikin ganin ɗan'uwanshi, Lawi yace

"Kai ne idon gari Abokina ban gane su ba gaskiya"

Kamal ya ce, "budurwar Aminu ce fa wadda ya susuce kanta kullum yana dakon ta kammala karatun da take yi ayi auren amman Mahaifinta sai ja masa rai yake yi, ko kallon zumuncin da ke tsakaninsu ba ya yi, ya fifita son zuciyar ƴarshi akan na kowa"

Lawi yace, "Eh kam sai yanzu na tuna amman kasan ni daman bansan yarinyar ba ai labarinta kawai nake ji"

Dije tana tsaye tana saurarensu ba tare da ta ma nuna tasan wani abu da ke faruwa ba, cikin dariyar yaƙe tace

"Ai kam dai yanzu sai dai Aminu ya yi haƙuri saboda ita ce matar da Malam Safwan zai aura tare suke karatu a cen ƙasar wajen"

Daga Lawi har Kamal suka zaro ido cike da mamakin jin wannan zance a bakin Dije, haka kawai Lawi ya tsinci kanshi da cewa

"To ke har kin amince kenan?"

Dije ta yi shiru tana yar dariya mai cike da takaicin da ke cin zuciyarta tace, "ku zo mu je mu barshi ya ji daɗin firar don kada mu takurashi"

Suka wuce Safwan da hankalinshi gaba ɗaya yana kansu saboda tsabar kishin da ke cin zuciyarshi, ya bisu da kallo ranshi a matuƙar ɓace yace da Zee

"Zo mu shiga ciki ku gaisa da Hajiya"

Zee ta bishi da kallon mamakin me ke damunshi tace, "my man what's wrong with you?? Ko na yi maka wani abu ne?"

Safwan cike da ƙunar rai ya shafo kanshi ya ce

"No! no! kada kiji komi mu je kawai"

Yayi gaba Zee ta bishi da kallo ƙawarta ta riƙo hannunta suka shiga cikin gidan, suna shiga suka yi kiciɓis da Fiddo ya ce da ita ta kaisu wajen Hajiyar idan sun gaisa abasu muhalli a wajen walimar, sannan ya barosu ya nufi ɗakin baƙin da zuciyarshi take ta azalzalarsa akan ya je ya ga wace irin wainar ce ake toyawa, ai kuwa sai ko ya taradda Dijen ta gama zuzzuba masu abincin tana miƙawa Lawi lemun da ta zuba masa a cup, daga ita har shi murmushi ne kwance a kan fuskarsu, idonshi a rufe yana zuwa bai wata wata ba ya fella mata wani wahalallen mari har sai da ta saki cup ɗin saboda tsabar tsoronshi da kuma azabar da ta ziyarceta, cikin wani masifar ƙarfi ya fisgo hannunta suka fice Kamal da Lawi suka bisu da kallo, cikin tsananin ɓacin rai Lawi ya dafe kanshi zuciyarshi sai tafasa take yi saboda zafin marin da Safwan ya yiwa Dije ya ji shi har cikin ranshi.

Kamal ya kalli Lawi yace, "wai wannan guy ɗin mi ke damun ƙwaƙwalwarshi ne?, Ko da yake banga laifinshi ba fa don ko ni nan ina da irin wannan mata WALLAHi dole ne na yi kishinta, amman kuma yasan yana sonta zai tsirowa kanshi auren Zee da rana tsaka?"

Lawi ya yi shiru saboda ɓacin ran da yake ji yasa ya ma kasa furta wata kalma a bakinshi, sai shafa ɗan ƙaramin gemunshi da yake yi yana nazari.

Safwan kam bai zame ko'ina ba sai ɗakinshi da Dijen, yana shiga ya saka key tare da wurgar da ita a tsakiyar falon yana ƙare mata kallo yana nazarin ma wane hukunci zai yanke mata don ya ji sauƙin abunda ke azalzalar zuciyarshi, cikin takaici ya cakumo gashinta da ƙarfi ya miƙar da ita tsaye, cikin jin zafin da ke ratsa kanta tace

"Don Allah ka yi haƙuri WALLAHi bazan sake ba"

Safwan ya turata baya da ƙarfi ta yi taga taga zata faɗi kuma ya yi saurin riƙota cikin fushi yace

"Kasheni kike so ki yi ne ko kuwa?, Me na yi maki Kika zaɓi ki tozartani cikin mutane?, To WALLAHi tunda har ke baki san darajar aure ba zaki janyo in fiddaki Makarantar da kike kwaɗayi gaba ɗaya, don na fahimci duk wannan rawar kan naki don kin ga an baki damar yin karatun ne, to daga yanzu ba zaki sake zuwa wata makaranta ba da sunan karatu idan ba islamiya, ita ɗin ma anan gidan za'a zo a dinga koyar dake saboda kawai ki san muhimmancin auren da ke kanki"

Dije ta kalleshi ido cikin ido tace,. "Wane aure naji kana faɗa ne? Auren da kai da bakinka ka ce da ni kada in yarda cewa wani yasan kai ne mijina? To Ni yanzu WALLAHi na gaji da wannan wahalallen auren, tunda mai sona tsakani da ALLAH ya bayyana ka barni kawai in auri wanda ya soni tun kafin ka aureni, don ni shi Nike so........."

Wani marin da ya kaiwa bakinta ne yasa ta yi saurin dafe bakinta tana zubar ƙwallah tace, "ko zaka kasheni ba zan fasa faɗar cewa ina son Malam Lawi ba tunda har kai bakasan darajata ba, shi nake so kuma shi nake da gurin zaman aure da shi idan ba haka ba kuma WALLAHi zan koma garinmu gaba ɗaya na haƙura da makarantar bana so"

Ta ƙare faɗar maganar cikin kuka ta durƙushe tana gunjin i kukanta gwanin ban tausayi, cikin wani sabon tashin hankali ya yi durƙuso gabanta har ya so ya shafo kanta, me ya tuna kuma ya yi saurin miƙewa tsaye yace

"Da ace zai amince ya karɓekin da nafi kowa farin ciki, to amman yanzu haka ko da kuɗi aka bashi ke bazai taɓa karɓar ki ba, ko ni nan don Allah ya ƙaddaro da zaki zama matata da ke kinsan baki kai matsayin wadda zan iya rayuwar aure da ita ba, nasan ba abinda ke damun zuciyarki a yanzu face kishi ko? to ki kwantar da hankalinki da anyi aurenmu da Matata Zee zamu bar maki ƙasar gaba ɗaya sai ki ji daɗin karatun naki"

Dije ta miƙe tsaye hawaye shaɓe shaɓe akan fuskarta tace
Chapter 48 · 0% Book details