← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 84

Sashe 65

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai ƴan mintuna a tsakani ta kasa haƙuri ta dawo abun haushi har lokacin bai duba ba, cike da takaici ta kashe datar ta kwanta abunta tare da ƙarewa pic ɗinshi da ta ɗauka kallo, haka ta kwana cikin begen Mijinta tare da mafalkinshi kala kala.

*****

Malam Safwan kam sai da ya kammala uzurin da ke gabanshi zuciyarshi ta ƙawata masa duba sauran text's ɗin da ake turo masa da numbers mabanbanta, cikin nasara ya kawo kan na Dijen Baffah cike da mamaki ya bi massages ɗin da kallo

_Salam_

_😢_

_Salam_

Sai hoton da ta turo wanda idonshi a kan dukiyar fulaninta da suka cika ƙirjim fam kamar za su fasa rigar su fito, ba shiri ya haɗiyi wasu yawu da suka tsinke masa, sannan ya sake yin zooming ɗin pic ɗin haka kawai ya tsinci kanshi da faɗin

"I like it"

Amman a zuciyarshi ya ce _ita kuma wannan wacece take son janyo hankalina da abunda na fi so a jikin mace??._

Haka kawai ya ji ya kasa ɗauke kanshi daga pic ɗin sai ga shi da tsintar kanshi cikin wani yanayi marar misaltuwa, cikin wata kasala da ta sauko masa ya mayar mata da reply kamar haka

_wslm plss wace ce?_

Sannan ya kashe wayar yana ta ƙarewa pic ɗin kallo duk da wani sashe na zuciyarshi yana yi masa kashedi da kallon pic ɗin, kuma ta shawarceshi akan ya goge hoton sai dai kuma ya kasa baiwa zuciyarshi haɗin kai, saboda ba ƙaramin kyau suka yi masa a ido ba.

Dije kam ko da safiya ta waye tana gama SALLAHr asuba ta janyo waya ta duba cike da zumuɗi tare da fatar ya ga massages ɗinta, ai kuwa sai ga shi ta ga ya duba har da su reply, cikin rawar jiki ta mayar masa da amsa kamar haka

_"Am the one how was the day??"_

Sannan ta sake ɗauko wani pic ɗin wanda daga ita sai rigar bacci mai siririn hannun vest, ga shi ko bra babu a jikinta sun fito sosai masha ALLAH ta yi crop ɗinshi ta cire fuskarta, sannan a ƙasan photon ta rubuta

_Good morning my life partner._

Sannan ta sauka ta nufi kitchen ita da su Husnah da wasu ma'aikatan gidan biyu suna shirya abun break fast, Bayan sun ƙare ne ta dawo ɗakinta da nufin yin wanka, amman zuciyarta ta ƙawata mata ta duba ta ga in ya ga saƙonta, sai dai ganin bai hau online ɗin ba yasa ta yi saurin shigewa toilet domin ta yi shirin zuwa school.

Dije har ta je makarantar ta dawo tunaninta yana kan wayarta, saboda son ganin wane saƙo ne ya turo mata, aikuwa cike da ɗoki ta duba wayar sai ga reply ta gani kamar haka

_"Idan ba zaki buɗe fuskarki ba kada ki sake yi man magana"_

Cikin daburcewa Dijen ta yi shiru tana nazari sannan ta yanke wata shawara ta sake ciro wani photon wanda ta yi daga ita sai wata doguwar riga half gown ta kanti da wani wando skin tight baƙi, inda ta juya gefen fuskarta kawai ya fito don gaba ɗaya ma bayanta kawai aka ɗauka sai gefen fuskarta ga gashinta ya zubo har gadon bayanta, sannan a ƙasanshi ta rubuta

"Good bye"

Aka yi da ce shima yana online saboda ya kasa natsuwa zuciyarshi sai hasko masa fuskar Dije take yi a matsayin mamallakiyar photon, shiyasa ya ce idan ba za'a turo fuska ba kada a sake yi masa magana saboda kawai ko wacece ta bayyana kanta, sai ko ga shi wannan photon da ta sake turo masa na ƙarshe ya tabbatar masa da lalle Khadijarshi ce, saboda ko a mafalki ya ga gefen fuskarta sai gano ita ce bale a ido biyu, sai dai kuma kokwanton da ya ke yi akan anya zata iya aikata hakan gareshi,sai ga shi da tsintar kanshi cikin wani tsantsar farin ciki marar misaltuwa, cike da zumuɗi ya yi saurin mayar da reply da cewa

_"wow! wonderful babe! plss Ina buƙatar wasu pic's ɗin amman masu ɗauke da kyakkyawar fuskar da ke jikin wannan tsadadden body"_

Cike da jin daɗin yabon da ta ji ya yi mata ta yi saurin rufe furkarta Kamar a gabanshi, kasancewar itama a matse take da son Mijinta na ta cikin sauri ta mayar masa da reply ɗin cewa

_"Thanks my angel"_

Safwan ya bi text ɗin da kallo zuciyarshi cike da tsanani ƙaunar Dijenshi, duk da bai tabbatar da ita ɗin ce ba amma jikinshi ya ba shi ita ɗin ce shiyasa ya sake cewa da ita

_"More pictures plss"_

Ta mayar masa da reply ɗin

_" No bye"_

Ya yi saurin rubuta _" wait! wait! plss my precious what's your name?"_

Dije zata mayar masa da amsa kenan ta ji muryar Aunty Ummin zata shigo ɗakin, cikin sauri ta ajiye wayar ta faɗa toilet, ko da ta zo taga bata ɗakin ta ce

"Ki fito ki ci abinci Ni bana son yi wa kai horon yunwa"

Daga cen toilet ta yi gyaran murya alamun ta ji ta sannan Aunty Ummin ta fice ɗakin, cikin sauri Dijen ta tuɓe Uniform ɗinta daga cen toilet ɗin ta yi wanka a gurguje ta fito, sai ga kira ya shigo wayarta tana duba sunan mai kiran ta ji ƙirjinta ya buga dam! Amman ta yi jarumtar ɗauka sannan ta ajiye wayar akan gadon ba tare da sanin cewa Video call ne Safwan ya kirata ba, ta ƙurawa wayar kallo ta kasa ɗauka bale ta saka a kunnenta sai ganin fuskarshi ta yi cikin screen ɗin wayar ta yi saurin zaro ido waje tare da dafe ƙirji, inda shi ma ɗin ita yake kallo cikin mamakin yanda ta koma saboda daga ita sai guntun towel iya cinya, ga abubuwan da yake so cike fal a ƙirjinta ba shiri ya tsinci kanshi cikin wata kasala tare da faɗin

"Khadijah me yasa kika tafi kika barni? Me na yi maki da ......."

Fisge wayar da aka yi a hannunshi ne yasa maganar da yake yi ta katse, saboda ZEE cike tsantsar kishin kiran sunan Dijen da ta ji ya ambata yasa ta ƙaraso wurinshi ba tare da ya kula da ita ba, hango yanayin da Dijen ta ke ne duk da bata ga fuskarta da kyau ba yasa ta ji wani bala'in kishi ya rufeta, wanda ya janyo ta fisge wayar da ƙarfi tare da dokata ga ƙasa ta tarwatse, ya bita da kallon takaici ranshi a matuƙar ɓace ya ɗaga hannu ya watsa mata wani wahalallen mari har sau biyu, sannan ya zare belt ɗin jikinshi ya yi ta mazgarta tana ihun neman taimako babu mai cetonta, sai da ta lallasu da kyau sannan ya saurara mata cikin fushi ya ce

"Akan wannan rashin hankalin naki WALLAhi zaki janyowa kanki wahala a hannuna, ko an ce maki ina cikin mazajen da mata suke juyawa ne?, Ke har kin isa ina tare da matata ki hanani yin abunda nake so?, To bari ki ji akan wannan haukar ta ki zaki janyo wa kanki komawa Nigeria WALLAhi, saboda ina da ikon da zan datse karatun naki gaba ɗaya idan kuma akwai wanda ya isa ya ce sai kin ƙarasa to sai ya dawo da ke in gani"

Yana ƙare maganar ya wuce fuuu ya fice ya barta tana ta kuka tare da mamakin wai ita ce yau Man ɗinta ya daka akan matsiyaciyar Matarshi.

To fa su Zee an Fara sanin wanene Safwanu😊

Akafta😝

D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Ina alfakhari da ku my fans saboda ku ne ƙashin goyon bayan duk wata ɗaukaka da zan samu, ina yinku all a ko'ina kuke kuma a duk inda kuka kasance, tsakanina da ku sai son so fisabilillah😅*

*Lamba ta 61*

Sai da ta ci kukanta ta ƙoshi sannan ta baiwa kanta haƙuri dolenta, don bai dawo gidan ba har sai da ya tabbatar da ta yi bacci sannan ya shigo, saboda baya son haɗa ido da ita akan nauyin dukan da ta janyo ya yi mata, duk da wani sashe na zuciyarshi yana ba shi cewa ko kaɗan bai yi laifi, don yanda ya ƙagu da yasan inda Khadijarshi take komi zai iya aikatawa akan wanda ya ke so ya toshe masa ƙofofin da da zasu sadashi da farin cikinshi.

Sannu a hankali ya ƙaraso wajen wayarshi da ke tarwatse har lokacin, ya duƙa ya ɗauki kangalwar wayar ya zare sim cards ɗinshi sannan ya saka cikin wata sabuwar wayar da ya siyo, sai dai baƙin cikin rashin saving ɗin numbar Dijen da bai yi ba tun farko yasa ya dannawa Hajiyarshi kira, bayan sun gaisa ya marairece murya ya ce

"Haba Hajiyarmu plss don ALLAH ki sanar da ni inda aka kai Khadija, saboda jikina yana bani cewa ba aikatau Khadija ta je ba, don ALLAH ki tausaya man Hajiyarmu ki bani matata WALLAhi ina sonta sosai"

Hajiya Mama ta yi shiru sannan ta ce

"Ka kwantar da hankalinka duk lokacin da ka dawo ƙasar nan insha ALLAHu zaka taradda kHadija a gidanka zaune tana jiran dawowarka"

Cike da tsananin jin daɗi ya ce "in dai haka ne to ni ai sai in tattaro kayana kawai in dawo gida Hajiyarmu"

Ta ɓata fuska kamar tana ganinshi ta ce "shi karatun na ka idan ka dawo wa zai ƙarasa maka shi ne?bayan saura lokaci kaɗan ka kammala"

Safwan ya sosa kanshi yana murmushin jin daɗi ya ce "to Hajiyarmu me zai hana ayi mata viza kawai ta samemu anan ɗin ta tayamu zaman, kin ga in mun kammala sai mu dawo gida tare gaba ɗayanmu?"

Hajiyar ta yi ƴar dariya sannan ta ce "ita kuma karatun nata fa? Sai ta ajiye ta zo ta tayaku naku karatun kenan? to bari ka ji idan ka kawo wasa ko ka dawo bazan bari ka ganta ba, matuƙar baka natsu ka ƙare karatunka da ya rage saura ɗan lokaci ba"

Safwan ya durƙusa ƙasa kamar a gabanta ya ce "plss Hajiyarmu don ALLAH ko numbar da zan sameta ne a bani plss sai mu dinga gaisawa, don wallahi rashin jinta zai iya janyo inyi asarar duka shekarun da na ɓata a baya wajen karatun"
Chapter 65 · 0% Book details