Sashe 63
Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wacece khadijar da na ji kana ta kira a jiya? Don Allah ka sanar da ni saboda ina jin tsoron ace sunan Uwargidanka ne ka ke ta ambata"
Safwan ya yi saurin kawar da kanshi gefe tare da jin nauyin abunda ya aikata mata cikin rashin sani, sannan ya ce
"Ki yafeni Matata nasan ban kyauta ba amman Insha ALLAHu hakan ba zata sake faruwa ba in dai har daga gareni ne matsalar ta fito "
ZEE ta share hawayenta da suke ta sauka akan fuskarta ta ce
"Ina jin tsoron ace akwai wadda ta fini samun muhalli a cikin zuciyarka, don WALLAhi matuƙar hakan ta faru to bazan taɓa yafe wa kaina ba"
Safwan ya rungumota jikinshi tare da ɗora kanshi saman kanta yana wassafo Dijen Baffah a ranshi da ruhinshi sannan ya sauke ajiyar zuciya yace
"So shu'umi ne my unique ki yafewa Man ɗinki albarkacin son da kike yi masa kin ji?"
Ta riƙo hannunshi sannan ta shafo fuskarshi ido cikin ido ta ce
"Ina sonka sosai My Man don ALLAH ka riƙeni amana ka ji?"
Ya lumshe idanuwanshi ya sake rufewa sai ga fuskar Dijen Baffah ta zo masa a cikin gilashin idonshi, cikin sauri ya yi saurin buɗe idanuwan yana kallonta fuskarta ƙur sai ga fuskar Dijen Baffah ta bayyana cikin ta ta, ya yi saurin duƙowa cike da zalama ya cafki leɓenta yana wata irin tsotsa tamkar zai rabata da bakin duka, cikin fitar hayyaci tare da rasa tunaninshi na wuccin gadi ya ɗago fuskarta idonshi a rufe ya ce
"Me yasa kika bari aka rabani da ke ne? Me yasa kika tafi kika barni? Kinsan iya adadin damuwar da kika sanyani kuwa? Plss ki dawo gareni khadija, plss ki dawo wurina na ce!!!!"
Ya ƙare maganar cikin zubowar wasu hawaye masu zafi waɗanda tunda ya shiga cikin damuwar bai sami damar yin ƙwallah ko ɗaya ba bayan kukan da ya yi wa Hajiya sai wannan, shiyasa hawayen suka kasa tsayawa sai sauka suke yi a fuskar Zee, saboda ta kasa ɗauke idanuwanta akanshi sabida mamakin da ya game jikinta da zuciyarta.
Zee cikin wani fushi mai cike da zallar tsagwaron kishinshi ta yunƙura cikin zafin nama ta yi saurin tureshi ta miƙe tsaye, idonta akanshi hawaye suna zuba masu zafi ta nunashi da hannu ta ce
"Ka yi gaggawar sanar da ni wacece khadija tun kafin ka janyo zuciyata ta buga"
To fa🙀Ke ko amarya kar ki yi fatar bugawar zuciya a ranar farko gidan aurenki😢
Akafta😝
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*special thanks to you all my FANS😉*
*Lamba 59*
Cikin sanyin jiki ya miƙe tare da janyo ƙafafuwanshi zuwa inda take sannan ya yi ƙarfin halin riƙo hannunta, cikin fushi ta ƙwace hannun tare da matsawa baya tana yi masa wani kallon mai cike da fushi tace
"Wacece wannan baƙar yarinyar da kake ambata a gabana?? Don na ce ina sonka laifi na yi da har kake ƙoƙarin baƙanta man cikin lokutana da Allah ya bani daga gareka??, Sakayyar da zaka yi man.. ke....nan?"
Ta ƙare maganar cikin sarƙewar murya tare da zuwan wani masifaffen kuka, cikin tsananin damuwa Safwan ya isa wurinta ya rungumota jikinshi, ba shiri ta faɗa ta narke masa tana wani irin kuka gwanin ban tausayi, cikin dakusasshiyar muryarshi da ta sha kuka ya shafo gashinta ya ce
"Don ALLAH ki yi haƙuri kinji? Insha ALLAHu hakan ba zata sake faruwa ba"
Zee ta share hawayenta sannan ta ɗago tana kallonshi tace
"Matuƙar kana son mu yi zama na jin daɗi da farantawa juna ni da kai, to ya zama dole ka nisanci duk wani abunda zai janyo muna matsala, saboda akanka wallahil'azim zan iya aikata koma menene saboda haka ka kiyayi faɗin sunan kowace shegiya a gabana, that's the first and last idan har kana son farin ciki a gidanka"
Safwan ya yi shiru yana nazarin rashin dacewar abunda ya aikata, amman duk da haka wani sashe na zuciyarshi cike yake da jin zafin baƙar da ta kira Khadijarshi, sai dai saboda sanin shine mai laifin yasa ya zare jikinshi daga nata ya nufi kan gadon ya kwanta, tare da dafe kanshi yana nazarin mafita akan matsalolin da suke son ruftowa rayuwarshi.
Cikin damuwa Zee ta bishi da kallo sannan ta ƙaraso ta zauna gefen gadon tare da riƙo hannunshi ta ce
"Baka sanar da ni matsayin wannan suna da naji kake ta ambata ba tun jiya har yau, wacece ita? Saboda jikina yana bani cewa tabbas itace silar shigarka cikin wannan sabon yanayin da ka ke ciki"
Safwan ya janyo hannunta saman ƙirjinshi sannan ya ce, "ki yi haƙuri khadija matata ce asali ma itace matar da kika ji an ce da ke ina da, kuma ita ce Uwargidana a yanzu haka, amman duk da haka nan ina baki haƙuri akan laifin da na aikata kuma insha ALLAHu bazan sake ba"
A hankali ta zare hannunta cikin na shi saboda wani kuka da ya zo mata, sannan ta miƙe cikin jarumta ta ce "bari in je wajen su Ruma kada su ga na barsu"
Ƙanzil bai ce da ita ba har ta fice zuciyarta cike da tsantsar baƙin ciki, tafiya take yi idonta a rufe saboda zallar tsagwaron kishin Dijen da ya rufe mata idanuwa, har ta isa sashenta bata san ma ta kai ba har sai da ta jiyo shewarsu Ruma sannan ta yi saurin share hawayenta tare da saita kanta ta shiga tana wasar baki, aiko suka yo mata caa da tsokana ko wa da abinda ya ke faɗa akanta, da kyar ta sulle ta faɗa toilet inda ta ɗauki lokaci tana ta kukanta sannan ta baiwa kanta haƙuri ta yi wankan ta fito.
Da taimakon ƙawayenta ta fesa wata arniyar kwalliya ta ci wani danƙareren less black colour tare da ɗigon pinck a jikinshi, an mata ɗinkin half bubu ta ji aiki sosai a gaban rigar, sannan ga ɗaurin ɗankwalin da suka yi mata irin na wayayyun ƴanmata, sai gata da fitowa sharri! Masha ALLAH sai pics ake yi mata tana jin kanta wata shegiya, sannan su ka ta yi tare da ƙawayenta suna iya shegensu, duk da ita kam ƙarfin hali ne kawai ta ke yi tana wayancewa cikinsu ana ta sharholiya.
Bayan sun yi break ne Safwan ya zo suka gaggaisa tare da yi masu godiya akan ɗawainiyar da suka yi, sai dai da yawa wasu daga cikin ƙawayen nata sun ƙyasa sosai akanshi, wasu ma har kwatantawa suke yi ina ma ace sune suka sameshi, wasu kuma suka ga gaskiyar Zee da ta nace sai shi duk cewa shi kanshi Aminun ba abun kushewa bane, amman ko kaɗan ba za'a haɗashi da Man ɗin Zee ba, saboda Safwan ƙosasshshen ingarman namiji ne cikakke mai cikar haiba ta ko'ina, saɓanin Aminu da yake siriri sosai sai dai daga ganinshi zaka gano cewa shima jarumin gaske ne.
Bayan fitarshi ne Zee ta samu keɓewa da wasu amintattun ƙawayenta biyu Ruma da wata Sadiya, inda ta sanar da su irin abunda Safwan ɗin ya yi mata, Ruma ta yi shiru sannan ta ce
"Ke fa mace ce don haka ki bi shi da taki kalar salon kissa don ki samo kan Mijinki, saboda irin wannan renin hankalin WALLAHI ba kowa ce mace ce zata iya jura ba gaskiya, don ance yana son Matarshi ai ba sai ya nuna maki ba tunda dai ke ma ɗin yanzu Matarshi ce, don ko an ƙi ko an so ke da ita duk matsayinku ɗaya a wurinshi, to cin zarafin kiran sunanta a gabanki na minene?"
Sadiya ta yi saurin faɗin
"Wa ya ce matsayinsu ɗaya? Don Allah ki daina ragewa Zee martaba Rumasa'u, ai ko makaho ya shafa Zee ya shafa waccen matsiyaciyar Uwargidan tashi duk da bamu santa ba WALLAhi kinsan Zee ta fita nesa ba kusa ba"
Ta dafa kafaɗar Zee da ta yi tagumi tana saurarensu ta ce, "ke mrs Man buɗa kunnuwanki da kyau ki ji Ni, WALLAhi ki zage damtse ki fatattaketa da kyau a zuciyarshi don ke ma ki sami matsugunnin da ya fi na kowa a wurinshi, in ba haka ba WALLAhi kina ji kina gani zata ƙwace maki mijin ta barki da cizon yatsa, kallarki da kyau mace har mace son kowa ƙin wanda bai samu ba, don haka ta ƙarfin tsiya ke ma ki mamaye ko'ina na zuciyarshi, ke in da hali ma kada ki bari ko kaɗan ta raɓeshi ki kama abunki ki riƙe gam gam tunda dai ba wani abu aka fiki da shi ba, kyau kuɗi iya soyayya da hali mai kyau kowane ALLAH ya baki ai, saboda haka ya rage naki ki ƙwaci Mijinki tun kafin kwaɗo ya yi maki ƙafa kina ji kina gani, don WANNAan tsadadden mijin naki ko wace mace a duniya tana son irinshi idan zata samu"
Ruma ta yi ƙarfin halin cewa "Haƙiƙa kam tun kafin ki aureshi ƙanwarshi da kanta ta sanar da ni yana bala'in son Matarshi, saboda haka Ni ina ganin tunda har karatu aka ce tana yi me zai hana ku tattara ku bar ƙasar ku koma school abunku ke da shi, kin ga daga cen sai ki cusa masa kanki ta yanda ko sunan wata mace ma ba zai so a faɗa ba bayan ke, kin ga duk lokacin da ku ka dawo ba wani power da ita waccen matar tashi zata fi ki a wajenshi, saboda kin riga da kin mallake komi dole ta yi haƙuri don kin fita a wurinshi, tsorona ɗaya ne kada ace itama sai ta biku kun je tare, don a gaskiya idan aka yi maki hakan za'a wargaza komi"
ZEE ta yi saurin faɗin
"Ba ma za'a je da ita ba WALLAhi, haka kawai in dai ba salon mugunta ba ai tun cen tare aka ganmu ita kuma tana nan, To yanzu kuma akan me za'a ce ta bimu? lalle ma ai WALLAHI da taga rashin mutuncina kuwa don sai nasa ta dawo gidan ubanta ba shiri, saboda sai na nuna mata cewa ita ƙaryar asirin farauto zuciyar miji take yi, da salon Soyayyata zan sakashi ya manta uwar da ta haifeshi ma ballantana ita ƙaramar ƴar iska"
Ta ƙare maganar cikin huci, Sadiya ta dafa kafaɗarta ta ce