← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 84

Sashe 29

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya yi saurin dafe kanshi yace,. "ta zama 'yar aikinki kawai Hajiya don gaskiya Ni ba Zan iya zaman aure da wannan tatsitsiyar yarinyar ba, musamman ma dai a yanda take d'in nan Tiphical Yar k'auyen nan?, Kai ina bazan iya ba gaskiya ai sai ta janyo ayi man dariya, ALLAH na tuba Hajiya me zan tsinta a jikinta Ni Kam!? astagfirullah ALLAH ya rabani da kayan takaici WALLAHI"

Not edited😕

Ayi manage plss 😍😍

Akafta🤣

D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Wannan page kyauta ce gareki sukutum Kanwata ta hannun damata, wadda nije jinki har cikin b'argona, ke ta daban ce a wajena HANNAH MAHMUD SUHANA ina yinki har abadan abade😍*

*Lamba ta 30*

Yana k'are fad'ar maganar ya mik'e tsaye zai fita har ya kai bakin k'ofa zai fita, Hajiya Mama ta kira sunanshi cikin wata muryar da shi kanshi sai da ya ji kiran ya fad'ar masa da gaba, cikin sanyin jiki ya dawo ya zauna tare da b'ata fuska tamkar wanda aka daka yace

"Nasan tambayar da kike son ki yi man Hajiya Mama plss ki yi hak'uri WALLAHI ni ma bansan me ya ja ni na kasa barinta ta auri D'ankauye irinta ba, ni dai abunda kawai na sani taimakonta na yi niyyar yi saboda naga tana son karatu sosai,kuma matuk'ar ta yi aure wannan bak'in k'auyen na su to gurinta ba zai tab'a cika ba, kinji abunda ya sa na aureta Hajiya Mama don nasan Mahaifinta ba zai bani ita haka kawai ba in zo da ita"

HAJIYA Mama tun daga kallon da ya ga tana yi masa ya gano cewa maganarshi bata yi tasiri a wajenta ba, shiyasa ya yi shiru dolenshi zuciyarshi cike da takaicin me ma yasa bai barta ta yi aurenta ba?.

Hajiya Mama ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya sannan tace,. "Baka sonta ka hana Abokinka Lawi ya aureta??? Bayan kasan cewa shi ma ai taimakonta yake son ya yi akan buk'atarta me ya hana ka taimakeshi ya sameta????"

Safwan ya sosa kanshi yace "ai baya garin ne shiyasa da ni ba abunda zai sakani wannan aikin, saboda haka ki barta a nan kawai ta shiga cikin ma'aikatan, su ci gaba da aikinsu kud'inta na wata idan an tara zan dinga aikawa iyayenta"

Hajiya Mama ranta a b'ace tace,. "Safwan ka fita idona in rufe yarinya dai ko kana so ko baka so yanzu ta zama matarka, kuma ko kai baka isa ka kunce shi ba matuk'ar ina raye, kai ko bayan raina ban amince da ka saki yarinyar cen ba matuk'ar ba wani k'wak'k'waran dalili ba"

Safwan ya yi saurin fad'in "haba Mama WALLAHI ni bana son zama da ita da sunan aure ki bari kawai a taimaketa ta yi karatun shikenan kin ga zamu sami ladar, amman a ajiye zancen auren kawai Hajiya Mama yafi gaskiya, don ni Makaranta ma zan koma in k'aro karatu har zuwa lokacin da zan sami wadda nike so in aura"

Ranta ya kai iya k'ololuwar b'aci tace,. "Tashi daga gabana Safwan bana son in sake jin wata magana daga bakinka, ka je kawai akwai ranar da gaskiya zata yi halinta, amman ina son ka fara cukucukun nema mata Makarantar saboda ka samu ka cika alk'awalin da ka d'auka tun wuri"

Safwan ya marairece yace,. "Don Allah Hajiya Mama kiyi hak'uri naga kamar ranki ya b'aci WALLAHI bana son ganin fushinki ke ma kin sani, kada ki bari wannan 'yark'auyen ta shiga tsakanina da ke don ALLAH"

Ta yunk'ura ta mik'e fuskarta a sake tace,. "Ka je ka ji da bak'in in sun kammala in zo mu gaisa amman ina son kafin su tafi ka kai Mahaifinta Gidanka ya ga muhallin 'yarshi"

Safwan ganin yanda yanayinta yake ya sa bai musa ba ya mike ya fice, zuciyarshi cike da tunanin yanda zai yi ya kunce auren cikin ruwan sanyi ba tare da ya b'ata ran Hajiya Mama ba.

Dije kam tana cen Surry tanata shiryata cikin tsanaki duk da taso ta zuba d'ige d'igen kwalliyarta da ta saba amman Surryn ta hanata, sai ko ga Dije ta fito Masha ALLAH da ita saboda daman cen ita mai kyau ce duk da ta kasance bak'ar Mace, amman bak'inta mai kyau ne don bai b'oyewa kyawunta fitowa ba, Dije sai wasar baki take yi tana kallon kanta cikin madubi ta makawa Fiddo harara tace da Surry

"Ashe haka nike da kyau ni ma ban sani ba? Ji rigar nan WALLAHI ta yi man kyau sosai amman ta Makkah ce ko?"

Surry tana 'yar dariya tace, "a'ah a nan garin aka siyeta ba ma ita kad'ai ba ce da wasu ma suna d'akin Hajiya Mama kuma donki kawai aka siyo su, ki yi ta sakawa ke ma ki zama 'yar gayu irin Fiddo"

Dije ta waiga ta kalli Fiddon da ke ta dariyarta tace,

"A'ah bana son in zama irinta irinki na ke son zama har da farinki ma don ALLAH ki sani a injinin da ake maku wanka da shi ni ma ya wankeni tas! in zama fara irinku in na koma garinmu su Ladiyo su kasa gane ni"

Fiddo me zata yi ba fashewa da wata arniyar dariya ba tace,

"to ai ke bak'in da shi aka haifeki mu ko farare ne na asali ta ya zaki had'a kanki da mu? Cab! Ki dai ciji bulo 'yanci tara sai kuma idan har farin shago kike so sai a siyo maki mayukan bleaching da allurori ki yi fess har ma ki fi mu farin tunda ke bak'ar gasar tsiya ce da ke, daga ganin Sarkin fawa sai miya ta yi zak'i to WALLAHI ki sake tunani don mu in banda k'addara ma mi yaya Safwan zai had'ashi da ke har ya kwasoki ya kawo muna cikin gida??"

Dije ta mik'e tsaye tace,. "Kan uban nan amman ina ganin baki san Dijen Baffah ba ne d'iyar Inna Hasiya kanwar Usmanu Mijin Hansai? Cabd'i jam ai billahillazi kada ki bari mu gauraya ni da ke, kin ganni yar tsiton nan ko ta tsaf zan had'a maki jini da majina in sauya maki kamannu cikin k'ank'anin lokaci, don ki gano cewa wacece asalin Dijen Baffah?ke garinmu kaf tsorona ake ji daga abokanaina har yaran garinmu duka, don haka ki daina shiga sabgata idan har kina son ki tsira a wajena"

Fiddo ta taso ta zo gabanta ta tsaya Surry ta yi saurin fad'in,. "WALLAHI kika tab'a 'yar Mutane ba ruwana sai na fad'awa Yaya Safwan"

Dije ta yi mata wani kallon tace,. "Ke wai a nufinki dukana zaki yi? Cabd'i jam to WALLAHI kar ma ki soma tun wuri na baki shawarar gari, idan kuma kinki ji ai ko ba zaki k'i gani ba don ko shi yayan naku yasan halina ku tambayeshi zai gaya maku don bai sha ta dad'i wajena ba shi ma."

Fiddo ta turata baya tace,. "Wai ke me kike tak'ama da shi ne bak'auyiyar banza d'iyar talakawa me kuke da shi a gidanku halan da Yaya Safwan zai k'yaleki ki rena masa wayo bai jibgeki ba??"

Dije ta kalli Surry tace

"Kin dai gani ko? kuma ke ce sheda ko? To duk abunda na yi mata WALLAHI kar ma ace za'a ga laifina, don ko yanzu sai da Baffahna ya yi man wa'azi yace kada in ce zan rama abu in yi hak'uri amman duk da hakan ta koma ba fa zan k'yaleta ba WALLAHI"

Fiddo ta fad'a gado tana cin uban dariya saboda ganin take yi Dijen ba wata ba ce a duka d'aya zata bugeta saboda ganin yanda take 'yar firit gata siririya ba wani kumarin kirki, Surry kam janyo hannunta ta yi suka fito zuwa diny suna karyawa abunsu tana cin dariyar Dije idan ta yi wani abun.

A gefen bak'i matan kuwa Hajiya Mama ta je sunyi Ina kwana sannan suka yi mata godiyar dawainiyar da aka yi da su, ta kawo alkhairi mai yawa ta Basu ta bangaren atamfofi da kud'i, sannan ta nufi inda su Baffah'n suma ta gaisa da su suma ta yi masu alkhairi sosai, Baffahn ya d'auko dunk'ulallin kud'i da zasu Kai dubu d'ari biyu ya mik'awa Hajiyar ya ce a yiwa Dije kayan d'aki da su, saboda ganinta da ya yi mace Mai nagarta da kamalar mutanen kirki a fuskarta.

Hajiya Mama tace ya barsu kawai ya je da su ya kara a kasuwarshi ita zata d'auki nauyin komi, Baffah ya dage shi kam ba zai koma da su ba a matsayinshi na Mahaifinta dole ne ya sauke nauyinta da ALLAH ya d'ora masa nata, sannan Hajiya Mama ta karb'i kud'in ta fito da nufin ta kira Dijen su yi sallama da Mahaifinta.

Aiko ba k'aramin dad'i Baffah ya ji ba da ya ganta ta sha wankanta masha ALLAH a lokaci d'aya ta fara canzawa, cikin jin dad'i ya dinga murmushi yana cewa

"Anya Dijengalata nan gaba ko zan ganeki kuwa? Wannan gayu haka ai sai in za ci canza man Dijen tawa aka yi"

Dije ta rufe fuskarta tana dariya tace,. "Ai Baffah ni ma naji dad'in zuwa gidan nan WALLAHI baka ga yanda Matar gidan take sona ba, sai dai kanwar Malaminmu fa WALLAHI Baffah ta cikani dukan tsiya zan mata sai dai a maidani garinmu"

Baffah ya zaro ido yace,. "Kar ki soma Dije Kar inji kar in gani ki barta ta ci albarkacin Hajiyar tunda kince tana sonki ko?"

Dijen ta d'aga kai tace, "Kuma ma ta ce zata sakani Makaranta fa"

Ya ce "to kin gani don ALLAH kar ki tab'a kowa gidan nan kinji ko Dijeta?, In har kina son in na tafi in siyo maki wata sabuwar akuya ki had'a biyu"

Dije ta washe baki ta ce "ina so Baffah ka siyo man ba zan biyeta ba ka ji?"

Haka suka dinga firarsu yanata d'orata akan hanya a fakaice har su Baba Ali su ka zo da tashar motar da aka d'auko masu har gida, sannan suka yi sallama cikin mutunta juna kowa yana ganin girman d'an uwanshi,

Dije kam da k'yar aka rabata da Baffah'nta saboda Uban kukan da take ci tana fad'in ta fasa karatun ita gida zata koma, don shi ma kanshi Baffahn sai da yayi guntayen hawayen rabuwa da Dijenshi.
Chapter 29 · 0% Book details