← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 84

Sashe 2

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Malam Buba ka fito da ita tun kafin mu shigo da kanmu mu janyota don kuwa Maigarin ne da kanshi yake nemanka tare da tijararriyar d'iyar taku"

Malam Buba ya fara had'a hannu waje d'aya yana fad'in,. "Don girman Allah ayi hak'uri da halin Dije yanzu haka Ni har yanzu ma ban ganta ba don ko Gida bata dawo ba"

Wani katoton bafaden Maigari ranshi a b'ace yace,. "Zaka fito da ita taje ta karb'i hukunci Koko sai mun shiga da kanmu mun fito da ita?"

Malam Buba ya marairece yace, "Ku yi hakuri don ALLAH duk da dai ni har yanzu ma bansan laifin da ta yi maku ba"

Bafaden ya zabura Kamar ya daki Baffah yace, "Yanzu duk guje gujen zuwan Kura da ake yi a garin nan kana nufin baka sani ba? To Bari kaji yanzu haka Uwardakin Maigari ta karye Kuma duk a sanadin yarka Dije, don haka Maigari ya bada umurnin a d'auko masa ita ko a raye ko a mace domin a ladaftar da ita"

Yana k'are maganar Baffah ya zaro Ido yace, "Don girman ALLAH kuyi hakuri amman Dije bata dawo gidan nan ba, idan kuma baku amince da maganata ba ku shiga na baku dama ku fito da ita"

Aiko kafin ma ya karasa maganar suka tureshi suka fad'a Gidan, Kai tsaye suka dinga neman Dije lungu da sak'o na gidan ganin d'akin Inna a rufe yasa suka zaci tana ciki, Aiko k'aton bafaden ya saka k'afa ya buge kyauren Inna da ke rakub'e tana salati don ta zaci ko Kurar ce ta shigo Gidan mutane suka biyota ana neman hanyar kamata, jin an bugo k'ofar yasa Inna rafka salati tace

"Wayyo Uwata wayyo Ubana zan biku ba tare da guzurina ba, wayyo ALLAHna ka taimakeni Kura zata yi man tsiya"

Inna ta make cen karkashin gadon bononta inda ta b'oye sai ihu take kwarmawa, jin motsin shigowar mutum yasa ta k'ara sautinta tana fad'in

"Yihhuuu Jama'a ku yo agaji tun kafin ta k'araso ta Kai mani wawa"

Baffah ya duk'o da kanshi ta karkashin Gadon inda yake jin sautinta, Inna tana had'a ido da kanshi ta zaci Kan kurar ne ta saka k'afa ta halbo wata fanteka dake ke karkashin gadon sai a fuskar Baffah, a zabure ya d'ago ranshi a b'ace yace

"Ke Mahaukaciya fito haka nan ba wata kura yarki ce ta janyo masifar don haka ga Maigari nan ya aiko a kamota"

INNA cikin wani sabon firgici tace

"Da gaske???"

A kufule Baffah yace,

"Karyar da na saba yi maki ce yau na k'ara kwatawa"

INNA cikin rawar jiki ta lallaba tana ture kwanukan da ta shige cikinsu ta samu ta fito, da kyar ganin Baffan baya d'akin yasa ta fito tsakar gidan, aiko sai gata da yin arba da mutane cike da gidan nasu Mata da Maza, cike da tsananin rudu tace

"Na shigesu jama'a Lafiya?"

Wata Yar tsohuwa tace,. "Ina fa Lafiya Dije ta janyo anyita jin raunuka a gari duk a sanadin rashin mutuncinta, ki je ki fito da ita tun kafin Maigari ya sa a d'auki hukunci akanku, daman ance d'ankuka Mai jawa Uwarshi jifa, to yau dai ta sake janyo maku abunda yafi na kullum"

Baffah cikin takaici yace, Na gaya maku bata gidan amman kunki amincewa"

Aiko daga cen saman itaciyar Dije ta kai iya wuya sai jin suka yi tace,. "Barsu Baffahna idan ma sunki amincewa su kasheni idan na sauko"

Aiko gaba d'aya suka d'aga Kai suna kallon bishiyar cike da tanbabar a'ina maganar take fitowa, Dije ta kurawa tsohuwar Ido tana maka mata harara tace,. "WALLAHI da kin cikani ta kanki zan diro Uwar tsugudidin tsiya"

Aiko a lokacin suka tabbatar da ashe ma saman itaciyar ta b'oye, Bafaden ya zo gaban bishiyar yace

"Ki sauko salun alun tun kafin a sare itaciyar duka ki fado ki kakkarye"

Dije ta yi saurin fad'in

"Yasin ba zan sauko ba duk Mai son in sauko ya hawo ya sauko dani, amman kusani duk Wanda yayi wautar hawa bishiyar nan to ina maku albishir ba zai sauko da Ido d'aya ba, don kuwa sai nasa aljanina ya zuke idon muga ta tsiya"

Aiko jikin kowa yayi sanyi saboda sanin halin wacece Dijen da hatsabibancinta, daga nan aka fara shawarar wa zai hau ya sauko da ita? Aka Kai karshe akan Baffahnta ya hau ya sauko da ita, ganin gidan sai k'ara dinkewa yake yi da mutane yasa shi yanke shawarar hawa ya sauko da ita ko don a samu rangwamen hukuncin da za'a yanke mata.

Aiko ya kama bishiyar zai hau kenan Dije tace,. "Jira in sauko Baffah ai dai Raina a hannun ALLAH yake duk cikinsu Babu mai ikon kasheni"

Baffah yace,. "Sauko a hankali to ai duk ke kika jawo komi muna zaman zamanmu kika d'auko muna abun magana"

Dije ta fara saukowa a hankali har ta kawo kusa ta diro k'asa aiko caraf Bafaden ya riketa gam! Ya janyota tana tirjiya har suka fito gidan, sai fad'in take yi "ka jira in tafi da kaina ai ko? Tunda dai ba Kai ka cire man kafafun ba"

Amman Ina janta kawai yake yi da k'arfin tsiya cikin zafin nama tana tirjiya da gangan don kawai ta wahalar dashi, mutane ko suka biyosu buuu! Har k'ofar Gidan Maigarin inda nan ma mutane sun cika ana jiran zuwan Dijen.

Aiko sai gashi ana ganinta wuri ya fara dinkewa da zage zage da surutai, Bafaden cikin matuk'ar gajiya ya Kai Dije gaban Maigarin inda a kallo d'aya zaka gano kumburewar da Bakinshi yayi suntum! Saboda garin gudun tsoron kura ya buge Bakinshi.

Dije ta ki zama tayi tsaye ta rik'e k'ugu tana k'arewa su Hansai da Lanti da Mune da kuma jummala da Ladiyo, zuciyarta cike tsantsar fushi wanda k'iris take jira ta tada wata sabuwar fitina.

Aiko Maigarin yace da ita ta zauna ta yi Kamar bata jishi ba, Bafaden ya katsa mata tsawa yace

"Don kaniyarki ba da ke ake magana ba? ko sai na zaunar da ke da kaina?"

Dije ta galla masa wata uwar harara tace,. "Laisal matsi bi gairi haza takura ka barni inyi ijlis da duwawuna"

Aiko ya zabura ya Kai mata wani lafiyayyen mari har sai da tayi zaman yan bori, rik'e da gefen da ya maretan nan take idonta suka canza zuwa ja cikin zafin nama ta zabura ta mike tsaye ta heta kuwwa iya k'arfinta tace

"Yihuuuuuuhuu kurunkus kan dan bera"

Ta yi tsalle ta haye jikin Bafaden ta cafko wuyanshi ta rik'e gam! sai surutai take yi kamar wata mai aljanun gaske tana fad'in

"Sai mun cire wuyan nan dole ai yasin wanga kai dashi zamu yi kalacin dare yau makogoron nan kuwa dashi zamu yi busa, idanuwan nan kuma zamu saka a bindin jakinmu mulkutus barakus rik'e man hancin nan"

Aiko jama'a kowa ya mike sai turin juna ake yi wajen leken Dije da Bafade, shi kam da yaji wuya ta Kai karo zuciyarshi ta tabbatar masa da aljanu ne yake fad'a da su ba Dije ba, don ya kasa kwatar kanshi ga hannun Dije duk ko da take Yar firit ba wani jiki gareta ba ko kad'an, aiko ya fara kwarantin Kiran

"Innahu min Sulaimanu lak'ada kawas da bak'in Aljanin, don inji dad'in narkar da shegiya k'asa"

Aiko dakyar da jib'in goshi aka banbari Dije daga wuyan Bafaden, kafin kace me wuyanshi yasuntume suntum idonshi sun yi jawur duk ta yakushe masa fuska da akaifarta.

Ita Kam ana banbareta jikinshi ta fadi ta sheme sai surutai take yi sai kace daman cen aljanun gaske ne gareta.

Akafta😂

D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*INA GODIYA SOSAI DA COMMENTS DINKU💃🏻💃🏻💃🏻 K'arangiya tana gaisheku🤣*

*Lamba ta 3*

Bafade rik'e da wuyanshi yake fad'in,. "Akwai kan bisa wuyan ko ta yi sa'ar rabashi da gangar jikin??"

Gaba d'aya wurin yayi shiru wasu Kam basu daina yin dariya k'asa k'asa ba, Baffah jikinshi yana rawa ya k'araso wurin Dije zai tab'ata ta yi saurin fad'in

"Aljani danduna rik'e man hannunshi kar ka bari ya tabamu idan ya tabamu hannunshi zai k'one zai k'one kurmus tamkar yanda wuta take cenye kara"

Aiko da sauri Baffah ya ja baya Maigari yace da Liman ya matso ya yi mata addu'a da nufin a samu aljanun su kwanta ta karb'i hukuncinta, Aiko Liman yana matsowa kusa da ita ta yi wata zabura ba mutanen da ke wurin suna kallo ba har shi kanshi Liman sai da yaji tsoro, hannunshi yana rawa ya d'ora hannunshi akan goshin Dije ya fara tofa mata addu'a, Aiko Dije ta kurma kuwwa ta fara surutai tana cewa

"Ba zamu fita ba kama daina addu'ar nan ko'ina ba zamu je ba muna nan har sai Maigari ya janye kudurinshi na son d'aukar hukunci akan god'iyarmu, akanta zamu tada garin nan akanta zamu mayar da garin nan toka"

Liman dai sai zuba addu'a yake yi sai cen Dije tace

"Ayi hak'uri zamu yi magana za muyi magana nace"

Maigarin ya yi Liman alamu da Ido akan ya dakata aiko Dije ta fara fad'in

"Mune muka zama kura mune muka fito a siffar kura muka biyosu, kuma a gaban idonta muka kashe mutum biyar a farkon gari amman ba mutanenku bane mutanenmu ne, tunda ta take muna 'ya'ya muka biyosu ita da kawayenta, don yanzu haka abokan fadan nawa ya jiman raunuka saboda fad'an da muka yi da junanmu Ni da yan uwana aljanu don haka Bari in fito a siffata ku gani nasan zaku tausaya man"

Kowa na wajen yace

"A'a kar ka fito"

Wasu suka ce "ALLAH ya baka lafiya ka ja Yan uwanka ku tafi kawai mun yafe mata"

Dije ta sake cewa

"Idan na tafi kuka daketa fa ko kuka d'auki wani mataki kanta fa zan gayyato Yan uwana mu sake zama kuraye mu zo garin nan sai mun kashe kowa don kowa ma ba zai tsira ba"

Aiko cikinsu ya duri ruwa Maigari yace,

"Ba za'a tab'ata ba amman don ALLAH in kuna wa ALLAH ku yi nesa da garin nan, Kuma ku yi alk'awali akan ba zaku sake shiga shirginmu ba"

Dije tace "zamu tafi amman har sai mun mayarwa da sarkin fadawa kanshi da muka tsige"
Chapter 2 · 0% Book details