← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 84

Sashe 5

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aiko cikin Bacci INNA ta jiyo sautin daka tsakar dare ta waiga taga Baffa kwananshi kawai yake har da minshari, ta yi saurin dunkulewa cikin tsoro sai dai ta kasa kunne tana jiyo sautin kad'a turmin da wakar da ake yi sama sama, kafin kace me INNA ta fara jib'i don ko numfashi dakyar take bari ya fito don tsoro, sai cen ta ji an koma dukan langa langar da aka yi rufin madafinsu da shi, sai waka ake yi inda cikin wakar taji muryar Dije tana fad'in

" Gamu yau munzo a gidan nan!, zamu tsolale idon matar gidan nan!, don nasan tana saurarenmu a gidan nan!, gamu nan gamu nan zuwa wajenki ki fito Nan! ko mu zo da kanmu a nan wurin nan!, murkutus barakus matso nan! d'an jugumuna matso nan!, ku matso ku matso ku kamota a cen din!, don mu had'u mu tsigale idon nan!"

INNA ta zabura da k'arfi sai gata k'asa ta fad'o tim!, Har ta fasa k'ara ta yi saurin toshe bakinta, saboda har izuwa lokacin ba'a daina wakar ba sai ma maimaitawa da ake yi, INNA cikin rawar jiki da kyarmar tsoro ta fara bubbuga filon Baffah, har ta yi nasarar tashinshi cikin rufe baki alamun tsoro tana zaro Ido tana yi masa nuni da k'ofar d'aki, Baffah cikin firgici yace

"lafiya? Me aka yi ne na ganki haka"

Inna ta yi mashi alamu da ya sassafta murya cikin tsananin tsoro bakinta yana rawa tace,.

"Saurara ka ji"

Aiko Baffah ya taso ya tsaya jikin k'ofar ya kasa kunne yana sauraren wakar da Dije take yi, cikin fad'uwar gaba yace

"Innahu min Sulaimanu......"

Ya dawo cikin tsoro ya fara tofe Inna da addu'a shima ya tofe kanshi sannan ya nufi k'ofar da nufin ya bud'e, INNA ta zaro Ido tace

"Don girman Allah Kar ka bud'e"

Baffah ya juyo cikin rada yace,. "Ke a ganinKi don mun rufe d'aki bazasu iya zuwa su cire maki idon ba? To kinyi kuskure don haka Ni fita zanyi in basu hakuri in kuma Ni sun cire nawa idon a madadinki shikenan, sai da nace maki kar ki matsawa yarinyar nan ai gashi kin janyo muna jangwam!"

Ya nufi k'ofar cikin fushi ya fara kiciniyar bud'e d'akin aiko sai jin Suka yi garam! A guje dukansu suka nufi karkashin gado kowa yana turin Dan uwanshi domin ya samu ma b'oya.

Dije Kam jin muryarsu da ta yi ne ta shige d'akin Innar ta rufo k'ofar da sauri har sautin yace garam! d'in, don tsabar sauri ko sakatar bata saka ba ta dunkule gado tana minsharin k'arya, don nufinta ko da sun zo su taradda ita tana bacci don su gasgata abun da gaske ne ba shirinta ba.

Akafta🤣

D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻*

*Lamba ta 6*

Aiko mai makon taji shigowar su Inna sai taji saukar duka a jikinta, da sauri ta zabura ta fara sosa inda dukan ya sauka tana muzurai saboda ganin Yaya Usman a tsaye da bulalarshi a hannu, cikin fushi ya fara magana yana cewa

"Don Ubanki buge bugen Uban mi kike yi muna cikin dare?"

Dije ta zaro Ido waje tace,. "Buge buge kuma? Yaushe?"

Ya d'aga bulalar ya sake kai mata wani dukan aiko ta fasa Kara, Inna da baffa da tunda Suka jiyo sautin tafiyar Usman suka sha jinin jikinsu suna addu'a k'asa k'asa tamkar wasu sababbin larabawa, ihun Dije yasa Suka kalli Juna ba shiri Inna ta dafe k'irji tace

"Wayyo Ni Uwata wayyo Ubana Dije ALLAH ya kawo maki d'auki"

Baffah ya yi saurin kallonta yace,. " Mi kike nufi? Ai dole muje mu dubo mu ga meke faruwa"

INNA ta zaro Ido tace

"Wa? Ni! WALLAHI ka je dai nikam ba inda zanje kana jin tana zuba irin wannan ihun haka kawai ace tarko ne suka had'a man inje su tsigale man idanuwa su barni da kwarmin ido wayam ba komi"

Baffah ya maka mata wata jar harara ya fara gungurowa yana fitowa karkashin gadon, musamman kuwwar da yaji Dije tana zubawa yasashi k'ara kid'imewa ya nufi k'ofar d'akin a sukwane zai bud'e, daga cen karkashin gadon Inna tace

"Ka rufeni ta baya da kwad'o Don Allah kar ka barni a bud'e"

Baffah yayi saurin bud'e d'akin yana tofa addu'a a gaggauce saboda ihun Dijen da yak'i k'arewa, Aiko yana fitowa ya fara jiyo sautin Dije tana magiya har ya Kai bakin k'ofar ya dawo da sauri saboda sautin saukar dukan da yaji ana yiwa Dije, sai murzar hannu yake yi yana muzurai yana sake tofa wata addu'ar, sannan yayi kundunbalar fad'awa d'akin aguje kamar an jefoshi sai gashi karaf ya hango Usman da bulalar dokinshi yanata laftar Dije, cikin tsananin b'acin Rai ya d'auke Usman da wani bahagon mari sannan ya fisge bulalar cikin fushi ya fara fad'in

"Wane rashin Imani ne ya sakaka dukanta cikin wannan talatainin dare? Me ta yi maka da bazaka bari har safiya ta waye ba ka horatan?"

Usman cikin k'unar zuciya yace,. "Yanzu Baffah duk wannan iya shegen da take yi a cikin gidannan baka ji ba?"

Baffah ya yi saurin fad'in,. " Don naji sai Kuma aka ce maka itace mai yin abun? WALLAHI Usman ahir dinka ka kiyayi janyowa kanka abunda zai hanaka bacci mai dad'i"

Usman ya nufi hanyar fita yana fad'in,. "Duk buge bugen iskancin da tayi ta hana mutane bacci baka gani ba sai ma Ni laifina aka gani"

Cikin d'aga murya Baffah yace,. "Tunda ifrituwa ce ai dole ta fito cikin dare tana Wasa, WALLAHI in banda muke dare da yanzu sai na rama mata dukan da ka yi mata na d'aukar alhaki"

Ya dubi Dije cikin d'aure fuska yace,. "Me ya kaiki fitowa cikin daren nan kina buge buge?"

Dije ta fara matsar kwallah tace,. "Ba fa inda naje ina tsaka da baccina mai dad'i na ji saukar duka"

Baffah ya janyo hannunta ya zaunar da ita akan Gadon Innar yace,. "Kwanta kiyi baccinki ki barni dashi da safe zamu gauraya"

Dije ta share hawayenta da gefen dankwalinta ta lallaba ta kwanta, sai ajiyar zuciyar take yi cikin tausayinta Baffah yace

"Barni da shi da safe sai ya yi man bayanin dalilin da yasashi dukanki cikin dare, amman ke tsakaninki da ALLAH Dije ba ke bace? har da muryarki fa na jiyo kina rangad'a waka mai dad'i"

Dije ta Sha jinin jikinta tace,. "Nima na jiyo ana wakar Baffah amman wata murya daban ce na jiyo Ni, sai dai ban gano me ake cewa cikin wakar ba"

Baffah ya kalli k'ofar d'akin ya hadiyi miyon tsoron da ya sake diro masa yace,. "To dai yanzu ki yi addu'a ki koma kiyi baccinki kinji?"

Dije ta d'aga masa Kai ya fara tofeta da addu'o'i sannan ya zo zai fita ya juyo yace,. "Tashi ki rufe d'akin kada ya zo ya sake dukanki a banza"

Dije ta tashi zauna tana sharar kwallah tace,. "WALLAHI Baffah tsoro nike ji in kwana ni kad'ai sai inji anata kiran sunana wai in zo mu tafi bakin teku muyi wasa"

Baffah ya dawo da sauri jikinshi ya d'auki rawa yace,. "Ku tafi Ina?"

Ta turo baki tace,. "Wai bakin teku"

Baffah ya fara fad'in,

"K'alu Innalilahi wa'Inna ilairraji'una teku? Lalle akwai gurmi a gaba muddin ba'a daina jangwalo fushin dan Sarkin ba, jirani bari in zo yanzun nan"

Ya fice da sauri har yana tuntube ya nufi dakinshi Inna da ta ji fad'an Baffan da muryar Usman ta lallaba ta fito karkashin gadon, tana so ta fita tana jin tsoro sai ko gashi Baffahn ya shigo d'akin ranshi a b'ace yace,. "To tashi kije cen ki kwanta tun kafin safiya ta waye ki shafa kiga an d'auketa an tafi da ita, tunda ke Kika janyo komi to ki san hanyar da zaki gyara"

INNA ta zaro Ido tace,. "A d'auketa kamar ya?"

Kai tsaye Baffah yace,. "Kamar yanda kika saki kwanji kika lakad'a mata duka, haka su ma za suyi wuf da ita sama su je wasa da ita bakin teku, watak'ila ma shikenan ba zaki sake ganinta ba kinga sai ki sake haifo wata tunda ita kin janyo munyi asararta"

INNA ta mike jikinta yana rawa tace,. "Muje ka rakani in ganota Don Allah"

Baffah yayi kwanciyarshi yace,. "Ni da na je ke kika rakani ki je cen ku kwana da ita sai da safe ALLAH ya tashemu lafiya"

INNA ta dad'e tana kallonshi gano da gaske yake yi yasa ta ja kafafuwanta ta fice, tafe take tana addu'a har ta isa d'akin, sai dai ganin Dije da tayi a zaune tana sharar hawaye yasa ta k'arasa wurinta da sauri tace,. "Ke lafiya kike kuka?"

Dije wasu hawaye Suka zubo mata tace, "ba Yaya Usman ba ne ya zo yayi ta dukana bayan ban yi mashi komi ba"

Inna ta yi saurin zaunawa tace, "au! Shine yake dukanki kike ihu?"

Dije ta saka bayan hannu ta share hawayen da suke sauko mata tace,

"Shine"

Inna ta yi saurin fad'in "to me kika yi masa cikin daren nan?"

Dije ta zumburo Baki tace,. "Wai cewa yayi na fita inata buge buge bayan Ni tuwo kawai naci na dawo d'aki ina cikin Bacci naji yana dukana"

INNA ta zaro mata Ido tace

"Kin dai fitan ko?"

Dije ta gyad'a Kai, Inna ta maka mata wata jar harara tace,. "Aiko naji dad'in da ya jibgeki don dama ace bai dake kin ba to da Ni yanzu sai na yi maki nawa dukan, don ina da tabbacin kece kike ta daka kina dukan rufin madafinmu kina waka"

Dije ta yi saurin ja da baya tace,. "Nasha aradu ba Ni bace nima Ina Bacci naji ana ta yi"
Chapter 5 · 0% Book details