← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 84

Sashe 67

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasa wasa sai ga Dije zaman ɗaki ya fara aurarta don kuwa yawan kiranta da yake yi yasa bata zama cikinsu Husnah, don yanzu ita kanta Aunty Ummin har ta fara yi mata tsarguwa akan soyayyar da suke kwasa, saboda yanda suke baje kolinsu ita da Malaminta abun ba kama hannun yaro, saboda da an taso school baya dawowa wurin Zee sai dare ya tsala sannan ya dawo ya lallaɓa ya kwanta, tun bata kulawa har ta zo ta fara damuwa tana yi masa ƙorafin rashin zama gidan da baya son yi, ba wani rufe rufe ya sanar da ita saboda baya son ranta ya ɓaci shiyasa ya ke zamanshi a cen wajen don kada ya shigo ya yi wani abun da zata ga kamar ya ci mata fuska, Zee ta fashe da kuka ta ce da shi ita sam bata yarda ba dole ne itama ya bata haƙƙinta itama tana buƙatar kulawarshi kuma ya bata lokacinshi su yi fira tunda ba ta da wani wanda zai ɗebe mata kewa a gidan bale su yi firar.

Ganin ta ɗaga hankalinta ne akan dole sai ya zauna gidan ya fara rage lokacin da yake yi a wajen, cikin haka ne watarana yana chatt da Dijen wani uzuri yasa ya ajiye wayar ya fita, jikin Zee yana rawa ta ɗauki wayar ta fara yi masa bincike saboda ko kaɗan baya bari ta taɓa masa waya, sunan da ta ga Ni saman contact chat ɗinshi ne ya ja ra'ayinta da shiga kundin ma'adanar, sai gata da zaro ido waje saboda mugun ganin da idanuwanta suka yi mata don kuwa photon Dijen ne daga ita sai wata vest shara shara ko hannu bata da kuma gaba ɗaya shafin dukiyar fulaninta duk a waje don har kan nipple ɗinta ana hangowa cikin yar rigar, ba shiri ta kai zaune dafe da zuciya hawaye suna zuba akan fuskarta tamkar famfo, fige wayarshi da ya yi ne a hannunta yasa ta yi saurin kallo inda yake idonta a kanshi ta ce

"Eh kam naga abunda kake ta aikatawa kullum shiyasa baka bari in tab'a wayar, wanda akanshi ne ma ka ke ɗaukar lokaci a waje baka dawowa gida sai dare ya tsala, to ita kuma wannan yar aikin taku da ka ce wa aikatau aka kawota gidanku yanzu kuma akanta ka lalace??, To billahillazi wannan karon sai dai ayi abunda za'a yi ko ni ko ita WALLAhi, don kuwa akanka wallahil'azim ko kasheta zan iya yi matuƙar ta sake shiga sabgarka, na fi son idan har na kasheta ni ma a zo a kasheni"

To fa wata sabuwa na yi nan WALLAh🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ tun kafin Zee ta gano ina masu leƙe ta shaƙo wuyana😅

Ina baran adduarku akan ALLAH ya baiwa Mahaifiyata lafiya mai ɗorewa😢saboda kwana biyun nan jikin sai a hankali😭

Akafta😝

D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Alhmdllh jikin Mummy ya yi sauƙi masha ALLAH, naji daɗin addu'o'inku sosai da sosai, hakan ya tabbatar man da cewa ni ma ɗin ashe kuna yi na😉, don da har na fara kishi da Dijen Baffah saboda yanda naga kuke sonta da yawa, shine na yi zaton kamar ta fini matsayi😅 ashe dai Ni ma ɗin ta ku ce ba algus tom Alhmdllh na gode sosai🙏🏻*

*Lamba ta 62*

Safwan ya bi ta da kallo baki a sake ya ce "wai ke me yasa ko kaɗan ba ki da hankali ne?, Yanzu ke ashe zaki iya kashe mutum da hannunki saboda kishi?"

Ta murguɗa masa baki tare da riƙe ƙugu tace, "kai da bakinka ka sanar da ni cewa ƴar aikinku ce, kuma daga kai har munafukar ƙanwar ta ka kun nuna man cewa ita ce ke sonka kai baka sonta, to yanzu kuma akan mi take bibiyarka? kuma sannan har ka bata damar da Ni ma da kake aure baka bani irinta ba? Ga shi ka janyo ta yi nasarar shiga tsakanina da kai, don na tabbata akanta ne kake raba daren da kake yi a waje, to WALLAHI ka ji da kyau ka ƙara ji matuƙar baka sanar da ita ta fita sha'aninka ba WALLAhi ka ji na rantse sai na watsa mata fetur na ƙoneta ƙurmus kowa ma ya huta da mugun halinta na bin Mazajen mutane, yar iskar banza baƙar karuwa ALLAH ya tsinewa iyayen da suka kawota duniya ma balle it.......... "

Saukar marin da ta ji ne a kumatunta yasa ta yi saurin haɗiye sauran maganar, cike da mamaki ta ke kallonshii hawaye suna sauka akan idonta ta ce

"My man ni ce na zama jaka a hannunka saboda matarka?, Yanzun ma kuma saboda da tsananin lalacewar akan wata ƙaramar karuwa ka ɗaga hannu ka mareni?"

Safwan ya yi saurin ɗaga hannun da nufin ya ƙara kai mata wani marin, me ya tuna kuma ya dunƙule hannun ya naushi iska sannan ya nunata da yatsa kamar zai tsole mata ido, jikinshi sai tsuma ya ke yi saboda tsabar ɓacin ran da ta cusa masa, ya ce

"Duk ranar da kika sake kiran Matata da sunan karuwa to WALLAHIL'AZIM kin ji na rantse a ranar zaki gano ainahin wanene Safwan, don kuwa sai na yi maki dukan da a RAYUWARKI kaf ba'a taɓa yi maki irinshi ba"

Sannan ya cisgo gashinta da ƙarfin gaske ta yi ƙara fuskarshi daf da tata suna kallon juna ido cikin ido ya ce

"Wannan da kike gani ita ce Matata Khadija kuma Uwargidana wadda kike da labarin na aureta tun kafin ke, zancen Ƴar aiki ya riga da ya wuce tuni don daman cen kawaici ne na yi maki na ƙi sanar da ke gaskiyar wacece, saboda kawai bana son ranki ya ɓaci idan kin ji ina da aure, to amman yanzu tunda har kin gano komi to kenan ɓoyon da nake maki ma ba shi amfani, saboda haka ki kwantar da hankalinki zan baki wata dama"

Ya fidda wayar da key ɗin da take ya damƙa mata wayat a hannu cikin fusata ya ce "karɓi ki shiga chat ɗina da ita da kike son ganin abunda ake yi maki ɓoyo kullum, to yanzu ki shiga duk inda kike so na baki wannan damar ki karanta komi kuma ki ga komi da idonki, kin ga kin hutar da ni akan duk wani labari da zan sake ba ki a yanzu kuma da gaba ma idan ta kama, na ba ki awa biyu ki yi duk abunda kike so saboda kawai idan kin ta shi kashetan sai ki haɗa da Ni, ke in ma da hali ki fara ta kaina kafin zuwan lokacin da za ki haɗu da ita itama ki kashetan"

Yana ƙare maganar ya fice ya barta da waya a hannu baki a sake kamar wata sakarya, idonta akanshi suna zubar da hawaye wasu bayan wasu, saboda tsabar baƙin ciki da takaicin da ya cika mata ciki, cikin sauri ta jefar da wayar kan kujera itama ta durƙushe ƙasa tana wani irin kuka gwanin ban tausayi.

Saboda izuwa lokacin ta fara yin nadamar biyewa son zuciyarta da ta yi ta aureshi, yanzu ga shi ba'a je ko'ina ba ta fara cin karo da takaicin auren mijin wata da ta yi, don ta tabbata inda Aminu ta aura to da babu yanda za'a ya yi mata irin wannan wulaƙancin akan wata mace, tuno irin renin hankalin da ta yi wa Aminun yasa ta ƙara sautin kukanta, don har awa biyun suka cika ya dawo bata daina kukan ba.

Ganin hakan ya ji jikinshi ya yi sanyi ya zo inda take ya ɗagota daga durƙushen ya zauna kan kujerar da ita a jikinshi yana bubbuga bayanta alamun ta yi shiru, saboda shi kanshi zuciyarshi cike take da ƙuncin da ya fi nata, saboda har ga ALLAH ba da son ranshi ya ke yi mata abunda ya ke yi ba, kawai dai don ya kasa controlling ɗin kanshi ne akan Dijen Baffah, shiyasa ya ke jin komi ma zai iya aikatawa in dai hakan zai farantawa Dijenshi, don izuwa lokacin ya fara fahimtar irin yanda take sonshi itama, kawai dai tana ɓoyewa ne don bata son ya fahimci itama ta yi kewarshi don wata manufa ta ta da shi bai gano nufinta ba, haka ya danne ta shi damuwar ya koma lallashinta har ya samu ta yi shiru sai dai ta ƙi cewa da shi ƙanzil har suka shiga bacci.

****

Haka rayuwar auren nasu ya ci gaba da zama yau fari gobe baƙi, duk da ya rage wasu abubuwa da yawa don kawai su sami zaman lafiya, amman kishinshi da Zee ta ke yi abu kaɗan ne zai janyo masu matsala sai an hau sama a dawo a shirya, don izuwa lokacin ita kanta ta matsu da su gama karatun su dawo gida, saboda tunanin da take yi yawan yi akan ita fa muddin bai canza hali ba idan suka dawo gidansu zata koma, ta sa Mahaifinta ya karɓar mata takardarta, don ba zata zauna ciyon zuciya ya kasheta da ƙurciyarta ba akan wata ɗiya macen da bata fita da komi ba.

Haka rayuwa ta yi ta shurawa sati ya zo ya wuce wata ya zo ya wuce shekara ta gangaro itama har ma ta nemi wucewa, sannu a hankali sai ga su Safwan sun kammala karatunsu, sun ƙara wasu watanni ne saboda su harhaɗa komi sannan su dawo, duk da turawa sun so su riƙesu su yi aiki da su ko na shekara ne, amman fafur Safwan ya buga kanshi akan cewa ƙasarsu za su koma itama ta moresu.

***

Dije kam a lokacin tana Ss 3 har ana cukucukun fara jarabawar candy, ga shi Hajiya Mama ta yi wa Safwan alƙawarin duk lokacin da zai dawo zai taradda ita cikin gidanshi, sai dai karatun da take yi yana so ya wargaza alƙawarin, don bata son ta dawo ba tare da ta kammala karatunta ba, amman duk da hakan da lokacin dawowarshi ya ƙaraso dole ba don dukansu sun so ba Aunty Ummin ta tattaro khadija ta dawo da ita Yola.
Chapter 67 · 0% Book details