← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 84

Sashe 10

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Dije shine kika ki tsaya man in fa an kamani kice me?"

Dije ta kalleta Kai tsaye tace, "Zan ce Sabida kinje ganin Yan birni ne sun kamaki kina lekonsu"

Jummala ta zaro ido waje tace,. "To ai kece kika leka ba Ni ba don ni ban ma hangosu ba"

Dije tuno abunda ta gani yasa ta yi saurin rufe fuskarta tace,. "Ai nikam na ganowa kaina shiyasa Inna tace leke baya da amfani don garin leken sai ka ganowa kanka abunda ba shi ba ashe da gaskiyar Innata"

Jummala ta bi ta kallo mai cike da son karin bayani tace,. "Me kika gano halan?"

Dije ta runtse idonta da sauri cikin jin kunyar kanta tace,. "Kinga Jummala bazan iya tuna komi ba tashi muje gida tun kafin a gano mu ne muka lekasu idan har ya sanarwa da Maigari"

Jummala ta Mik'e jikinta yana rawa tace,. ,"Hakane fa to Ni dai Kinga na tafi ko banza tallah zan je ma yanzu"

Jummala ta yi hanyar Gidansu Dije ta yi Gida zuciyarta sai wassafa mata Yanayin da taga Safwan d'in take yi, inda take jin kunyar kanta da kanta saboda mugun ganin da idanuwanta suka yi.

Aiko haka ta kwana duk wani motsinta sai taga fuskar Safwan tana yi mata gizo yana harararta tare da yi mata kashedi da gargadi kala kala, don har Inna sai da ta gano akwai abunda yake damunta, amman da ta tambayeta tace, "wasu bak'in Yan boko suka zo garin nan zasu koya muna karatun Boko, shine na matsu Litinin ta zo mu fara zuwa Makarantar".

Inna kam sanin wacece Dije dangane da son karatun yasa ta amince, sai ko gashi ko da safiya ta waye aka yi gangami akan kowa ya taru k'ofar Gidan Maigari ana nemansu babba da yaro, aiko cikin kankanin lokaci aka hallara k'ofar gidan inda kai tsaye Maigarin yayi masu bayanin zuwansu Safwan da Lawi da dalilin da ya kawosu garin, inda yayi masu gargadi da jan kunne sosai akan tabasu da abunda zai biyo bayan hakan.

Aiko kowa jikinshi yayi sanyi duk da wasu da yawa cikin garin bokon ba damunsu yayi ba bale har su damu da wani zuwansu, don da yawa cikinsu yaransu ko Makarantar basu tab'a lek'awa ba, masu k'ok'arin zuwan ma irinsu Dije kasancewar Malamman daga wani babban garin da suke a karkashinshi ne ake turosu, saboda sun fahimci daliban kalilan ne yasa suke yin tsalle akan zuwan nasu garin kullum, don wani zubin ma sau biyu ko sau uku ne suke zuwa a sati har ta kai yaranma kansu basu zuwa Makarantar sai ranar da suka san malamman zasu zo,Dije ma tana cikin masu k'ok'arin zuwa Makarantar na sahun farko, don wani zubin ma a sanadinta wasu yara da yawa suke zuwa Makarantar don habaici da take yi masu tana yi masu gorin cewa su jahilai ne tunda har basu iya abacada ba, amman duk da hakan a class d'aya duka ba zasu wuce mutum biyar zuwa shida ba, yanzu haka aji biyar Dije take a Makarantar tare da su Jummala da su Hansai, yan ajin shida mata duka anyi masu aure mazan kuma daman cen karatun bai wani damunsu ba.

Haka Maigarin ya Kare yi masu bayanin ya gabatar da su Safwan garesu, Lawi dai kam ya saki jiki yayi masu bayani dai dai da saninsu amman Safwan kam iyakacinshi gyad'a kai yana dariyar yake, saboda shi warinsu ma yakeji yana damunshi a gundure yake da akai k'arshe ya bar wajen.

Da ma aka zo kanshi akan ya tofa albarkacin bakinshi don tsabar renin hankali irin nashi da harshen turanci yayi magana, dukansu ko sai zarar Ido sukeyi suna kallon Bakinshi don su ko zo in kasheka da turancin basu sani ba, bayan ya k'are bayanin ne Abokinshi Lawi ya fassara masu abunda ya fad'a tare da yi masu bayanin cewa Safwan bai iya hausa ba baya jin yaren sam, Dije kam tana jin haka tace

"Tab! Kace dai shi d'in katon kafuri ne ya zo muna cikin gari? To sai ka barshi ta k'arfin tsiya tunda mu babu irinka marar sallah cikinmu"

Lawi yayi saurin Kai kallonshi ga Dije don yaga yanda take murgud'a Baki sai makawa Safwan harara take yi tana mui mui duk da baisan me take fad'a ba amman ya gano bakinta ba alkhairi yake fad'a ba, cikin wayancewa ya d'aga murya yace

"Magana kike yi ne?"

Dije ta yi saurin Shan jinin jikinta tace,. "Me kaji nace?"

Lawi yayi Yar dariya yace, "na zaci akwai wata tambaya dangane da abunda ya shige maki duhu akanmu ne"

Dije ta wani mere tace

"Ba komi wancen din ne kawai nake ta ganinshi Kamar ba musulmi ba"

Safwan yayi saurin Kai kallonshi gareta Aiko sai gashi ya gano fuskarta da idanuwanta da ya kasa mantasu tun lokacin da ta zuro kanta wajen lekenshi sukayi four eyes, aiko sai gashi da jin wani sabon b'acin Rai ya ziyartoshi, saboda daman cen da takaicinta da garin nasu duka ya kwana yana tsinewa wanda yayi tsanin postoshi garin, inda abokinshi Lawi yayi ta yi masa dariya don waya ma har sai da suka tambayi Maigarin yasa aka kaisu wani wuri nesa kad'an da cikin garin inda ake samun service, sannan ya yi waya da Yan gidansu ya sanar dasu halin da garin yake ciki don kada su kirashi suji basu sameshi ba su d'aga hankalinsu.

Shima Lawi yayi waya gidan nasu da abokan arzik'i sannan suka dawo zuciyar Safwan kamar ta fashe saboda takaicin garinsu Dije, da yake yiwa 'yan garin kallon bagidajai tamkar wasu mahaukata saboda kyankyaminsu da yake yi, don ko abincin da aka basu baici ba fiddo rishonsu yayi ya kunna ya dafa indomin da suka yo guzurinta kwali kwali, sannan ya kwankwadi ruwan gorarshi da ya zo dasu catoon catoon yasha ya jefar da gora sannan yaji hankalinshi ya dan kwanta.

Lawi kam sakin jikinshi yayi ya ci abincinshi kuma cikin dace yaji dad'in abincin don ba laifi basu da wata shahararriyar kazanta sukam.

Idonshi akanta yana jin tamkar ya shaketa a wurin, inda itama shi d'in take kallo tana yi tana harararshi tana murgud'a masa Baki tana mui mui.

Ranshi a matuk'ar bace ya mike ya koma d'akin da aka basu zuciyarshi cike da kuna tamkar yasa bindiga ya bindige kowa ma na garin yake ji saboda takaicinsu da abunda Dije ta yi masa yanzu.

Dije kam binshi ta yi da kallo tana yi masa hararar gefen Ido har ya bar wajen, sannan ta cije lebe tana wassafa irin matakin da zata d'auka a kanshi don ta ga kanshi yana rawa.

Har aka gama jawaban aka watse tunaninta baya wajensu tafe take zuwa hanyar Gidansu tana tunanin abunyi har taje Gida, aiko tun da sassafe Dije ta shirya cikin uniform d'inta da sukasha wanki tun jiya da marece, ta linkesu ta saka a karkashin filonta suka kwanta luf tamkar anyi guga, sannan ta baje ta zuba kwalliyarta da digo digon kwalli a fuska ta ranbada janbakinta ram a Baki taja Jakarta tana yiwa Inna da Baffah sallama.

Inna ta bita da kallo tace,. "Lalle wad'annan bak'in turawa da Sa'a suke, irin wannan kwalliya haka sai kace ranar JUMU'A??"

Dije ta rufe fuskarta tace,. "So nike yi abani shugabar Makarantar Inna naji wani Malami ranar yana cewa duk wadda kayanta suka fi haske itace za'a baiwa, don naji ma ranar yana magana da wani Malamin wai Ni yakeso a saka"

Inna ta rik'e baki tace

"To kenan ba ta k'ok'ari ake bi ba??"

Dije ta yi saurin fad'in

"To ai nafi kowa k'ok'ari ke Inna shiyasa ma da bak'in suka zo Ni aka baiwa takarda na karanta, baki ga yanda na burge kowa ba saboda turancin da nayi ta karantawa kamar ba Ni ba"

Sai jin Suka yi ance "Kika iya karanta shirme dai, ai an fad'a mani komi bale ki zo ki dinga yiwa mutane bak'ar k'arya"

Usman da ke shigowa cikin Gidan ya katse masu firar, Dije ta zunburo Baki ta yi d'akin Baffah tace

"Baffah na tafi sai na dawo kayi man addu'a"

Baffah ya fito yana yi mata adawo lafiya ta fice cikin sauri don gudun Usman ya ci gaba da fallasa gaskiyar karyar da ta yiwa Innar.

Tun daga nesa ta hango Mutanenta da ke zaune bakin doguwar barandar ajijuwan hudu da ke Makarantar, wad'anda su kadai ne a duk fad'in Makarantar saboda rashin Muhimmancin da basa baiwa bokon bale har su nemi gudunmuwar gwamnati akan ta k'ara masu wasu ajujuwan domin k'ara fadada Makarantar.

Dije kam tana hangosu ta had'e Rai fuska murtuk'e alamun ba wasa tana tafe tana wasa da Karen da ke hannunta har ta zo ta gabansu zata wuce ko kallo basu isheta ba, Lawi ya bita da kallo yana dariya Safwan kam a hasale ya ce

"Hey you come here"

Dije ta waigo ta murgud'a masa Baki taci gaba da tafiyarta, aiko ya kara d'aga murya yace

"Stupid girl I say come here"

Dije ta waigo ta sake murgud'a Baki ta yi gaba, Lawi da dariyar da yake makalewa taso fitowa yayi saurin fad'in

"Da ke ake magana fa ko baki ji bane??"

Dije ta waigo cikin dan guntun ladabinta tace,. "Ai ni to bansan me yake cewa ba"

Lawi ya had'e fuska yace,. "Ki zo aka ce"

Dije ta dawo tana cin magani tace,. "Ai Naga banyi latti ba shiyasa"

Ta zo ta tsaya kansu kikam tare da rik'e kugu tana yiwa Safwan wani mugun kallo sannan ta kalli Lawi tace,. "Gani Malam"

Lawi yana kumshe dariyarshi yace,. "Kinga wanda ya kiraki nan ko shi ba Malamin bane?"

Dije ta kawar da kanta a gefe ba tare da tace kanzil ba, cikin fushi Safwan ya ce da ita

"Stupid girl kneel down!"

Cikin tsawa yayi maganar ya taso Kamar zai daketa, Dije ta yi saurin durkusawa k'asa cikin gunguni tana fad'in,

"Kaci sa'a nasan wannan da WALLAHI bazan durk'usa ba"

Aiko cikin fushi Safwan ya cira hannu ya gaura mata wani azababben mari, tare da nunata da yatsa cikin harshen turanci yace

"Zaki fad'i abunda kika ce ko sai na kifar da ke a k'asa??"
Chapter 10 · 0% Book details