← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 84

Sashe 25

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan ta ajiye ledar wainar ta d'auko wata leda sai ga k'aton Biredi ta zaro ido tace,. "Idona idonka WALLAHI wayyo ALLAH dad'i na gode sosai ka ji in akuyata ta haifu na yi maka alk'awali zan baka abunda ta haifa kyauta ai kana so ko?"

Safwan ya shafa gemunshi yace,. "A yi ta kaya Ni kam na yafe"

Dije ta zunburo Baki tace,. "Don ma ka samu zan baka?"

Tana k'are fad'ar maganar ta ciro ledar shayin ta huda ta fara gutsuro biredi katoto guda ta kurbi shayin, tace

"A'a'a'ah haka shima
nasu shayin yake da dad'i haka? Wayyo har wani k'amshin dad'i yake yi yasin, Kai garin dad'i na nesa Kai! Kai! Kai!"

Haka ta dinga sambatu tana Shan shayin da biredin har ta kusa canye rabin ledar biredin sannan ta yi gyatsa tace,. "Alkur'an yau na yi cin haram ALLAH ya jikanki Dije ina Innata tana kusa ta ci itama ta ji"

Ta mik'awa matan biredin da ledar shayin ta shafa cikinta tace,. "Sai ka sacce in sake cin wainar itama inji ya take"

Kafin ka ce me sai ga Dije da langabewa tana bacci sai ajiyar zuciya take saukewa a hankali, Safwan ya kai kallonshi gareta ya girgiza Kai a ranshi yace,.

_"Dole ki yi bacci wannan ci da kika yi kam acicin banza wa'kazuba"_

Sannan ya mayar da hankalinshi akan tuk'inshi yana yi yana murmushin da shi kad'ai yasan ma'anarshi.

Tafiya ta mika Safwan da sauran abokan tafiyar sai shillawa suke yi Kan titi suna k'ara nausawa Kan hanyarsu, Dije kam har lokacin baccinta take yi har sai da lokacin sallah yayi Suka tsaya suka yi suka ci abinci Suka k'ara mikar titi tun suna jin dad'in tafiyar har dukansu suka fara jigata musamman su Baffah da Basu tab'a irin tafiyar ba, Dije kam duk sai da ta canye komi sannan ta ji natsuwa ta zo mata, shiyasa ba wuya ta sake komawa bacci har duhun dare ya sauka.

K'arfe d'aya saura Suka isa garin Gombe inda suka yada masauki a wani hotel da nufin tun da sassafe su kama hanyarsu ta zuwa Yola.

Akafta👍🏻

D/AUTA CE🤝🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*GA KIRA DA BABBAR MURYA BAN YARDA BA KUMA BAN AMINCE BA BAN LAMUNTA A CANZA A SARRAFA MANI LITTAFAINA BA TA KOWACE SIGA*
*TARTSATSI.*
*RUWA DA KANKARA.*
*DIJE K'ARANGIYA*
*NI HADIZA D/AUTA BAN LAMUNTA BA AKAN KOWA YA SARRAFA MANI LITTAFAINA BA BA TARE DA IZININA BA AKASIN HAKA KUWA WALLAHIL'AZIM ZAMU GAURAYA DA KOMA WACE DON SAI NA JA HAKKINA AKAN KOMA WA YE A BI DOKA A ZAUNA LAFIYA🤝🏻*

*Lamba ta 26*

Hak'ik'a ba k'aramin k'auyanci Dije da Baffah'nta da 'yan rakiyarta suka yi a Hotel d'in ba, sai dai kasancewar su Safwan d'in sun san daga ina suka fito shiyasa ba su yi mamakin hakan ba, don Dije A.c'n da ta zuk'a ya sata bajewa tana bacci har da su minshari, daga ita har abokan tafiyarta don dak'yar aka tashesu suka yi wanka mai cike da k'auyanci shi ma, sannan suka yi breakfast suka shirya suna jiran Safwan ya dawo daga fitar da yayi cikin gari su tafi.

Aikuwa Safwan fitarshi ke da wuya bai zame ko'ina ba kai tsaye sai Gidansu Lawi, inda ya taradda shi kwance yana bacci kasancewar d'akinshi lik'e yake da gidansu k'ofarshi tana kallon hanya.

Ba k'aramin mamaki Lawi ya yi ba da ya ganshi, cike da d'okin son jin wani labari daga Dijenshi ya yi saurin wartsakewa yace

"Abokina wannan tafiya babu sanarwa fa? Ko dai bazata ka zo ka yi man akan ka sanar dani cewa an amince in zo in auri Dijena? WALLAHI yanzu haka da ka ganni mafalkinta nake yi"

Safwan ya b'ata fuska tare da mik'ewa tsaye ya fito da kud'inshi da Dije ta bada a bashi ya ajiye masa a gefen katifarshi, sannan ya soka hannunshi duka a aljihu yace

"Ga kud'inka nan inji Khadija ta ce in kawo maka, saboda gidansu ance bazata karb'a ba don Ni ma ban so na rabata da kud'in ba shine ta wurgosu d'akinmu ban sani ba ta tsere abinta".

Lawi cikin tsananin firgici tare da fad'uwar da gabanshi yake ta yi da sauri da sauri yace

"Yanzu shi kenan ana nufin an rabani da ita da gaske an aurawa wani ita wanda bai san darajarta ba?, D'ankauye irinta wanda ba zai taimaketa ta cika gurinta a rayuwa ba?"

Ya k'are maganar tare da zubowar wasu hawaye masu zafi akan fuskarshi, Safwan ya yi taku d'aya biyu tare da juyawa Lawi baya sannan ya furzar da iska mai k'arfi a bakinshi yace

"Gurinta zai cika Insha ALLAHu kamar yanda kake yi mata fata don ni zan rik'eta da zuciya d'aya har sai na tabbatar da ta cika gurinta na zama likitar kamar yanda take gurin zama"

Lawi cikin k'ullewar kai da maganganun Abokin nashi ya yi saurin mik'ewa tsaye ya fuskanceshi idonshi fes akan fuskarshi zuciyarshi cike da wasi wasi yace

"Fashe man bak'i akan abunda kake nufi Abokina, don zuciyata ta fara hasasoman abunda nake hangowa kamar ba gaskiya bane"

SAFWAN ya saka hannu ya dafa kafad'ar Lawi yace,. "Ka d'auka cewa komi rubuce yake a Littafin kundin k'addararmu mai kyau ko akasin hakan, kuma ka d'auka cewa matar mutum kabarinshi wani ba zai tab'a auren matar da ba tashi ba"

Lawi cikin matsananciyar damuwa yace,. "A tak'aice kana son ka sanar dani cewa anyiwa Dije aure kuma ba da d'ankauyensu ba to da wa aka d'aura da har zaka d'auki nauyin cikar burinta??"

Ya k'are maganar cikin yi masa kallon tuhuma, cikin sanyin jiki tare da daburcewa Safwan yace,. "A lokacin da ka baro k'auyen KHADIJA ta tub'ure akan ba zata auri wanda aka zab'a mata ba, ganin hakan Mahaifinta ya ce ta je ta auri wanda take so amman a rana da lokacin da aka saka da wancen d'in, idan ba haka ba shi ba zai fasa auradda ita ba kuma ba zai d'aga lokaci ba, shine da ta zo ta sanar dani na yi ta neman layinka ban sameka ba gashi lokacin ana saura kwana biyu, hankalina ya tashi sosai ga Yarinyar ta d'aga hankalinta akan rashin samunka da ba'ayi ba, shine ta rok'eni akan don ALLAH ni in amince in aureta"

Rassssss! Gaban Lawi ya buga ba shiri hawayen da yake mak'alewa suka gangaro masa cikin muryar kuka yace,. "Ba sai ka k'arasa dogon labarinka na k'arya da ka shiryo man ba wanda ko kad'an k'arya bata kamaceka ba don ba halinka ba ce, na fahimci inda duk ka dosa don daman cen na dad'e da gano kana sonta, na kyaleka ne don kawai inga iya gudun ruwanka ka je kawai ALLAH ya baku zaman lafiya, kuma Ni na yafe maka duk abunda ka yi mani saboda kawai nasan cewa kula mata ba d'abi'arka bane, Kuma na godewa ALLAH da ya jarrabeka da son abunda ka rena ko don ka fahimci cewa wulak'ancin da ka ke yiwa Mutane ALLAH ya nuna maka cewa su d'in ba abun reni ba ne, ka je kawai ALLAH ya baku zaman lafiya amman ka sani naji haushin da tun farko ka b'oye mani cewa kana sonta, ka barni sai da na zurma da yawa sannan ka dawo ka kwaye mani baya ka sani amincinmu bai ci haka ba"

Yana k'are maganar ya fice d'akin cikin sauri, Safwan ya bishi da kallo zuciyarshi cike da takaicin abunda ya aikatawa abokinshi, jiki a sanyaye ya janyo k'afafuwanshi ya shiga gidansu Lawin, kasancewar sun sanshi sosai Shiyasa suna jin sallamarshi k'anwar Lawi ta lek'o tana ganinshi ta koma da sauri ta yi cikin Gidan, sai gata ta dawo tace da shi ya shigo

Safwan ya shiga zuciyarshi cike da jin kunyar abunda ya yiwa Lawi, ya isa wurin Mahaifinshi da ke zaune yana fama da jiki ya gayar da shi, sannan Mahaifiyar Lawin ta zo itama suka gaisa, suna yi masa ya Hanya.

Banyan sun gama gaosuwar ne Mamar Lawin tace,. "Aiko ina jin yana d'akinshi ko kun had'u?"

Safwan ya duk'e kanshi yace,. "Eh mun had'u daman wucewa zan yi nace bari in zo in ga jikin Baba, ALHAMDULILLAH ma naga lafiya ta samu"

Mamar tace,. "Eh ai kwanan nan Masha ALLAH jikin sauk'i sai samuwa yake yi"

Safwan ya zura hannu aljihu ya fiddo kud'i masu d'an kauri ya ajiye a saman shimfid'ar Baban yace,

"Ga shi Baba ni zan wuce ALLAH ya bida lafiya"

Mahaifin Lawin yace

"Masha ALLAH Safwanu ALLAH ya tsare ya kaika lafiya ka gayar da mutanen gidan duka"

Haka suka yi sallama ya fito sai dai kam ba Lawi ba samatarshi, haka aka yi ta bulayin nemanshi akan su yi sallama da Safwan amman ba'a ganshi ba, dole ya lallab'o ya baro unguwar cikin jin haushin kanshi akan me yasa bai hak'ura ya barwa Abokin nashi ba, wata zuciyar tace da shi

_"To Kai fa ko ka manta halin da ka shiga ne akan ganin zata sub'uce maka?Shareshi kawai zai hak'ura ne daga baya"_

Haka ya nufo Hotel d'in suka d'uru motocinsu suka kama hanyarsu ta zuwa Yola, har suka isa zuciyarshi bata daina yi masa canki in canka ba, a k'arshe dai ya tsayu akan magana d'aya wadda yake ganin itace mafitar da zai wanke laifin da ya yiwa Abokinshi.

Kasancewar an san da zuwansu shiyasa kai tsaye aka wuce da su ainahin gidansu Safwan d'in, aikuwa sai ga Mahaifiyarshi da k'annenshi biyu sun fito tarbarsu cike da d'okin ganinshi, Mama Hajiya waton Mahaifyar Safwan kai tsaye wajen Dije ta nufa inda zuciyarta ta tabbatar mata da itace Matar Safwan d'in, duk da zuciyarta ba k'aramin bugawa ta yi ba lokacin da ta yi arba da Dijen ba, sai dai ta mazge ta rik'o hannunta tace

"Oyoyo 'yata sannu da zuwa"

Dije ta bita da kallo Baki washe tace,. "Laaah! Ashe kin sanni??"

Safwan ya yi saurin fad'in "to maganatu ke bakinki ba zai yi shiru ba? Ko gaisawa ba'a yi ba sai surutu"

Dije ta sunne kai tare da maka masa hararar gefen ido ta kalli Mama Hajiyar ta rusuna k'asa tace,. "Barka da yini Inna"

Mama Hajiyar ta d'agota tana dariyar yak'e tace,. "Barka dai 'yata sannunki da zuwa to mu shiga daga ciki"
Chapter 25 · 0% Book details