← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 177

Sashe 99

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 4 Kamin yaron daya aika ya dawo Aliyu ya shiga ciki yayi wanka ya canja tufafi sannan ya dauki wayarsa ya kira Mama Barakat ya tambaya ko tana gida. "Eh ina gida Aliyu ko ka shigo garin ne?" "Eh na shigo kuma yau nake son na shigo gurinki saboda ina son komawa gobe kin san aikin na mu babu daga kafa" "Haka ne to sai ka shigo" Ya sauke kiran sannan ya fito falo yayi sallah yana sallamewa aka yi knocking, knocking din da ya tashi Fatima ta farka idonta har sun yi ja tsabar bachi, Aliyu ya karba ya rufe kofar. "Yaushe muka zo nan?" "Kina bachi little princess" Ta yi mika "Kai ka dauko ni?" Ya risina inda take zaune yana kallonta da murmushi a fuskarsa. "Eh kin tashi lafiya?" Ta kalli falon. "Nan gidanka ne?" Ya daga mata kai. "Ashe kana da wani gida Vito ma gida biyu yake da shi" "Good taso ki wanke baki ki yi wanka sai ki ci abinci ki yi sallah" Ta kalli shaddar dake jikinsa. "Kai ka yi?" "Eh" Ya kama hannunta suka sauka tana fada masa kanta na ciwo, ya shiga da ita dakinsa ya nuna mata bandaki da yadda zata yi komai sannan ya fito ya dawo falon ya zauna yana taba wayarsa, har a lokacin sai da ya gwada kiran Number Emily ya ji ta a kashe. Yana ta nazarin abun da zai saka ta kashe wayarta kuma ta dauki lokaci har haka bata kira ba bayan sakon da ya tura mata, duniyar tunani ta dauko shi daga can bangaren Emily zuwa na Turhan idan ya ce be ji tausayin abokinsa ba yayi karya, ya san da zarar Emily ta bayyana a rayuwarsa komai zai zame masa daidai, sai dai kalamansa na dazun cewar da laifin Emily na amincewa ta aure shi ya sanyaya masa guiwa, jikinsa kuma yana ba shi cewar Emily ta yi gaskiya ko Ammy ta san da Fatima a matsayin jikarta abu ne mai wahala ta bar mata ita balle kuma Turhan, hakan ya saka shi ya ji lallai ya kamata ya bar garin Kaduna gobe gudun kar makamancin abun da ya faru a Airport ya sake faruwa, gashi kuma yana son ya san halin da Emily take ciki domin rashin samun wayarta da kuma maido masa da amsar sakonta ya saka shi a damuwa. A tare suka ci abincin da Fatima tana ta fada masa mafarkin da ta yi, ya rigata koshi a dole ya jira sai da ta koshi ita ma sannan ya kwashe kayan ta bishi Kitchen tana kallo komai ta gani sai ta taba ta tambaya, ko ta fadi Momy na irinsa. "Fatima Zaki iya zama a gidan nan ke kadai naje wani guri na dawo?" Ta lake kafada "Aa ba zan zauna nan ba, sai dai mu tafi tare" "Ba zan dade ba kuma zan iya bar miki wayata ki yi game ki yi kallo" "Duka na kalli komai na cikin wayar ni bana son zama" Ya rasa ta ina zai fara rarrashinta ta zauna domin baya son tafiya da ita gidansu Kameela, na farko dai yana ganin hakan kamar cin fuska ne ga Kameela na biyu kuma iyayenta ma ba lallai su fahimce shi ba domin ko kowa be gane yar waye ba Kameela zata gane kuma karamin aikinta ne ta fallasa shi a gabansu. Ya mika mata dayar wayar da ita ya fi aiki da ita ya dauki wanda ya bata dazun ya saka aljihunsa. "Wannan baki san me ke ciki ba, na kunna data zaki iya duba duk abun da kike so a YouTube ki kalli cartoon kuma ki sauke duk game da kike so, Momy ki na na san zata kira ta wannan wayar idan ta kira sai ku yi magana kamin na dawo?" Ya karba ba dan ranta ya so ba, can ta kalli hotonsa dana Kameela dake makalle a falon. "Waye wannan?" "Matata ce" Aiko take ta hade girar kasa da ta sama ya nukokoce kai. "Ba zan zauna ba, so you have a wife" "Yes Baby" "I hate you" Yayi murmushi "I know I'm sorry, Bari na tafi na siyo miki chocolate da ice cream kinji?" Sam ta ki yarda gaba daya mood dinta ya canja daya fada mata yana da mata, ita a tunaninta idan suka saba da shi zata iya dawowa gidansa ita da Emily su bar gidan Vito, amman tun da har yana da mata ai ba wannan damar. "She's ugly" "No she's not" Ya amsa yana dariya. "I want my momy" "Bari na tafi na dawo sai na kaiki gurinta" Daker ya samu ta yarda ta zauna sannan ya dauki dayan key din motarsa ya fice, daga gidan be zame ko'ina sai family house din su Kameela, a bangaren Mama Barakat ya faka ya fito yana tunanin ya kamata ace ya riko musu wani abu, gashi babu enough cash a aljihunsa, sai dai kuma babu yadda ya iya domin ya riga ya zo dama ace be zo ba ne sai ya tsaya ya nema. Haka dai ya aje komai ya shiga bangaren da sallama, yaranta suka amsa masa suka gaishe shi sannan suka kawo masa drink da abincin, suka fice daga falon cike da tarbiya, babu jimawa Mama Barakat ta sauko sanye da wani lace mai tsada irin na su na yarbawa domin zama a cikin hausawa da kuma auren bahaushe be saka ta jefar da al'adarta ba, yaranta ma yawanci da yaren yarbanci take musu magana shiyasa duk sun iya yaren. "Maraba maraba da Aliyu" Ya sauka daga kan kujera ya zauna kasa saboda ta zauna akan kujerar. "Haba zaunawarka mana" "Aa nan ma ya wadatar, na same ku lafiya" "Lafiya Kalau Alhamdulillah, ya hanya" "Alhamdulillah" "Maa Shaa Allah baka ci komai ba?" "Already sai da na ci abinci na fito" "Tohm, ina godiya dai Aliyu daka saurare ni kuma ka ni umarnina a matsayina na step mother din Kameela, hakan ya nuna kai yaro ne mai jin magana mai biyayya kuma mai tarbiya, na jidadi sosai Allah ya maka albarka" "Ameen" "ka shiga bangaren na su ne?" "Aa na fara zuwa nan ne tukuna" "To yayi kyau, da har jiya nake cewa ina son na sake kiranka, domin Kameela gaba daya ta fara fita hayyacinta abincin kirki bata iya ci, yarinyar nan tana sonka kai ma kuma na san kana son matarka, ni ban san me yake shiga tsakaninku kuke ta samun matsala ba" "Kameela ta cika kishi ne, da abun da ya kai da wanda be kai ba duk na kishi ne a gurinta, bata tsayawa ta saurara kuma bata amfani da tunani kamin ta aikata abu, amman dai In Shaa Allahu ba za a sake jin kam mu ba" "Hakan yayi kyau domin na tabbatar ita ma kanta a yanzu ta dauki darasi kuma zata gyara" "Allah yasa" "Ameen" Mama Barakat ta ji kamar ta masa maganar Emily sai kuma ta ji rashin dacewar hakan, domin be kamata ta shiga tsabgar rayuwarsa ba, bayan kuma ta fada masa Kameela bata fada musu komai ba, sai kawai ta sauke numfashi ta ce. "Tashi ka tafi, ka yi hakuri da duk abun da zaka ji ko ka gani gurin Hajiya, kasan ita uwa dole ta nuna bacin rai idan aka taba mata ya, balle ma Kameela bata fada mana dalilin dawowarta gida ba, amman dai duk yadda zaka yi ka yi iya kokarinka ka tafi da matarka, Allah ya kawar da fitina a tsakaninku" "Ameen na gode Mama, tafiyar ta zama ta gaggawa ban riko komai ba, sai dai idan na koma In Shaa Allahu" "Haba ina ce ai an zama daya, idan zaka zo gida sai ace dole sai ka riko wani abu? Yanzu ai mun zama iyayenka ba surukai ba, saurarena da kai yi kawai ka bi shawarata Wallahi ya fi duk wani abu da zaka ba ni na gode" Yayi mata sallama ya tashi ya fice ta bishi ta kallon burgewa tana jin ina ma ace daya daga cikin yayanta yake aure yadda yake da biyayya da jin magana haka. Motarsa ya shiga ya yi mata key yayi reverse ya shiga bangaren mahaifiyar Kameela yana faka motarsa tana fitowa tare da kanwar Kameela cikin shirinta da alama fita zata yi, Aliyu ya fito mota ya nufo inda suke sai Hajiya ta yi kamar bata ga Aliyu, sallamar da yayi ma kanwar ce ta amsa masa shi ma cikin rainin wayo domin basa kallonsa da daraja gaba daya, ya mika mata gaisuwa bata amsa ba sai kokarin shiga mota take. "Hajiya Gurinki na zo" Ya dago ta kalleshi a wulakantacce kai kace ba shi da gata ko kuma dan talakawa ne. "Ina jinka?" Ya danna tafarfasar da zuciyarsa ke yi. "Na zo ne akan maganar Kameela" "Ina jinka bani da lokacin batawa fa fita zan yi, kuma saboda kai ka san ba zan fasa fitar da zan yi ba" Ya hade yawu zuciyarsa na bugawa da karfi. "Ina son na dauke ta mu koma ne" "Kam uban nan" Kanwar ta fada Hajiya kuma sai ta fito motar "Ka dauke ta ku koma saboda a titi ka aureta? Ko kuma an fada maka bata da kowa? Ai ko baranta muka yi aka ba mu ita sadaka ba zaka shigo haka nan kawai ka dauke ta ku tafi ba, kuma ta inda aka hau ice ai ta nan ake sauka, kai karan kanka baka isa ka zo na tsaya tattaunawa da kai akan matsalarku ba, idan ma bikonta za zo toh ba kai ya kamata na gani ba, domin kai ka maida auren kamar wasan yara, haka kawai dan ta maka dadi zaka turo yarinya gidansu, yanzu kuma da ta yi maka dadi ka shigo kana fada min zaka dauke ta ku tafi, ai ba ni na baka aurenta ba ubanta ya baka aurenta kuma shi kansa yanzu yadda ransa ya bace ba lallai ne ya yarda yarsa ta koma inda ba a san darajarta ba, daman can abu ne da Allah ya riga ya tsara babu yadda za'ayi, amman da na san idan ka aureta haka zaka wulakantata kai da iyayenka ba zan yarda Kameela ta aureka ba ko zata mutu" "Iyakar abun da zamu tattauna tsakanina da Kameela ne Hajiya ban
Chapter 99 · 0% Book details