Sashe 176
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 7 Kin dade kina sha awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba? Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na yarki? To, ga sau i ya iso! ADASHE NE NA GATA! Ki zuba ku i, ki auki abin da kike so daga: Sutura da zannuwan gado Kayan kitchen Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu) Talkami da jaka Zanen gado Frames (flowers decoration ko standing ones) Console mirror Boxes na Lefe ko na traveling. Warmers iri-iri Food flask iri daban-daban Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so! i ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa. Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati. Akwai sharudda da ka idoji. Domin arin bayani, ki/ka tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660 Ko ta hanyar WhatsApp Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1 Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t Thank you Daga London zuwa Edinburgh/Glasgow kusan 1 hour flight ne. Jimilla tafiyar ta zame musu ta 10 - 12 hours bisa layin jirgin da suka bi. Scottish, Scotland tana cikin United Kingdom (UK) ne, arewacin Ingila take. Tana da manyan birane kamar Edinburgh (babban birni), Glasgow, Aberdeen, Dundee. Yanayin can yawanci sanyi ne sosai, musamman lokacin hunturu (November March), akwai ruwan sama da iska mai arfi, balle kuma yanzu da yake January. Shiyasa suna sauka filing jirgin Edinburgh Airport (EDI) dake garin Edinburgh, Aliyu ya rufe matarsa da rigar sanyi da ya riko mata, dan kam tun a jirgi yayi masa tanadi daman shi yake kula da abunsa.. Tun da suka sauka kasar Emily ta tabbatar sun zo garin yan'uwanta domin yawan mutane kasar kowa zaka gani jan gashi ne irin nata, tana ta kallon manyan gine ginen da kawar gari ta zo inda bata sani ba. New Town, wata sabuwar unguwa ce da mai taxi ya kaisu bayan Dr A-B Ya Fada masa domin a unguwar mahaifinsu yake. Aliyu ya fara fita motar yana rike da Abulkhary dake bachi sannan ya bude mata ta fito tana kallon gaban gidan da suka tsaya wanda tsarinsa ya sha banban da na mu na hausawa. Karamin gate ne ba mai tsawo sosai ba an saka flower gefe gefen na gida ga haske normal ba. Gidan sama ne mai fadi amman ba mai ado da lankwashe lankwashe kamar na mu ba. Aliyu ya tsaya a gabanta ya saka hannunsa daya ya gyara mata fuskarta,.ya cire mata hullar kanta gashinta ya bayyana sai ya baza mata gashin ko'ina, sannan ya rika hannunta suka nufi kofar shiga gidan. Dr A-B ne a gaba tare da matarsa Emily tana daga baya tare da Aliyu. Door bell ya taba sannan ya kara fuskar sa gaban ring camera yayi magana kasancewar sun shigo da dare ne a lokacin da sawu ya fara daukewa. Wata kyakkyawar matashiyar yarinya ce ta fara bude kofar tana ganin Dr A-B ta saka ihu ta rumgume shi shi ma ya rumgumeta yana murmushi. Aliyu ya kara matse hannun Emily take hannunsa domin ya lura fargaba ta cikata ta ko'ina. Da suka shiga ciki kowa kallon Emily yake saboda an labarta musu ita tun kamin ta zo, kuma sun ga zahiri domin bata rage komai daga kammanin mutumen dake tsaye gabanta yana kallonta ba. "Dad wannan ce Emily yarka, Emily wannan shi ne mahaifinki" Ya dade yana kallonta kamar ya rasa abun yi, bata bar komai daga kammaninsa ba, shi kasan da ya ganta sai da yayi rabin mutuwar tsaye, domin duk yayansa babu wanda yake kama da shi sosai da sosai kamar yadda ita take yi. ita ma tana ta kallonsa sai hawaye take. "Dare yayi ya kamata kowa ya kwanta gobe za mu yi abun da ya kamata domin tabbatarwa" "Dad baka ga kamammi ba?" "Kammanin kawai ba su isa su wadatar ba ya kamata mu bi ka'idodi" Kamar wanda be san taya zai karbe ta ba, haka ya tarbe ta sai duk kuzarinta ya gushe. Sai dai Aliyu da Dr A-B sun kafarara mata guiwa, a dokar kasar be isa ya amsa cewar shi ne mahaifinta kai tsaye ba ta hanyar kammani ko sheidu sai da takardun shedai gwajin jini kuma sai ya zama tana bin sunansa ne. Emily ta kwana da tunani, washe gari da suka hadu teburin cin abinci sai ta lura babu mahaifinta a gurin sai yan'uwnta maza biyu da mace biyu da kuma matarsa da tun jiya suke rigima saboda abun da ya aikata shekaru da yawa da suka wuce. Kusan kowa be saki jiki da ita a gidan ba, saboda dokar bata tabbatar ba, har sai da suja tafi Asibiti aka yi musu gwajin kwayoyin halitta ita da mutumen da take ikirarin anta ne results din ya fito at 98% sannan mahaifinta ya yarda. Tana zaune wajen asibitin ita da Aliyu dake rike da hannunta ta dora kanta a kafadarsa. Mahaifinta ya fito daga cikin asibitin yana rike da takardun gwajin. Emily na ganinsa ya mike tsaye tana kallonsa ya nufo inda yake with so much emotional tana jiran ya fada mata results din dake hannunsa sai ta ga kawai ya rumgumeta. Aliyu ya sauke sanyayar ajiyar zuciya yana murmushi tare da yi ma Allah godiya. Shi kansa abun da ya faru jiya ya ba shi tsoro. Ya dagota daga jikinsa ya duba fuskarta ya taba ya sake maida ita jikinsa. "Na san kin zo da tari tambayoyi da suka bukatar amsa.." Ya sunbance saman kanta. "No na riga na san amsar komai, na san duk abum da na ke son sani, komai ya faru ne ba da son ran kowa ba" "Yeah ki yafe min, da ace na san tana dauke da cikinki ba zan juya baya ba, dukan mu muna kuskure na yi kuskure na sani I'm sorry" Emily ta rike hannayensa. "Mu daina tuna baya, na zo nan ne saboda samun karin farinciki da kuma sanin asalina, ba amfanin tuna abun da ya wuce" Ta juya ta nuna Aliyu. "Wannan mijina ne, wannan kuma yarona" Ya mikawa Aliyu hannu suka gaisawa, da ya tara hannu zai karbi Abulkhary sai yaki zuwa saboda kewa yake yi baya yarda da kowa sai iyayensa. Duk yadda Dr A-B zai yi ya fahimtar da Step Mom dinsa mahaifinsa ya aikata kuskure kuma yayi nadama sai da yayi, domin a gurinsu kamin abu ne ta maka shi a kotu ta nemi a raba auren, kuma a raba har ma da ganimar daukar dukiyarsa a damka mata kuma a bata ragamar yayanta. Ta inda ta saurara masa be aikata hakan a lokacin da yake aurenta ba. Ya aikata ne kamin ya hadu da ita. Sam ita kam baya yarda ta karbi Emily ba, sai ya zama ma. Kamar tana kishinta saboda Emily ta fi kama da mahaifinta fiye da yayanta, ga shakuwa da ta shiga tsakaninsu na dan zaman da ta yi a gidan, yaran ma sun sake jiki maza da mata amman ita bata yarda da Emily ba. Mahaifinta ya kaita gurare da yawa, ya nuna mata abubuwa wasu daga tarihinsu wasu kuma daga tarihin garin. Mutumen mai kaunar karensa sosai duk inda yaje yana tafiya da su domin rakiya, tun tana tsoro har ta daina. Wata rana da ya tafi da ita gurin da yake kamun kifi ne yake tambaya labarin Mama Baraka, ta fada masa kuma ta labarta masa yadda abubuwa suka faru da ita. Ya tausaya mata matuka, ta nuna masa hoton Fatima a wayarta. Honeymoon din da Aliyu be samu tafiya yayi da matarsa ba lokacin da suka yi aure shi yayi da ita a nan. Ya jata sun shiga gari sun yi yawa har makotan garin sun ziyarci gurare dabam dabam. Sati daya ta yi a gidan ya dauke matarsa suka tafi yawon amarci. Dr A-B daga can wata kasar ya bulla. Mahaifinta ya saka ta gaba suka tafi aka ayi komai a rubuce da ka'ida cewar shi ne mahaifinta a doka. Da za su tafi Emily ta yi kuka sosai tana ta kewar mahaifinta, ta rumgumi yan'uwanta ta yi musu bankwana tare da jaddda musu za ta dawo a duk lokacin da ta bukaci haka. ya rumgume yarsa ya saka mata wata sarka tashi mai tarihi ya dauko kudi mai yawa ya bawa Emily amman bata karba daman bata zo domin kudinsa ba sai dan ta san waye ubanta shi ma kuma ya san wacece ita, amman ta karbi kyautar agogo da hotuna da yayi mata... Karfe bakwai na safe suka bar kasar ita da Aliyu, sai da suka sake daukar awanin da suka dauka da farko sannan jirginsu ya isa Nigeria suka sauka da dare saboda awaninin ba daya ba. Ummi ta aika da mota aka dauko su daga Airport, zuwa gidan inda suka samu tarba ta musamman. Washe gari suka sha hira da Ummi na abubuwan da suka faru da kuma yanayin garin da guraren da suka ziyarta, hotunan da suka dauka da sauransu. Satinsu daya Abuja sannan suka dawo Kaduna, rayuwa ta cigaba kamar yadda aka saba. Da Fatima ta yi arba da hotunan da aka dauka a wayar Emily ta sha kuka sosai ba a tafi da ita, Emily ta mata alkawarin idan zata koma da ita zata tafi. Har a lokacin Ammy bata yarda Fatima ta zauna a hannun Emily sai dai ta rika zuwa tana dawowa, sai kuma idan fitsarar Fatima ya tashi ta nace sai ta kwana a gidan. Emily na yaye Abulkhary Aliyu ya biya mata Ummara ta tafi tare da Fatima da shi, da Abulkhary, a can suka yi sallah karama ba su dawo na sai bayan Sallah. Da lokacin hajji yayi kuma ya cika mata kawarin da ya daukar mata tun tana da cikin ansa. Ita kadai ta tafi ta yi hajji ba da shi ba saboda yanayin aikinsa. TURHAN POV. A shekarar da Emily ta tafi hajji a shekarar Turhan ya yafi, shi da matarsa sai dai har kowa yai ibadarsa ya gama be hadu da dan'uwansa ba saboda jirginsa kasar da masaukin kowa dabam. Turhan yana zaune yana waya da Fatima yana fada mata abubuwan da ya tara mata a dakinta dake gidan. Matarsa ta