← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 177

Sashe 119

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

gidan bata fito ba. Ummi ta kunna wutar dakin ta kalleta. "Kin tashi lafiya Emily?" Ta tashi zaune. "Good Morning" Ummi ta karasa kusa da ita ta zauna tana kallonta da murmushi. "Kin tashi lafiya?" Ta daga kai kawai tana boye idonta. "Za a kawo miki abun karyawa, asibiti na kwana gurin Aliyu na manta ban fada miki ba, and Aliyu ya bawa Khaleefa hutu saboda ki samu sakewa, zaki iya fitowa harabar gidan ko falo ki shakata, kuma ki saka tufafin da ya miki ki sake jikinki babu wani damuwa" Nan ma ta daga kai. Ummi ta mike tsaye ta fice daga dakin. Sauka ta yi kan gadon ta shiga bandaki ta yi fitsari ta wanke da ruwa domin ta kasa daina wannan dabi'ar ta musulmai wato tsarki da ruwa ko wanke bayan gida da ruwa, ta wanke bakinta ta fito ta tana jin sanyi na abun da Aliyu yayi mata, ya fahimci feeling dinta tun bata fada masa ba, domin babu fuskokin data tsana a duniyar a yanzu kamar ta Turhan da Khaleefa. Ta zauna saman gadon ta kai hannunta ta dauki katin DR A-B data tsinta a jacket dinsa, ta dadde rike da katin tana kallonsa kamin ta dauki wayarta ta saka number shi duka biyun, sannan ta shiga gallery ta kama hotunan Fatima tana kallo sai ga kiran Aliyu ya shigo wayarta. Ta amaa da sauri tana fatan dayan wayarsa ce dakw hannun Fatima aka kira da ita so that ta yi magana da yarta. Tana jin sallama da muryar Aliyu ta san ba yarta ba ce. Bata amsa sallamar ba bata ce masa komai ba kuma bata amsa Good morning da yace mata ba, hakan ya saka shi fahimtar kuka take ko kuma fushi take da shi. "Idan akwai abun da kike son aikawa ki aikata, karki bar tunaninki ya hana zuciyarki abun da take so" "Ina son yarinyarta a kusa da ni, i want my baby" Ta fada tana fashewa da kuka. Aliyu be ce komai ba ya kashe wayar. Kiransa na sauka kiran Vito ya shigo wayarta cikin kuka ta amsa kiran shi ma bata ce masa komai ba sai saurarensa take. "Kalle ki Emily, kin yi yaudara kina tunanin kin yi nasara ko? Saboda zuciyarki na raya miki ba zan iya miki komai ba? Mamana ta yi gaskiya kin din ba abar yarda ba ce, idan kina tunanin kin gudu kin tsira to kin yi kuskure, ba'acin amanata a zauna lafiya, sai na ga bayan wannan dan iskan yaron da kike so, kuma sai na maida rayuwarki labari Emily, ba zan raine ki wani ya ci moriyarki ba, no way! Daman kina nemam damar butulce min ne, shiyasa kika karbar soyayyata bayan duk abin da na yi miki? Ban ga laifin komai da yake faruwa da ke ba, saboda ke yar iska ce fuck you Emily" Maganar yake cikin yanayi na maye. Ta hade kukanta tana jin tausayinsa domin abu ne data sani Vito yana sonta, kuma ya kula da ita irin kulawar da kowa be bata ba, ba al'adarshi ba ce shan kayan maye da safe sai idan yana cikin damuwa, and she knows ita ce silar damuwar tun da har ya kira yana karanta mata wannan bayanan. "Zan dawo Vito, zan karbi yata zan dawo zamu yi aure zamu irin rayuwar da kake son mu yi, kai kadai ne nauyin da ya rage min na sauke, but don't hurt anyone mutumen da kake kokarin ganin bayansa taimako kawai yayi bashi da wata manufa akaina, ba abun da kake tunani ba ne" "I don't need you now, i already have Chidimma na yi replace dinki da ita, daman daga ke sai ita nw kuka san sirrina, dan haka zata kasance da ni har abada ke kuma zan baki mamaki, daman haka kike ko? Su ma butulci kika musu shiyasa suka horar dake, to ni horon da zan miki ya fi na su, a hannuna kike ina kallon duk wani motsi naki" Ya katse wayar sai ta lumshe ido ta cije baki tana jin ba zata iya yafewa kanta ba, domin ta san yadda cutarwa take da ciwo and kasa samun soyayyarta da Vito yayi bayan duk taimakon da yayi mata ya zama kamar cutarwa. Ta kai hannu ta taba zuciyarta tana jin kamar ace zata iya cusawa kanta kaunarsa kai tsaye, tun bayan da Khaleefa ya ci amanar ta bata sake jin tana son wani da namiji ba, Turhan ma ta aure shi ne kawai saboda mahaifiyarsa ba dan tana son shi ba. Sai da ta fara raya ma kanta cewar zata cusa zuciyarta ko bata so ta amince da soyayyar Vito, ko dan rama masa alherin da yayi mata, be zama lallai sai tana son shi ba, zata iya zama da shi su rayu yadda yake so, sai kuma maganar Ummi ta fado mata arai. "Kina fifita farincikin wasu akan naki, kina fargaba tunkarar wasu da abun da yake zuciyarki, shiyasa kika cutar da kanki...karki sake tsorata ko cilasta kanki abun da ba shi kike bukata ba..." Ta bude ido tana ba kanta amsa zuciyarta kuma na raya mata Idan bata amince da soyayyarta ba zai iya cutar da Aliyu. "But i have to Vito ya cancanci komai daga gareni" Ta share hawayenta sakamakon turo kofar dakin da aka yi za'a shigo. Mama Baraka ce da lullubinta dauke da katon kwandon abinci yaranta yan mata biyu ma suna dauke da abinci, ta shigo da far'arta ta aje abincin a kasa suma suka duka suka aje Emily sai kallonsu take su ma suna kallonta, Mama Barakat ta zauna a bakin gadon tana kallon Emily. "Ina kwana, kin tashi lafiya" Emily bata amsa ba, duk kuwa da tana tunanin ko Ummi ce ta ce ta shigo mata da abincin. Mama Barakat bata damu ba ta gabatar mata da yaranta biyu. "Kin ga bakuwar fuska ko? Wannan sunanta Misira, wannan kuma Hakima zaki iya kiransu da kawayenki ko kanenki" Emily ta watsa mata harara. "Bana son ganinki ba na fada miki ba? Duk wani abu mai alaka da Kameela bana bukatarsa" Mama Barakat ta girgiza kai da sauri. "Aa Wallahi zuwana ba shi da alaka da Kameela ba wai ina kokarin gyara abun da Kameela ta bata ba ne, Kameela yar kishiya ta ce kawai bayan wannan babu wata alaka, dan Allah ki yarda da ni" "Ku ba abun yarda ba ne, ku fita daki nan" Mama Barakat ta fara hawaye tana bude abincin da suka zo da shi. "Dan Allah karki tsaurara ganinki da nake ina jin sanyi, kin ga abubuwa na shirya miki na karyawa ban san wanene favorite dinki ba, amman abubuwa sun kai bakwai a nan ki ci duk wanda kike so, jiya kuma na yi waya da ita mahaifiyar yaron da suka rike miki Fatima, da na ce zan je na same ta sai kuma na ga ba zan iya yakin ni kadai ba, dole sai da taimakon mai gidan sai na yanke shawarar na fada masa, kuma na fada masa sai dai ban yi nasara na samun amincewarsa ba, be ma fahimce ni ba, amman... Amman... Dai na san zan samu kansa" Mama Barakat tana maganar jikinta na rawa kamar wanda aka turke, iya kar kokarin na fahimtar da Emily ne bata nufin cutar da ita. Cikin daga murya Emily ta dagawa Mama Barakat tsawa domin ta fahimci so take ta shiga jikinta ta cutar da ita, bata san me suke kullawa ita da Kameela ba. "I don't need your help, bana bukatar abincikin Bana bukatar komai daga gareki, ki fita ki bar nan i don't need you" Babbar yarta ce misira ta kasa jure yadda Emily take magana da mahaifiyarsu ne ta daka ma Emily tsawa. "Ke dan Allah wace irin mace ce, baki san darajar iyaye ba ne da zaki rika cin mutuncin mahaifiyarmu a gaban idonmu? Haba Mama Wacece wannan kika ta rawar jiki da ita ne, duk girkin nan da kika tashi kina yi tun asuba duk saboda wannan banzar ne?" Misira na rufe baki Mama Baraka ta dauke ta da mari ta nuna mata kofa. "Fita fita ki ba ni guri" Misira ta kalli Mama Barakat da mamaki dafe da kumatu. [7/16, 10:07 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy ABOKIN RAYUWA
Chapter 119 · 0% Book details