← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 177

Sashe 132

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fada ko na nuna ba abun yana a zuciya" Sarkin yayi shiru na tsawon lokaci kamin ya ce "Karka manta da asalinka, kar ka bari mahaifiyarka ta saka maka kalmomi marasa amfani a kanka" "Ba zan taba mantawa da asalina ba, ni dan wata mace bakar fata ne daga arewacin Nigeria, kuma dan Sarkin Sudan balarabe mai asali, Mahaifinta bata saka min kalmomin manta asalina ba, amman ta fada min yadda mahaifina ya mu'amalance ta, wanda ya sha banban da yan'uwana da nake gani a Masarautar, kuma laifinta shi ne ita bakar fata ce kawai. Bana son yata ta tsane ni, ko kuma ta kalleni da laifin dana aikata saboda son zuciya shiyasa ba zan ki mahaifiyarta ba, mahaifiyata ta cancanci girmamawata a kowane irin hali, duk uwar da zata dauki cikin danta ta raine shi ta haife shi ko wace uwa ce ta cancanci biyayya daga gurin anta" Sarki Mohamed Abdou ya dauke kai kamar mai jin kunyar Turhan, kuma ya gagara bayyana bacin ransa. "Mahaifita ta dandani daci mai tsananin kashe halshe daga gurin mahaifina, a yanzu kuma da anta ya kawo sai take ganin ta cancani kauna da biyayya, da kowace dakika tsoron rasani take, ni ma kuma ina fargabar rasata saboda ciwon dake neman rayuwarta, Ya shugaba kuma mahaifina tambaya ce mai nauyi na amsa cewa ina da muhimmanci a gareka ko akasin haka, saboda na zama farin tuwo daga bakar tukunya, be zama lallai ka kaunaci abun da nake kauna ba, saboda ni ba Laraba ce ta haife ni ba, amman dai bakar matar nan daga arewacin Nigeria tana da matukar muhimmanci da kima a idona, ina kyautata zaton ba zaka hana ni yi mata biyayya ba, domin Annabi S. A. W ma ya ambaci uwa sau uku sannan ya ambaci uba, saboda muhimmancinta" Mahaifinsa ya kalleshi, hawaye ne suke saukowa a fuskar Turhan ba na wasa ba. "Idan an yi min izinin ina son na kama hanyar komawa gobe, kuma zan dawo ne kadai idan mahaifiyata ta samu farinciki da ta dade tana nema, kuma na samu matar da ita kadai nake muradi a yanzu" Ya risina cike da biyayya. "A gafarci halshena idan yayi kure, na barka lafiya" Ya mike tsaye ya share hawayensa ya fice daga fadar. Masarautar ya bari gaba daya, ya tafi gurin abokansa da ya nunawa Fatima a waya tun a kamin ya karaso, biyu suka goya masa bayan dawowa da Aisha dayan kuma ya nuna masa ya karbi yarsa kawai ya barta ta yi tafiyarta tun da har ta nuna bata bukatarsa. Ya dawo gidan ya shiga bangarensa sai ya samu an gyara komai an kwashe duk wani abu daya fashe, wasu abubuwan kuma an maida su a muhalinsu. Ya shiga dakin da matarsa ta fi zama ya zauna a kujerarta sai tunani yake kala kala can kuma ya mike tsaye ya fito daga dakin ya shiga dakin da komai nasa yake ciki, yana kokarin cire rawanin kansa ya hango wani karamin kwali a kan gadonsa, ya karasa kusa da gadon ya dauki kwalin ya bude. Sai yayi arba da ticket din first class na jirgin da zai tashi daga Khartoum zuwa Abuja a gobe, ga kuma manyan kudi mai kauri a ciki da wata yar karamar takarda. "Rihla sa da, Allah yisahil tareeqak" (Safe journey, may Allah ease your way) ib al-Jal la Mohammed Abdou_ Turhan ya kai zaune da jallabiyar dake jikinsa yana murmushi, ya dade zaune yana sake karanta kalmar da ba zata canja daga haruffa ko ma'anarta ba, sake shiri yayi sannan ya fita zuwa bangaren mahaifinsa sai ya samu an shirya liyafar abincin dare da yaran da suke gidan ya zauna aka ci abincin tare da shi, bayan an gama ya shiga bangaren mahaifinsa duk yadda ya so ya samu wata dama ya yi kibabbantacciyar magana da mahaifinsa be samu dama ba, domin mahaifinsa be ba shi wannan damar ba. Daya fito sai ya dauki motarsa ya tafi gidan iyayen matarsa ita ma dai be samu ganinta ba domin ko kofar gate di gidan ba a bar shi ya shiga ba. Da ya dawo sai ya hada kayansa da abubuwan bukatunsa tsab cikin akwai har biyu sannan ya kwanta, washe gari da wuri Khadima ta kawo masa abun karyawa ya karya yana video call da Fatima saboda ta fitini Ammy da kukan rashin Turhan da Emily a kusa, sannan yayi wanka ya shirya ya sake kiranta video call be kashe kiran sai da suka shiga jirgi aka umarci kowa ya saka maka wayarsa a airplane mode. AMMY POV. "Jirgin nan zai zo?" "Eh" Ammy ta amsa mata tana shafa kanta. "Zai tafi biya ya dauko Momy ne? I miss her so much" "Aa Momy sai idan ta huta zata zo" "When?" "Ban sani ba tukuna, amman a yanzu idan ana son ganin mahaifiyarki ko kuma a daukota a ina kike tunanin za a same ta sanyin idaniyata?" "A waya" "Bayan waya" "Gidan gurin Uncle Aliyu, ko Vito" "Aliyu yana ajeta a gidansa ne? Da kuka zo garin nan a gidansa kuke zaune?" "Aa" "To da kuna PH ma a gidansa kuke zaune?" "Aa a gidan Vito ne, shi yana dukan Momy ne shiyasa bana son shi, kuma baya so na yana hade rai" "Shi Viton Momynki ta aure shi ne?" "Aa ba zata aure shi ba, ba zamu koma gidan ba, za mu zauna a nan da daddyna ko? Da Momy ko?" "Haka muke fata" Fatima ta mika mata wayar da har yanzu bata san yadda zata sarrafata ta kira ba, amman ta iya shiga YouTube da Gallery ko Camera. "Zaki iya kiran Momy? Ita ma zan yi magana da ita" Ammy ta karbi wayar ta shiga gurin kira ta gwada kiran Layin Aisha da sunan da Aliyu ya saka mata a wayar wato Emily, sai ta ji wayar a rufe. "Ba a samu" "Sake kira" Ta sake gwadawa" "It the same thing" "To kira Uncle Aliyu ki ce ya bawa Momy" "Basa tare, kin san a ina za a iya samunta?" Ta yi shiru can kuma ta ce gurin Vito. Ammy ta yi shiru tana nazari. "Amman Momy ma zata dawo? Ina son na ganta?" "Zata dawo Fatima" Ammy ta amsa mata sannan ta sauke ajiyar zuciya. KAMEELA POV. Ta shiga bangarensu da mamaki tun a falo ta labarta musu komai, sai Hajiyarsu taja tsaki. "Aikin kenan, daga Aliyu sai abun da ya shafi Aliyu" Anty Shafa ta kalli Mahaifiyarsu. "Hajiya, abun be baki mamaki ba?" "Miye abun mamaki a ciki? Wata kila ta fadi hakan ne saboda Kameela ta daina zuwa can, daman idan ba neman suna ba yaushe zaka kashi sirrinka ka fadawa kishiyar uwa?" Kameela ta ce. "Ba wai ta fada ne kawai saboda na daina zuwa mata da maganar ba ne, domin na ga tsananin bacin rai a tare da ita, har fa marina ta yi, kuma idon ta ya kumbura kamar ta yi kuka" Can kuma ta juyo har lokacin tana dafe da kuncinta. "To kuma ma idan ba tsananin bala'i ba ta ina Mama Baraka zata zama mahaifiyar tsinaniyar Emily nan? Ta ya ta ina? Kwata kwata ma basa kama fa, kuma ita Emilyn nan ma fa ruwan turawa ne da ita, fara ce sosai mai jan gashi da blue eyes, amman dai ga dukanin alama akwai wata a kasa" Hajiya ta tabe. "Ita fa kishiya ba yar'uwa ba ce, ba mamaki wani abun ta shirya, amman dai anjima idan Alhaji ya dawo, zan kwankwasa kofar na ji ko zata yi kara" Kameela ta haura sama ta shiga dakinta da mamaki da kuma tsananin kishin ace Emily yar Mama Barakat ce, idan har wannan abun da hankali ba zai dauka ba ya tabbata ai ita kam an gama da ita gamawa ta musamman. "Kai ba ma gaskiya ba ne, ai ba hadi hanyar jirgi dabam mota dabam" Ta zauna cike da kewar mijinta da son sanin halin da yake ciki. Wayarta ta dauka zata gwada kiransa sai wani bangare na zuciyarta ya hana ta yi haka sau hudu sai a biyar ta gwada kiransa, wayar na shiga gabanta ya fadi ta mike tsaye tana safa da marwa a dakin, wayar ta katse be daga ba, ta sake gwadawa be daga ba daga karshe sai yayi rejecting kiranta. Ta zauna baki gado tana hawaye domin tana tsananin kaunar mijinta. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [7/29, 10:20 PM] : https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t ABOKIN RAYUWA
Chapter 132 · 0% Book details