Sashe 84
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kana son shiga sha'anin Emily Aliyu kamar ka manta waye kai, musulmi kuma mai iyal..." Bata karasa ba ya yake wayar ya koma motarsa sai ga kiranta ya biyo, when he pick ya fada mata. "Kar kiran da na yi miki ya baki damar fada min magana, kuma idan kika dame ni zan bata miki rai ne" "Ka yi hakuri, ina camp ne zaka iya zuwa ka dauke ni, sai mu je na dubata" "Ba kai ki zan yi ba, ke zaki je ki dubata, duk abun da ake ciki sai ki fada min" Yana kaiwa nan ya kashe kansa wayar. "Matarka ce? Daman kana da mata?" Fatima ta tambaya tana shan ice cream. "Aa ba matata ba ce" "Toh kana son mata" Ya kalleta kawai yayi murmushi. "Kana son Momyna?" Ya sake yin murmushi. "Fatima zan tafi dake gidana na zauna a can mu huta kamin Momynki ta kira sai na maida ke" "Tohm" Taja motar suka kama hanya, tana ta masa surutu har suka isa gidan, a lokacin da ta fito motar ta kalli gidan ta ga babba ne sai ta ce. "Da zaka yarda sai mu dawo nan gidan tare da Momy da Chidimma, mu bar gidan Vito, ba za mu maka barna ba" Shi dai be ce mata komai ba ya bude motar ya dauko wasu daga cikin kayan da suka siyo ya wuce cikin gidan tana biye shi tana ta masa surutunta da fluent English dinta pure one domin bata iya hausa ba, duk wata magana da ake da ita da halshen turanci ne, hausa kadan ta iya saboda Emily bata damu ta koya mata ba, kuma bata taso a gurin da ake hausar sosai ba, ba kamar Emily ba. TASMIA POV. Da tufafinta na bautar kasa ta tafi gidan Emily fuskarta sanye da mask, bakin gate din aka ajeta, ta sallami mai okada sannan ta buga gate din mai gadin ya leko, sai ta masa karyar Emily ce ta kira ta da kanta tace tana son ganinta. "Idan ka shiga ka fada mata Tasmia tana waje" Mai gadin ya kira wayar Emily ga ji ta a kashe, sai ya shiga ciki ya kwankwansa Chidimma ta bude ya tambaya ko Emily ta san da zuwan wata kawarta, sai ta amsa masa da eh alhali bata da tabbaci. Mai gadin ya koma ya budewa Tasmia ta shigo, da yaren turanci ta tambaye Emily Chidimma ta nuna mata upstairs, har ta nufi saman sai kuma ta juyo ta saka tambayar Chidimma ko Vito yana nan Chidimma tace mata baya gidan sai ta haura sama da sauri jikinta na rawa, na dan tana son faranta ran Aliyu ba da kuma yi ma kanta yaki, da babu abin da zai saka ta risking rayuwarta a gidan Emily, kiranta kawai da Aliyu yayi a karan kansa ya faranta mata rai balle kuma har ya nemi alfarma a gurinta, a ganinta hakan ma wani matakin nasara ne, domin da sannu bako ke zama dan gida. Tsabar rikicewa ma dakin Fatima ta fara shiga, ta fito da sauri ta tura dayar kofar ta leka sannan ta shiga. Sautin kukan Emily ta fara ji kamin ta hango ta kwance a kasa, ta karasa da sauri. "Lafiya me ya same ki?" Ganin Tasmia ya saka Emily ta dan ji sanyi sanyi har ta dago ta jingina jikin Tasmia tana duka tana fada mata Vito ne ya duke ta. Tasmia ta kalli kofa sannan ta rage murya. "Me kika masa?" Emily ta kasa magana sai kuka take. Tasmia ta kalli yadda fuskarta ta yi ja wani gefen ya kumbura ga kuma shatin belt a saman kafadunta, kana gani ka san dukanta aka yi, kuma ko bata fada mata ba, ta sani ba zai wuce ace saboda Aliyu ba, shiyasa shi ma ya damu ya san halin da take ciki. "Wata kila ya gaji da halinki ne Emily ta ina zaki zauna kina wahalar da shi, bayan duk hallacin da yayi min? Ko da yake ban san me ya faru ba, amman kina cin amanar mutumen nan, yana sonki kin kasa fahimta" Emily ta takaita kukan da take ta share hawayenta. "Ya aka yi kika samu shigowa nan?" "Karya na yi ma mai gadi cewar kin san da zuwa, na ce ya zo ya tambaye ki sai yace na shigo kin san da zuwa" "Be shigo nan ba, ban yi magana da shi ba" Mamaki ya cika fuskar Tasmia. "Toh taya ya bar ni na shigo, ni daman dai na zo ne kawai na duba ki" Emily ta yi shiru alamar tunanin sannan tace. "Tashi ki tafi kar Vito ya tarar da ke a nan, ransa a bace yake" Emily na rufe baki Tasmia ta zabura tsaye ko sau anjima bata cewa Emily ba ta fice gidan fuuuu kamar walkiya. Hankali be kwanta ba sai da ta isa gida, sai kuwa aka yi a daidai tana shiga gidan kiran Aliyu na shigowa wayarta domin hankalinsa ya tafi gurin son sanin halin da Emily take ciki. "Hello" Ta amsa da far'arta kamar gaske. "Assalamu Alaikum" "Wa'alaikumussalam" Ta yi shiru tana jiran sai ya tambaye ta. "Lafiya take?" "Lafiya Kalau take na same ta ma girki take yi" "Vito na gidan ko da kika je?" "A A Baya gidan mai aikinta ce kawai shiyasa ban tsaya komai na ina ganin lafiyarta sai na fito, kar ya zo ya tarar da ni a samu matsala, ba dan kai ba a yanzu da babu abun da zai kai ni gidan Emily ko dan gudun fitina" "Me yasa wayarta take a kashe" "Toh ban sani ba, wata kila tana gudun a kira ne yana nan, amman lafiyarta kalau na same ta ma ta sha ado abunta" Idan be ce mata thank you ba ai be kyauta ba ko ba komai ta cancanci godiya domin hankalinsa zai kwnata a yanzu sanin cewar Emily na cikin aminci. "Na gode" "Always Aliyu, ka aje duk wani tunani da kake, ka dauke ni a matsayin kanwarka, bayan shi babu wani ba" Ba tare da ya sake furta komai ba ya kashe wayar. [6/20, 7:25 PM] : https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 ABOKIN RAYUWA