← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 177

Sashe 95

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

zauna da kowa ya watse na goya jaririyata na kama hannun dana na bi ta cikin gidanen dan kar ma wani ya gan ni na gudu na bar unguwar. Tafiyar kuma wani sabon labari ne, domin ba san kowa a inda na tafi ba, haka na kwana a jikin wata tsohuwar gina sauro ya cije ni ya cije yarana musamman Fatima dake ta jaririya a lokacin, a daren ne na rana mata suna Fatima sunan da ba a yanka mata rago ba kamar yadda kuke yi a addinin musulunci, a lokacin akwai son addinin a raina shiyasa na zabi sunan da yake min dadi bayan Aisha, da gari ya waye na barka dankwalina na yi amfani da shi domin pad din ya lalace kuma ba ni da wani, na cigaba da tafiya kafafuwana sun gaji haka nake ta mika su ga danyen jego ga yaro karami idan ya fasa min wani ihu sai na rikice, na daukeshi idan na gaje na aje shi haka dai har na isa wata unguwar marowata domin duk gidan da na shiga na yi roko hakuri ake ba ni wasu kuma su koroni. Yunwa ta ci ni sosai ga tafiya na gaji har na fara ganin jiri, tsakaninkanin kafafuwana ma ciwo nake ji sosai domin ban samu hutu da kulawar daya kamata ba bayan haihuwar da na yi kwana biyu da suka wuce. A haka har na isa kofar wani karamin gida irin na mazan nan da ba su da aure a bude na sallama na sallama na ji shiru sai na taka ciki kadan na jiyo kamshin girki, sai na yi sunsun na dawo baya na koma can bayan gidan dake da wata gona na samu wani guri na raba na kwance Fatima dake bachi yarinya kyakkyawa fara sol na kwantar da ita a gurin na zaunar da London dake ta kukan yunwa na fito na koma wacan gidan dake bude na kara sallama ina sallama ina shiga ciki har na kai inda nake jiyo kamshin a wani karamin Kitchen na duba waiga na ga babu mai ganina na nasa kafata a Kitchen din, sai na yi arba da mutum kwance cikin jini farar vest din dake jikinsa duk ta bace da jini, da sauri na dawo baya ina numfashi daker, na ga tashin hankali kala kala amman ban taba ganin gawa ba sai a ranar, na fito da sauri na falfala da gudu na dawo gurin yarana ina dawowa na samu London yana ihu yana yunwa, ni kaina kuma yunwar nake ji, sai hakan ya saka na manta da tunanin abun da zai biyo baya na sake komawa zuciya na zillo kamar zata fado na shiga Kitchen din na duba ko'ina har na hango karamin gas a kusa da kafar mutumen da ban san ko waye ba, da alama dai girki yake aka kashe shi, na fito na sake leka waje na dawo da sauri na nufi girkin na bude indomie ce har ta fara kamawa na tara hijabina na juye na saki tukunyar na fito a guje ga zafin indomie ga tashin hankali na dawo gurin da yarana suke na cire hijab din gaba daya na aje a gurin na bude indomie na saka hannu ina hurawa ina ci ina bawa London. Ban an kara ba ma ga mutum tsaye a gabana dana daga kai na kalleshi sai na ga fuskarsa babu annuri ga katon Cross a wuyansa, ashe ma ba shi kadai yake ba har da wasu mutun uku. "Miye alakanki da Risk Guy" Ya tambaya cikin hausarsa da bata gama zauna wa a bakinsa ba. "Ban san waye shi ba, ni abinci kawai nake nema" Ashe yayi zaton na ga lokacin da ya aikata kisan kan ne, a take ya nuna Fatima da bindiga. "Jaririya ce, bata san komai ba bata maka komai ba karka dauki alhakinta" Ya maida bindigar a gurin London dake ihun ganin bakuwar fuska. "Ba shi da lafiya, Autism ne kuma be maka komai ba" A take ya dawo da bindigar a kaina. "Idan ka kashe ni yarana ba su da wanda zai rike su ba su da kowa sai ni, ni ma ba ni da kowa sai su, Wallahi ban ga abun da ka aikata ba kuma bazan fadawa kowa ba, abinci kawai naje nema tun jiya rabona da abinci ni da yarona yunwa muke ji, dan Allah ka yi tafiyarka ni ban san waye kai ba, kuma daga nan tafiyata zan yi daman a hanya nake, ina neman mafaka ba ma dan yarana da sai nace maka na shirya mutuwa a yanzu" Ina maganar cikina da muryata suna rawa ina kuka sosai a take Fatima ta farka ta fara kuka ga London yanayi. Ya kalli yaran ya sake kallona sannan ya sauke bindigar ya juya ya tafi, ni kuma na dauki yata na rumgume London a dayar cinyata ina hura abinci ina ba shi ina kuka. Kamin na daga kai sama na kwala wani irin ihu iyakar karfina sai kuma na tashi na goya Fatima da sauri na dauki London na dauki agogon ka Aliyu da nake ta yawo da shi na fita gonar domin na fara hango mutane kar ayi zaton ni na kashe shi alhalin ban ma tana ganinsa ba sai ranar. Na yi nisa da gonar na samu wani ice na zauna a gurin na rumgume yarana ina kuka jikina nata rawa ina fargabar me kuma zai sake faruwa da ni. Ashe mutumen daya tashi kashe ni yana biye da ni saboda yana ganin kamar zan iya tona masa asiri ne, a nan kamar daga sama a sake ganinsa gabana sai ya saka hannunsa ya dago fuskata ya kalleni ni ma na kalleshi sai ya hura min abu a fuska mai kamar farar hoda amman yana da karfi sosai da zogi domin ina shakarsa hankalina ya bace... ***. ****. **** Aliyu ya lumshe ido ya jinginar da kansa yana kallon sama, kwallar dake makkale a idonsa suka sauko masa ta gefen idon, Fatima na gani ta fara masa tambaya. "Ba za mu isa Lafiya ba? Mutuwa za mu yi?" Ya bude idon da sauri ya kalli Fatima yana murmushi domin be san ma kwallar ta sauko masa ba. [6/28, 10:18 PM] : https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL ABOKIN RAYUWA
Chapter 95 · 0% Book details