← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 177

Sashe 89

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3 ALIYU POV. Ya gyara zamansa da kyau sannan ya kunna Voice din ya fara saurare. *** *** *** Tun ana sauran sati daya Turhan ya zo garin Kaduna, mahaifiyarsa ta fara shirye shiryen tarbarsa, duk wani abun da ta san zata girka masa ta tanade shi da wuri, a tsawon satin daya kullum ni take sakawa na gyara masa dakinsa na saka turare. Ana gobe zai iso Ammy tasa na fara shirya masa abincin da ta san ko ya kwana ba zai lalace ba kamar snacks da nama, ranar da zai iso tasa na shirya masa full Medames miyar waken fava daya daga cikin abincin da mutanen sudan suke so sosai, ita ta koya min yadda zan hada har aka yi nasara na gama komai cikin sa'a, ragowar abinci kuma sai ta bukaci na girka miyar waina (masa) bayan na hada na bar miyar a wuta sai kuma ta bukaci na zo na toya Masar, haka dai na daure na karasa aikin, bayan na gama tasa na yanke masa fruit, na hada fruitsalad, kusan komai da Turhan zai ci ko ya sha ko ya taba Ammy ni ta saka na shirya, sannan ta bukaci na shiga ciki na yi wanka na shirya, tufafin da zan saka ma ita ta zaba min. Bayan na yi wanka ina tsaye gaban madubi ina daura lafayar da ya ki dauruwa a jiki Ammy ta shigo fuskarta dauke da murmushi tana kallo. "Maa Shaa Allah kin yi kyau sosai yata, shiyasana zaba miki wannan lafayar ai, nasan bakin abu zai miki kyau sosai, ki yi hakuri yau na saka ki aiki da yau, so nake Turhan ya ci abincin kuma ke ma ki saba da fara yi masa hidima tun yanzu" Ban ce komai ba, kuma ban ji farinciki ko kishiyarsa ba, ita da kanta ta taimaka min na daura lafayar sannan ta fice. Be shigo gidan ba sai da La'asar. Ina daki Ammy ta aiko a kira ni muka dugunzuma gaba dayan gidan har masu aiki zuwa tarbon da aya a gurin Ammy. Sarauta da kudi wani abu ne mai matukar burgewa da daukar hankali, wa can lokacin kamin ranar ban taba ganin irin motar da aka kawo Turhan da ita ba, sai dai na ga tsabanin yadda Ammy ta fada min cewar mutanen kasar Sudan musamman a gidansu Jallabiya suke sakawa, dan haka na tsammaci ganin jallabiyar a jikinsa, sai dai ya zo akasin tunanina domin kananan kaya ne a jikin wando da riga, wani irin kamshi yake mai dadi. Kuma tabbas kyakkyawa ne a zahiri fiye da hoto ma, fari fes kamar dai kai yana da tsaye duk wata siffa da namiji zai cika aso shi ko ya burge Turhan ya cika wannan, Wallahi da na yi arba da shi sai na ji burgeni ba, wata kila saboda kyau ya daina rudata tun daga kan Khaleefa, ba ma akasin kuma ya zama dalili na banbanci al'ada da kalar halshe. Ya shigo da far'asarsa Ammy tana ta gu a, kowa yana murna da zuwa ni ma sai na yi yake na yi masa sannu da zuwa kamar kowa, sai da ya fara shiga falon sannan kowa ya shiga ya zauna Ammy na watsa masa fulawa tana masa marhabun da zuwa, shi ma dai ba laifi yana da far'a da sakin fuska a farkon ganina da shi, amman yana da jin kai sosai a kallonsa kadai zaka iya fahimtar hakan. Bayan an gama murnar zuwansa na koma dakina shi ma ya shiga dakinsa yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin sannan yayi sallah, sai da kowa ya hallara falon sannan Ammy ta aiko a kira wai na sauko mu ci abinci, daman babu wanda ya ci komai duk shi muke jiran ya iso. Cikin rashin sakewa na sauko na zauna a dinning din na fara zuba nawa abinci ina sauraren yadda yake taba hira da hausarsa mai harshen larabci yana yi yana hadawa da larabci, sai yaba abincin yake. Tun da na zauna be kalli inda nake ba ni ma ban kalleshi ba, haka nan kawai babu dalili nake jin be yi min ba. Sai da yayi rabin plate sannan ya kalleni ya ce. "Ammy ina kuka samo wannan katuwar mace? Mai kama da orange cat" Na ji gabana ya fadi domin ya aybanta hallitatta tun gabanin ya san wacece ni. Ban ce komai ba na cigaba da cin abincina. Sai Ammy tace. "Kasan orange cat fa kyakkyawar mage ce kowa yana sonta, kuma orange cat din ita ta shirya maka komai da yake nan har kake santi, kuma ita ta gyara maka daki ta saka turare" Ya dan tabe baki yayi murmushi. "Yayi kyau" Daga haka be sake cewa komai ba, ni kuma ban sake kallo inda yake ba, ba karya ya fada ba na yi kiba da yawa na wuce kimar shekaruna, domin a lokacin ban kai shekara ashirin ba, amman kumburin da na yi na haihuwar London sai ya shige min a jiki ya zame min kiba, sai dai ban taba jin muzancin kibar ba sai a ranar da Turhan ya kira da big fat, kuma orange cat, a take na ji abincin ya fita raina gudun Ammy ta gane raina ya bace ya saka na yi karya. "Na ji kamar Ibrahim yana kuka bari na duba shi" Ina fadar hakan kan na mike tsaye kan kujera Turhan ya maido da abincin dake bakinsa a plate din dake gabansa. "Haba Ammy kin san tana da yara kika bari ta girka min abinci? Kin san bana son yara kyamarsu nake" Na kalleshi kawai ya dauke kai na nufi hanyar da zata sadani da stairs, kamin na shiga dakin na cika kaina fal da tambayoyi kala kala. Anya abun da Ammy take kokarin aikatawa mai yiyuwa ne kuwa, ni dai tun ganin farko be kwanta min a rana ba, da alama ni ma ban burge shi ba da va zai furta wannan kalamin a yanzu ba, baya ga haka kuma ya fadi cewar baya son yara kazantarsu yake gani, har yana kyamar abincin da na girka masa to ta iya zai iya zama da ni ma? Ko dai minene ni dai na yi alkawarin ba zan taba furtawa Ammy cewar bana son danta ko kuma ba zan amince da kudurinta ba, domin ta yi min hallaci a lokacin kuma idan na ki danta ina zan koma na zauna. Na yi tunanin Ammy zata duba dan abun da ya faru a tsakaninmu gurin cin abincin nan ta tsagaita wasu abubuwa amman babu abun da ta fasa, gaba daya idonta ya rufe saboda tana son danta yayi aure daga bangarenta ya samu nasa iyalin tana son danta ya dawo kusa da ita, bata duba halin da ni zan kasance ba. Tun daga wacan ranar ban sake shiga Kitchen ba ita take girka masa abun da zai ci ko ya sha, sai dai a kullum teburi daya muke zama gaban dayanmu mu ci abinci, na safe ko rana ko dare, idan ya riga ni zama na iso zai daure fuska ya daina dariyar da yake idan na gaishe shi ya amsa min kamar an masa dole. Idan kuma ni na fara zama baya sake fuska yayi hira da Ammy sai idan na bar gurin. Sai da ya kwana bakwai a gidan a gidan sannan ya shigo dakina, bayan Ammy ta shigo ta sanar min zata je dubiya marar lafiya ta dawo. Ina zaune ina yi ma London wasa yana dariya a cikin yanayinsa, kamin ya zabura ya kwalla ihu saboda shigowar da Turhan yayi yanayin bude kofar sai ya firgitashi a take ya saka kwallowa yana wani birkicewa ni kuwa na kama shi na rumgume ina rarrashinsa. "Me ya same shi?" "Shigowarka ce ta firgita shi" "Shigowa ta kuma? Dodo ne ni?" "Aa haka yake idan ya tsoro ta, komai a sannu ake masa saboda autism ne" Ya maida kofar ya rufe. "Kice mahaukaci kika haifa kenan?" Ita ce magana ta biyu da ya furta a gareni mai daci tun bayan zuwansa gidan, abun da ban sani ba ashe shi din gwanin cin fuska da bakar magana ne. "Aa ba mahaukaci ba ne, ba shi da lafiya ne dai" Ya zauna a nesa da ni jikin wata kujera dake kusa da kofar dakin. "Yana daya daga cikin dalilin da ya saka bana son yara, wannan hayaniyar da kazantar ni ba zan iya dauka ba" Yana maganar yana yatsina fuska kamar wanda yayi arba da wani abun kazanta, sai kuma ya bi dakin da kallo. "Ammy ta ba ni labarinki, ta fada min musulunta kika yi ko? Ke tubabbiya ce? Kuma na tausaya miki matuka, amman abun da ban gamsu da shi ba shi ne, miyasa mijinki be tashi wulakantaki ba sai da kika haihu?" "Wata kila ta manta bata fada maka ba, da cikin ya kore ni a hanya na haihu" "Yeah what i mean is, Allah yasa da gaske mijin ne ya koreni ba irin abun nan kika yi ba na yan matan zamani, kin san akwai wadanda kunyar haifar yaron ke saka su barin gari sai su tare a wani gurin su yi karya saboda su samu mafaka" Na yi shiru bance masa komai ba, zuciyata kuma bata fasa sosuwa da kalamansa ba. "Ke ruwa biyu ce? Ko kuma zabaya ce ke? (irin mutanen da ake haihuwa masu fari sosai)" Na fi kyautata zaton ruwa biyu ce ni, domin zabaya ba haka suke ba" "Eh na ga kuna da dan banbanci, maganar gaskiya ba wai na zo ne saboda na muzantaki ba, duk wani abu da zan fada miki gaskiya nake fada miki zahirinta, ban sani ba ko Ammy ta yi miki maganata?" Nan ma ban ce masa uffan ba. "Ke ba wata macen arziki ba sai shegen jinka, baki san waye ni ba? Ko kuma saboda Ammy ta kawo ki a nan gidan kika jin wata ce ke? Har ina tambayarki ki yi min shiru? Kina fama da jiki kamar uwar mata" "Wa can lokacin bana iya maida magana dan haka na danne zuciyata ina jin yana aybanta ni amman bana iya ce masa komai" "Ammy ta so ma
Chapter 89 · 0% Book details