← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 177

Sashe 102

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 4 KAMEELA POV. Tun da ta fara tukin bata tsaya ko'ina ba sai bakin gate din gidanta, ta yi horn mai gadin ya leko ya ga ita ce ya koma ciki ya bude ta shiga ta faka rai a bace bata ko tsaya kashe motar ba ta fita ta banki kofar falon da karfi ta murda ta shiga, Fatima dake zaune kan kujera ta zabura ta mike tsaye tana kallon Kameela. Kameela ta harari Fatima kasa da sama ta tabe baki. "Eh lallai ashe da gaske ne, amman Wallahi Aliyu ya gama cin mutumci na, kuma ya nunawa yarinyar shegiyar matar nan ba ni daraja a gurinsa" Ta yi kwafa ta shiga kitchen din ta duba abincin da suka ci suka rage, ta fito tana tambayar Fatima da turanci. "Ina Emily take?" "Tana can ba da ita muka zo ba" "Ke ma da ganinki zaki yi munarfuci, waya sani ko daukota yayi har uwar suka zo" Ta fada da hausa sannan ta kama hannun Fatima ta karbe wayar hannunta. "Ai yau za'ayi ta ta kare, sai na datse duk wata alaka dake tsakanin matsiyarcin uwarki kwartuwa mai bin mazajen mutane" CONTACT list dinsa ta shiga ta nemo number Ammy ta kirata da layin Aliyu, Ammy ta daga tare da sallama, Kameela ta amsa tana fadar ba Aliyu ba ne. "Ni ce Ammy matarsa Kameela" "Maa Shaa Allahu Kameela kina lafiya ya gidan?" "Ammy ba lokacin gaisuwa kwatancen gidanki zaki min faka faka" "Lafiya?" "idan na zo zaki ji Ammy fada min kawai" Ammy ta kwatanta mata Kameela ta sauke wayar ta kama hannun Fatima sai Fatima ta ficike hannunta. "My Momy warn me not to talk to strangers" "Aliyu ne ya ce na zo na tafi da ke yana can wani gida zai siya miki ice din yace ma kawo ki" Fatima na jin haka sai ta yarda Kameela ta kama hannunta suka fita ta bude mota ta saka ta ta shiga taja motar mai gadin ya sake bude mata ta fita, tana tukin tana bala'i Fatima sai kallonta take domin bata jin yaren da take. "Ki bani wayar zan cigaba da kallona" Kameela ta mika mata wayar ko kira zata yi ai ba shi da amfani yanzu tun da ta riga ta san gidan Ammy, daman sau daya ta taba zuwa shi ma kuma Aliyu ne ya kaita. "Dan ubanki gurin uwar ubankin zan kaiki, ayi ta ta kare, na huta da wannan bibiyar da uwarki take ma mijina, sai kace shi yake nemanta, ga mai nemanta ga wanda take likewa, ina na taba ganin haka dan kawai neman a dora min hawan jini" Bata sha wahala gurin gane gidan ba kasancewar unguwar ba a boye take ba, kuma gidan babban gida ne a layin, tana isa bakin gate din gidan ta gane lallai gidan dai da suka taba zuwa da Aliyu sau daya. Ta yi horn mai gadin ya bude mata ya shiga ciki ta faka ta zagayo ta budewa Fatima ta riko hannunta ta fito da ita. "Ina yake?" "Yana ciki sai mun shiga" Fatima ta bita babu wani rigima suka shiga cikin falon, tsabar neman fitina da tsoron abun da zata aikata da kuma bakin kishi da suka hade mata guri daya Kameela har numfashi take sama sama kamar wanda ta dauko katon dutse. Da sallama ta shiga falon Yan matan nan biyu da Ammy take riko suka amsa mata, Ammy na zaune kan kujera nurse na kusa da ita tana hauna bp dinta, daman ta fi yawan zaman falon gudun wahalar da mazu zuwa ganinta ba sun haura sama inda take ba. "Ina yake?" Fatima ta tambaya da karfi tana fisge hannunta daga rikon da Kameela ta yi mata. A take Kameela ta daka mata tsawa ta watsa mata harara. "Ki zauna" "Ba zan zauna ba, ina Uncle Aliyu? Kina kokarin sace ni ne? Su waye wadannan mutanen mama na tace kar na yi magana da wanda ban sani ba" Ta saka ihu mai karfi babu saurara ahhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh ta cika musu kunne. Ammy ta kalli Kameela tana tambayar tafiya, Kameela ta rasa ta ita zata fara bayani ga Fatima na mata ihu gashi bata san yadda zata fara warware zaren zancen ba. Ihun Fatima ne ya saka Turhan dake dakinsa cikin damuwa ya saukowa kasa domin duba abun da ke faruwa. Saukowa da Turhan yake ne a hankali ya saka Ammy daga kai ta kalleshi daga kansa ta sauke idonta akan Fatima dake ta ihu, sai gata a tsaye kamar ba marar lafiya ba. Ta ko'ina Fatima kama take da Turhan kamar an tsaga kara kamar har ta bace har gashin kanta baki ne kamar na mahaifinta sai ka rantse tsumata aka yi a cikin jikin Turhan aka ciro bata rage komai nasa ba, banbancin kawai ita mace ce shi namiji kuma ita tana karama shi kuma babba. "La'ilaha illallahu, La'ilaha illallahu, La'ilaha illallahu" Kawai Ammy take maimaitawa jikinta na rawa hawaye na sauko mata. "Yauwa kin gane kenan" Kameela ta fada kamin ta juya ta kalli Turhan daya tsaya be karaso ba, bata san yana garin ba sai a lokacin. "Alhamdulillah faduwa ta zo daidai da zama" Ta fada tana kallon Turhan da gabansa ke dukan uku uku ba kuma tare da fahimtar komai ba, shi dai ya san ba lafiya ba, ganin yadda Ammy take ta ambaton Allah ta mike tsaye ga kuma yarinyar dake ihu ga kuma Matar Aliyu. "Ka karaso mana Turhan wannan yarka ce" Turhan ya kalleta ya kalli Ammy. "Ban fahimta ba" "Yarka ce sunanta Fatima, Emily ta haife ta muma jininka ce Aliyu ma da kansa ya fada, tana boye maka ita ne tana boye maka kanta, ni na gaji shiyasa nake son ayi ta ta kare shiyasa na kawo ta, na gaji dan Allah idan ka ga Emily ka rike ta na huta, na samu kwanciyar hankali da mijina, ta kyale min mijina dan Allah duk wani boye boye da ake ban gane kanshi ba, matar nan ta hana ni zaman gidana cikin kwanciyar hankali abun ya wuce PH ya biyo har nan Kaduna na gaji, Aliyu be san na kawo ta nan amman na san dole Emily zata zo" A cikin kalamanta babu wanda Turhan ya ji kuma ya fahimta sai kalmar ARKA CE... kalma ta maimaita kanta a kunensa ya fi sau saba'in tun da ya dora idonsa akan Fatima be kyabta ba, sigar jikinsa kawai ke tashi zuciyarsa ta karaya bugun zuciyarsa ya karu fiye da kima, sai a yanzu ya fahimci Ammy na ambatar Allah ba tare da an bata mata ba, kamaninsa ne sak a fuskar Fatima. "Ke dalla dufewa mutane baki kin ga ubanki can" Kameela ta fada ma Fatima da turanci tana nuna mata Turhan. Sai Fatima ta lake kafada ta fara magana cike da tsiwa da iyayi. "Noooo Momy ta fada min ni bani da Baba ni kadai aka haifa haka, kowa yana da Baba amman Momy tace ni ba ni da Baba baki kiji sunana ba Fatima Emily Aisha" Turhan ya zube kasan guiwowinsa ya daga kansa sama ya bude baki yana numfashi da karfi kamar wanda zai mutu. Fatima ta fashe da wani irin kuka mai karfi na gaske domin bata fahimci me suke ba, gashi bata san kowa ba a cikinsu yanzu kam ta fara tsorata. "Take me back to uncle Aliyu or Momy" Kameela ta buge hannu. Ammy ta karasa ta dafa Fatima tana kuka ta kama fuska tana kallo, ta zube a gurin tana ta taba taba jikin Fatima "Allah na gode maka, Allah Aisha kawai nake nema amman ka hado min har da yarta, jikata Allah na gode, Allah ya miki albarka Kameela" Kameela dai bata ce komai ba ta juya ta fice da sauri. "I want my momy" Ammy ta dorata a cinyarta tana kuka ta rumgumeta. Turhan ya ka dagowa daga inda ya fadi durkushe ya kara karasa gurin da Fatima take jikinsa da zuciyarsa sai rawa suke abun ya zo masa kamar mafarki, ya rasa ta yi zai yi ya yarda wannan abun ba mafarki ba ne, shi dai Emily kawai yake nema shi ma kuma saboda Ammy. Da rarrafe ya karasa gurin tana kallon Fatima ya kai hannunsa zai taba ta sai ya kasa ya maida hannu, ya shafe hannunsa jikin rigarsa gaba da baya kamar mai kokarin cire kazanta ya sake mika hannunsa zai taba ba a nan ma ya kasa jikinsa sai rawa yake. "Yarka ce Turhan, jinin ya fi ruwa kauri, jini be karya, yarka ce" Ammy ta kama hannun Turhan ta kai a jikin Fatima, sai ya ji wani abu kamar shokin Fatima kuma ta zabura da karfi, a take ya tuna da abun da ya faru a airport lokacin da suka hadu da Aliyu ya taba babyn da yake dauke da ita tana bachi amman sai da ta zabura. Turhan ya fisge Fatima a jikin Ammy ya rumgumeta da karfi jikinsa ya mike tsaye yana kuka kamar wani karamin yaro, a take kukan Fatima ya yanke ta yi shiru kamar ba ita ba, ita m ta ji wani abu na dabam gashi ta ji yana kuka bata san dalilin ba, daga tsayen kukan ya kasa rike shi ya zube kasa yana rumgume da ita, kusan kowa a falon kuka yake har Nurse din da bata san hawa da sauka ba. Ammy ta daga hannunta tana magana. "Haka na yi nufi, ku zauna tare ku yi zuri'a ta dalilina, Alhamdulillah ko a yau na mutu burina ya cika, na ga jininka Turhan, ashe ba a banza na ke jin bukatar ganin yarinyar nan ba, ashe akwai abun da Allah ya shirya min da ban sani ba Allah na gode" Ta shafa kan Fatima ta shafa kan Turhan hawaye da murmushi, Turhan ya kwanta jikinta yana rumgume da yarsa Fatima. Wayar dake Hannun Fatima ta yi ringing Turhan ya dago da sauri ya kar i wayar, Emily ya gani rubuce a wayar ya amsa kiran amman ya kasa cewa komai. "Hello Fatima My Baby Girl where are you?" Muryar da ya dade yana nema ta daki kunensa, amman ya kasa amsawa. "Hello baby girl talk to me, ina kike?" Muryar matar daya wulakanta ya nuna mata rashin gata da kiyayya ce take sake
Chapter 102 · 0% Book details