Sashe 8
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Barka da warhaka mutanen arziki Shim kun san cewa Khadeeja Candy komai da komai? Amman banda an mutum da mutum Ina masu neman kayan Kitchen masu kyau masu inganci, Luxury Warmers manya da kanana, ina masu neman Bedsheet kings and Queens manya da kanana, ina masu neman Akwaitunan lefe da na tafiya. Khadeeja Candy na da Boxes kala kala, ina masu neman tufafi, kama daga Atamfa, Laces, Shadda Lace, Veils, shoes and Bags, Materials. Akwai freezer, Gas cooker and water dispenser. Duka zaku samu a gurin Khadeeja Candy Store, Khadeeja Candy dai taku ta makaranta, da fatan za ku yi patronizing ina. Za ku iya join group dina domin bawa idanuwanku abinci https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Kuma zaku iya saka order ta wannan number 08036126660 WhatsApp. KHADEEJA CANDY STORE expect more, and pay less... Page 4 Ragowar cake din dake fridge ta dumama musu, ta dumama madara a microwave sannan ta zuba a plate biyu kowa da cups dinsa sannan ta fito kai tsaye ta nufi dakin London ta shiga da murmushinta sai ta same shi zaune Nannynsa na karanta masa story book. Gefen gadon ta aje masa cup din da cake sannan ta shafa kansa ta sumbance shi. How are you My love Murmushi kawai yayi mata daman be cika magana ba, sai idan ta dauro. Emily ta kalli Nannynsa Chidimma. Ina fatima? Ta shigo amman ganina a dakin ya saka ta fita ina tunanin tana dakinta Okay Ficewa ta yi daga dakin ta tura kofar dakin Fadima sai ta ji ta a rufe, cup din da plate din cake ta hade guri daya ta yi knocking da dayan hannunta. Baby, bude kofar mana I won't Na kawo miki cake da madara Bana so Na fada miki babu kyau bachi da fushi, me yasa kike da kafiya ne? Ki fadawa Vito ya daina zuwa nan i hate him Emily ta daki kofar dakin da karfi. Ki bude kofar nan Fatima and kar na sake jin kin fadi wata kalma marar dadi akan V idan ba haka ba zan bata miki rai Ba zan bude ba!! Fatima ta amsa mata a tsawace kai kace Fatimar ce uwa Emily a, runtse ido ta yi tana maida numfashi a hankali, sanin halin yarta da kafiya da rashin kunya ya saka bata sake bata second a gurin ba ta juya ta sauka kasa, tana saukowa kwakwalwarta na tuna mata da wasu kalamai na bakin littafin da zuciyarta ta aje. _Ka yi hakuri karka rabu da ni, ban san kowa anan ba, ba ni da kowa a nan_ Ina rike da kafarsa nake fadin haka sai ya fisge kafarsa ya matsa baya. _Ina da kafiya akan abun da nake so, da kuma wanda bana so, karki sake nuna kin san ni_ Ina da akan center table ta aje cake da milk din cikin bacin rai, ta zauna a kujera zuciyarta na yi mata babu dadi. _Ina da mata ina da iyali, kin zo ne kawai ki ruguza rayuwata Aisha_ Jefe jefa kanana da manyan abubuwan da suke faru a rayuwarta ta baya suke dawo mata a duk lokacin da take zaune ita kadai ko kuma rai ya bace. A fusace ta mike tsayeta ture madarar da cake din har sai da suka zube kasa. Daman idan baki yi kafiya ba ai ke ba yarsa bace...!! Ta karasa da kara sosai kamar mai shirin yin duka sai haki take, windows falon ta nufa da curtain dinsa suke a bude ta tsaya sai ta hango Sarkin nata zauna kishingiden a cikin motarsa gilashin motar yana kasa gaba daya, yana kallon windows din da take tsaye, rufe curtain din ta yi ta nufi kofar falon ta bude ta fita. Hango fitowarta ya saka shi fitowa daga cikin motarsa yana jiran tsorowarta. Tsayawa ta yi a gabansa hasken kwayayen dake cike a gidan suna haska fatarta mai tsananin fari. Akwai abun da kake bukata ne? Ta ido yana amsa tambayarta, a sa'ilin da bakinsa yayi nauyi furta mata kalamansa. You... Ya furta bayan ya kwaci kansa. Babu bata lokaci ta rumgume shi, ta lumshe idonta dake kwance da ruwan hawaye. Da ace tana da wani abun da zata aikata ta biya V da tuni ta aikata, domin shi ne mutumen da ya mayar da ita yadda take a yanzu, shi ne mutumen da be nuna mata kyama ba, ko da yake shi din kistane dan'uwanta da musulmi ne babu tantama da yanzu ya rabu da ita ko ya ci amanarta, amman shi yana nan tare da ita duk kuwa da irin kyamar da yarta take nuna masa. Slowly ya zagaye bayanta da hannayensa ya rumgume ta comfortably, idonsa a sama yana kallon window Fatima dake rufe cike da bacin rai, domin ya tsani duk wani abu da zai batawa Emily rai idan aka cire shi kansa, a iyakar gidan yasan babu mai yi mata rashin kunya da rashin magana da kokarin bata mata rai ko tuna mata da rayuwar da ta jefar sai Fatima, domin London ba shi da lafiyar damuwa rayuwar kowa sai idan ciwonsa ya tashi. Ta dago daga cikinsa a hankali ba tare da ta kalleshi ba, sai ya kai hannunsa ya rika pink lips dinta ya dan dagota kadan. Karfe nawa zaki tafi aiki gobe? 6:30am Ya sake kallonta da kyau yana matsawa kusa da ita. Wane irin aiki ne ake tafiya karfe 6:30am na safe? Haka matar ta fada min karfe 7 ta yi min a can Ta amsa har lokacin bata kalleshi ba. Ya kankance ido kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya kai hannunsa yana shafa gefen fuskarta. Shiga ki kwanta, ki samu bachi da wuri Ta kalleshi kadan. Good night I love you Ya furta ba tare da jiran ta mayar masa ba, domin be taba furta yana kaunarta ta amsa masa ba, tun farkon haduwarsu har zuwa yanzu da take kokarin samun kanta, ya mata uzuri domin ya nutsa a labarinta, yayi rayuwa da ita ya san zahiri da badininta, yana iya jin yadda abun ke tsikarta duk kuwa da kasancewar be wanzu cikin wancan rayuwarta ta ba, sai dai a yanzu ya jiku da kaunarta sonta na hana shi ganin abubuwa da yawa a na laifi akanta. Tana tafiya rumgume da hannayenta har ta shiga falon ta rufe sannan ta shiga wani bangare na falon ta dauko mopper ta gyara gurin, a falon ta zauna na tsawon lokaci, ba kallo take ba, ba tunani take ba, ba bachi taka ba, wani yanayi take ji wanda rabinsa babu bakinciki, kuma babu kishiyarsa, wani yanayi taka ji na dabam. Motsin saukowar Chidimma ya saka ta juyo tana kallon stairs din har Nannyn ta sauko. London yayi bachi, Fatima kuma dakinta a rufe yake, na murda bata bude ba, wata kila ita ma ta yi bachin ne Nannyn ta fada cike da ladabi, Emily ta dago daga kishingiden da take a jikin kujerar tana cigaba da kallon Chidimma. Kina kokarin da yarana, musamman Fatima, halayenta ba masu kyau ba ne na sani, amman ina fatan zata sauya nan gaba Chidimma ta yi murmushi tana jindadin yadda Emily ke karfafa nata guiwa tana appreciating duk wani abu da take yi ma yaranta. Zata canja ranki ya dade, a yanzu tana da kurciya ne, she's just 6 Emily ta daga gira. I hope so, Good night Chidimma Good Night Ma'am Ta amsa mata da kai sannan ta fice daga katon falon, Emily ta mike tsaye ta rufe kofar falon sannan ta kashe komai na kallo da kuma na'urar sanyaya falo ta haura sama, dakinta ta shiga ta dauke wani makullin ta nufi dakin Fatima ta saka key din ta bude dakin. Turawa ta yi ta shiga sai ta same ta kwance a kasa rumgume da teddy dinta, sanin yarta sikila ce ya saka ta fara kashe ac dakin dake kunne domin akwai sanyi a garin, karamin abu ne ta tashi da ciwo washe gari. Gefen gadon ta zauna tana kallon Fatima da kamanin mahaifinta suke zube a fuskarta kamar an tsaga kara, ta kai hannunta ta shafa fuskar yarta. Ina da tsada a gareki Fatima, amman baki sani ba, saboda kina karama, kina fada min magana son ranki, kina wasu halaye da bana so, ina jin cewar kamar ke ma kin tsane ne kamar mahaifinki Ta share hawayen da suka zubo mata. Kin yi sa'a kina da ni a raye, a lokacin da nake sa'arki, ina a wani gidan marayu tare da yaran da suka rasa iyaye ko aka tsinta, macen dake kula da ni ta fada min ina jaririya ba a yanke min cibiya ba aka aje ni a gidan, har yau ban san dalilin da zai saka uwa ta aikatawa yarta haka ba Ta shafa fuskar Fatima a karo na biyu, sai kuma ta yi murmushi. Na san zafin rashi, na san zafin yaudara, na san zafin kiyayya, ba zan yarda ku fuskanci ko daya ba, zan jure zan mutu saboda ku yara, ku ne kawai iyalina Ta sumbanci kumatun Fatima ta aga daga kan gadon ta gyara mata lullubinta sannan ta fice daga dakin, ta nufi dakin anta na fari. Tana kallon fuskarta sai ta yi murmushi ta gyara masa kwancinsa tana zancen zuci. Wata kila ni tawa uwar ta mutu, shiyasa aka kawo ni a nan, amman me yasa yan'uwanta ko yan'uwan mahaifina ba su iya rike ni ba? Haihu ba tare da aure ba a addinin kirista ba abu ne na kunya ba, kamar wasu addinan ba, balle nace ko tana kunyar haihuwata ne Ta sauke ajiyar zuciya a hankali, sannan ta fito daga dakin ta koma dakinta, gaban madubi ta zauna tana kallon kanta, sam ba zaka santa a da ka ganta a yanzu kace ita ce ba, sai idan ka yi mata farin sani, domin jikin da take da shi a can da, yanzu babu, ta zama fit da ita like a model, farin fatarta a yanzu ya sauya ya ninku da kaso mafi daraja domin a yanzu ta samu kwanciyar hankali da abinci mai kyau da lafiyayyen gurin bachi, da kwanciyar hankali, abubuwan da ta rasa a baya. Ta fara tsege kanta tana tuna wani lokaci da Khalifa yake yanke mata gashin kai saboda kawai wulakanci da tozarci, har ta gama tsife kan ta