Sashe 167
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saurayi zan yi aure" Farida ta gwalo ido. "Eyyy sai kice ya saki matarsa ya aure ki? Tsakani da Allah Kameela ki aje wannan tunanin a gafe, yanzu fa gasar kudi ake ba ta kishi ba, kishi da hauka na talaka ne, indai mutum yana da yan kudadensa iya ruwansa da wani kishi, kuma duk manyan mutanan da ke sonki kowa da matarsa da yara ta ina zai saki matarsa ya aureki? Wani ma mata biyu" "Ki daina zancen manyan mutane, na auri wanda ya kusa haihuwa da majina zan ji ko da kishi ko yayansa? Ko kuma so kike na sake auren na fito?" "Aa amman mai kudi wake zancen majinarsa? Murar ma ai sai talaka, da kudinsu wa zai kula wannan kuma mataki suke dauka, ni Wallahi kawai ki yarda hannu ya koma miya bawan Allah nan yana aurenki first lady zai maidaki, daman yana neman yar boko kuma wayayen kyakkyawa ta nuna mai dan jiki fit haka dai kamar ke" Kameela ta ja tsaki ta tashi ta fice ta bar mata dakin. Ta yi ma kanta alkawarin ba zata sake waiwayar Aliyu, ta riga da ta aje shi a gafe yanzu saboda ya yi aure. Abu kamar wasa kamar gaske, Kameela ta kasa kula kowa, idan ta ji labarin kana da aure da iyali sai ta aje ka a lissafi. Mahaifiyarta da iyayenta suna kokari sosai gurin lurar da ita abubuwan da ya kama ta dauka da muhimmanci a aure amman ta kasa domin ba wai iya rabuwa da mata ba, ita ko mai yayan wata bata so. Burinta ace ita kadai ce agidanta sai yayanta. Saurayin da take ta jira ya ki samuwa, akan nuna ana sonta, wasu da yawa da suka nemeta lokacin da tana budurwa ba su samu ba, sun dawo amman ta gagara kula ko daya saboda dukansu suna da aure, jiran take sai ta samu marar mata kuma wanda zai fara gina iyali da ita. Ta kasa karyata zuciyarta ta kasa yarda da kaddararta tana da wasa da lokacinta, zuciyarta na ta yi mata hange hange marasa amfani. Kuma ta kasa cire Aliyu a ranta, kawai ta hakura da shi ne, amman sonsa ya ki barinta, kishinta ya ki ya tafi, kusan kullum idan ta kwanta da tunaninsa ai ta tuna a yanzu wata macen ce a kirjinsa ba ita ba, wata macen ce take kula da shi ba ita ba. Wasa wasa Kameela ta fara nisa cikin burin da zuciyarta ta dora nata, na yaki da umarnin Allah, madadin hakuri da hukuncinsa. Ba iyayenta kadai ba ita kanta abun yana damunta, ta kasa focusing a kan rayuwarta, ta kasa manta Aliyu da zamantakewarsu, ta kasa bawa wasu mazan dama. Tun yan'uwanta suna lallabata mata har lamarin ya fara ba su haushi suna fita sabgarta. Ta kai ita kadai take iya fahimtar kanta, ta kan kebe ta yi ma kanta tambayoyin da ba su da amfani da kuma nadamar da bata haifar mata da komai ba sai bakinciki. A yanzu ta gane ta inda matsalar ta bullo, sanadin zafin kishinta ne, ya kaita ga kokarin halaka mijinta, domin ita ce babbar damuwarta a yanzu, wata kila da bata yi kokarin kashe su ba, da Ummi ba zata hana su zauna ba, duk abubuwan nan da suka faru da yanzu ba su kawo nan ba. Wata kila kuma da ta daure ta hana zuciyarta daukar Fatima ta kai ga Turhan mai yiyuwa da yanzu Aliyu be sake ta ba domin ne mafarin tonon asirinta kuma mafarin rabuwarsu. Idan ta so samawa kanta sassauci kuma sai ta tuna ai Aliyun ne ya fara kula Emily bayan kuma yayi mata alkawarin babu karin aure sai kuma ya zagaya yana bibiyar Emily. Ba ita kadai ba kowace mace ba zata dauka ba balle kuma ita dake da zafin kishi. Wani alkawari da ta daukarwa kanta kuma take da yakinin zata iya cikawa shi ne, hakura da zaman aure da Aliyu, ko da kuwa zai dawo ya ce zai maida ita a yanzu, bibiyar da ta yi masa a baya ma nadama take yanzu, domin ta san ba ajinta ba ne, namiji ya sake ta akan abun da ta fishi gaskiya kuma ta bibiyeshi ya kasa saurarenta. Ita sam bata ma amfanin zama da mutumen da ya nuna wata macen ta matarsa ta gida muhimmanci ba, ba dan haka ba babu abun da zai saka ba zai aje lamarinta a gafe ta kula Emily ba. Idan yan'uwanta suka so kara mata bakinciki sai su ce "Ai daman can Aliyun ba wani sonki yake ba. Ke ce kika makale masa, uwarsa ma ba sonki take ba" Zata iya yarda Ummi bata sonta even though bata mata wani abun dake nuna tsantsar kiyayya ba, sai dai kuma bata taba nuna mata tsantsan soyayya ba, bata yi mata gatan da ta yi ma Emily ba, bata kulata kamar yadda take samun labarin tana kula Emily ba. Kuma a yanzu ma ita ce ta cilastawa Aliyu juya mata baya bayan ta wulakanta a gidanta. Amman zancen Aliyu be sonta, sam hankalinta ba zai dauka ba, ta san mijinta yana sonta, domin mai aki shi ya san inda yake masa yoyo, ta san waye Aliyu ta san irin zaman da ta yi da shi, ta san rigimarta da yadda take kureshi kuma duk ya daga mata kafa, ta san yadda yake nuna mata soyayya ciki da waje. Wannan na daya daga cikin dalilin da ya saka take hango yadda zata yi rayuwa da wani wanda ba shi ba. Yan'uwanta a kullum cikin nuna mata yadda zata walwala su ninka arziki da karfi a siyasa suke idan ta yarda ta auri abokin mahaifinsu. "Ni gaskiya ya min tsufa ga mata ga yara, ni ba ta siyasar ko kudinsa nake ba" "Matsalata da ke baki iya daukar shawara ba, ga kuma rashin hangen nesa, ai ko dan ki bawa Aliyun da uwarsa haush da ma matar ya kamata ki aure shi, kullum su yi ta ganinki gaban tv komai za'ayi sai da ke, idan kika yi hakuri ma kina gidan sai ya sake su ki koma ke kadai sai yayan da za ki haifa, ke yanzu ni ban isheki ishara ba? Yau ina Baraka ina Yayanta suke? Sai dai idan ubansu yayi marmarin ganinsu ya je ya gansu ko ya aika musu da sako, ni ko ganinsu ma bana jin yana zuwa yi, domin ko jiya da na masa maganarta cewa yayi na daina tuna masa da ita, na ce ranka ya dade ai dole na tuna maka saboda akwai yaya a tsakanin sai ya ce yara idan suka so ganinsa sun san inda yake ai, shi dai hakkin dake tsakaninsa da su ya kula da cinsu shansu da kuma sauran hidindimun rayuwa, ke har cewa yayi ba dan kar dawowar nan ya zama matsala a gareni da su ba sai ya karbe yaransa sun dawo nan, ni kuwa na yi karaf na ce a'a ya bar mata yaranta ta rike, toh ina zan iya da rikon balagagun yaya?" Tana magana tana tsire baki dadin ya isheta, yanzu Mama Baraka da yayanta basa gidan. Ta shafa kanta yarta. " Shiyasa nake son ki fitar da miji ki yi aurenki ki manta da wani Ali, daman can ba ku dace da juna ba, balle kuma yanzu da ya auri shegiya, kuma yar Baraka, ko dan ke na san dole ta aura masa ita, kuma abun kamar ba na banza ba, kin san lamarin yarbawa fa, in ba shi ba yaushe Aliyu zai auri shegiya? Ko da tana da kyau ai Asali wani abu ne mai girma, ko dan yayan mutum" "Daman ita ta lalata komai gurinta nake tafiya neman shawara lokacin da muna samun tsabani kuma ba ta ba ni shawarar kwarai har cewa take ba laifin yarinyar ba ne, ashe saboda ta san yarta ce" "Eh mana, dan Allah ki bawa mara a kunya, ki zabi mijinki ki yi aurenki ga ki tsaye da kyau zaune da kyau son kowa kin wanda ya rasa, idan ma ba ki som shi His Excellency ki zaba cikin masu son ki mana, daman Alhaji yace tun da yayi maganar be sake ba, be zama lallai sai shi ba, ki zaba wanda kike so ki ba shi dama idan vaki bada daman ba baza ki iya kawar da tunani da damuwa a ranki ba, amman fa karki dauko an makiyinmu kuma, karki mana na Aliyu, yanzu kam ba za mu bari ba ma" Ta kwnatar da kanta a cinyar mahaifiyarta. "Ki taya ni da addu'a Hajiya Allah ya sauya abun da nake ji a zuciyata kuma ya zaba min inda zan samu kwanciyar hankali da zaman lafiya, duk masu mata ne, samarin sun ki zuwa wai ko dai dan na yi aure ne?" "Aa ina ruwan aure da samarin, ke yanzu baki san an fi son zaurawan ba? Kuma saurayin zai iya zuwa, amman dai mun fi son mai kunbar susa, kin san logi be kin dadi, ba mu ki ace surukanmu duk manyan mutane ne ba, su kuma samari nan wasu ba rikon aure ba wasu kansu babu komai ciki sai tunanin abubuwan da ba su za su gina gobensu ba, kadan kake samu na kwarai, yanzu ba ga Aliyu ba? Amman da ace wanda ya san ciwon kansa kika aura inda ba shegen zamani ba ne, babu ruwansa da wani hango wata sai hada hadar kudi, ina za su shigo ina suka fita, daman duk abun da iyaye ba so babu albarka a cikinsa, shiyasa Aliyu ya zama haka" Hausawa suka ce wanda ya cika da ya i ya mallakeka har anka, babu yadda Kameela iya bayan bin shawarar mahaifiyarta da yan'uwanta matukar tana son zama lafiya da su, kuma ta shirya samawa zuciyarta salama. Abun babu dadi kam amman dole ta daure a haka ta budewa masu kwankwaso kofarta dama, ko labarin zai sauya. Tun da wadanda take dakon zuwa sun manta hanya, wato marar mata da yaya ko kuma saurayi, har yau bata samu ko daya ba, masu matan ne dai suke ta kawo mata hari, daga mai daya, sai biyu har da mai uku yana nema ta hudu da ita tsabar sun raina mata wayo. [8/31, 11:54 PM] ABOKIN RAYUWA