← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 177

Sashe 35

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ya fadi haka ne saboda hankalinta ya kwanta. A asibitin ya kwana tare da matarsa ya kwantar mata da hankali kuma ya lalabata akam tafiyar da Hajiya za ta yi da ita. EMILY POV. Driving kawai yake tana kalle kalle bata shirya komawa gida, kuma bata san gurin da zata je ba, haka ta yi ta yawo kamar zata zagaye garin kamin ta faka motarta kusa da wasu dakuna da suke kamar quarters. Bude gambun motar tayi ta fito daga cikin motar ta nufi wani katon dutse da yake gurin ta zauna. Kallo daya zaka yi mata ka fahimci bata cikin farinciki, domin fuskarta a fili take nuna damuwar dake zuciyarta. Rabo ido take amman zuciyarta da hankalinta suna wani gurin na dabam. Me kike a nan? Maganar ta ji ne daga gefenta ya saka ta juyo gaba daya sai ta yi arba da matar da ya kusan kade Fatima, kuma ita dai matar da ta gani asibiti ta yi mata magana. idan kina son na tashi na baki guri, zaki iya cewa na tashi na bar unguwar ko gurin, ba sai kin tambayi mai nake ba, ai zaune kike same ni, zama nake yi Ta dan yi murmushi ta zauna kusa da Emily. Baki yi kama da masu zafin rai ba, daga ganin yanayinki na san ranki ne a bace, na hango ki tun daga dakina, karki manta jiya ne ko shekaran jiya ke kika min magana kamin na miki Da na yi miki magana yi kika yi kamar baki san ni ba Ni ma ranar raina yana bace ne ki yi hakuri, Sunana Tasmia" Ta mika mata hannu, Emily ta kalleta kamin ta mika mata nata hannun. Aysha Emily "Nice to meet you Aysha, me kika zo yi unguwar mu?" A nan kika" "huh" Emily ta daga kafadunta. Kawai dai ina yawo ne ban san inda zan je ba" "Zaki iya shigowa ciki ki sha ruwa?" Emily ta kalleta for few seconds... "Be kamata na yarda da kowa ba" "Haka aka fada miki?" Cewar Tasmia tana murmushi. "Haka duniya ta koya min" "Da alama duniya ta rike ki a makarantarta ta yi ta zuba miki darussa a ajinta" "Haka ne, na zuba min ilmi kuma na karantu, yanzu yayewarta kawai nake jira Emily ta karasa zance idonta na cika da hawaye. Matsalar miji ce? Ko ta yaya? Ko ta family? Ya kamata na yi wata maganar dake? Emily ta yi maganar a siga tambayar. Zaki iya yarda da ni, baki ga yadda kaddara take ta hada mu ba? Wata kila tana nufin mu zama kawaye, ko kuma abokan shawara ta wani bangaren, karki damu da banbanci addininmu ba, ko launin fatarmu dukanmu mata ne, da suke dauke da matsala in one way or the other "Zan fada miki damuwata ne kawai saboda ina bukatar fashe kurjin dake min ciwo, kamar yadda na so na yi a wacan ranar da na yi miki magana, saboda bani da kawar da zan tattauna damuwata da ita, ba ni da uwar da zata ba ni shawara, bani da dan'uwa da zai share hawaye, ba ni da kowa sai ni kadai Tasmia ta zauna a kusa da ita tana kallonta cike da tausayin ganin yadda hawaye suke kwaranya a idonta. Kin rasa iyayenki ne? "Kin rasa iyayenki ne? Ni ma dai ban sani ba, mutuwa suka yi aka rasa inda za a aje ni sai gidan marayu? Ko kuma dai haihuwata aka yi ta gurbatacciyar hanya aka jefar da ni, su waye iyayena miyasa suka bar ni? Shi ya fi tsaya min a rai, ki kalli fatar jikina haskena yayi yawa, ina da blue eyes, gashin kaina ja, waya biyo mahaifina ko mahaifiyata, ban sani ba A ina kika samu kanki bayan kin girma? Su wa suka rike ki?" "Mutanen da ban sani ba, labari ne mai tsawo "Toh yanzu wa kike aure? Baki jin dadin zaman gidan mijin ne ko me da har kika tunawa da baya tunatar da ba zata miki amfani ba Ta share hawayen da suka ki tsaya mata. Wasu sun yi dacen rayuwa Tasmia, sun san su waye iyayensu, wasu sun yi rayuwa da su, wasu sun san a ina familynsu suke, wasu suna da kawaye, suna da masu kula da su, ni ba ni da kowa yarana ma basa bukata ta a yanzu" Jimmm Tasmia ta yi kamin ta ce. Yaranki suna bukatar tsawatarwa, gaskiya na lura da tarbiyar yarki sai a hankali, me zai saka ba za ku tattauna da mahaifinta... Bata karasa ba Emily ta tari numfashinta. Bana tare da mahaifinta, a yanzu ina zama a karkashin kulawa da ikon wani ne, da baya bari ma rabi kowa, baya barin na yi kawa, banbancin rayuwar baya da ta yanzu kadan ne, har yanzu a cikin kangi nake" Tasmia ta dafa ta. "Miyasa ba zaki yi nesa da shi ba? "Ba zai bari ba, saboda shi yake ciyar da mu shi yake mana komai ko da kuma na yi kokarin gina kaina ba zai bari ba" Tasmia ta juyo da ita suka fuskanci juna. "Ban san iya hidimar da yake miki ba, amman da alama akwai tsoro da fargaba a zuciyarki, irin tsoron da fargabar da yake samu kowane dan'adan mai rauni har yayi nasarar sauya tunaninsa ya saka shi a cikin wani kogo ya hana shi walwala, daga lokacin da tunaninki yake hango miki rauni a tafiyarki, zuciyarki take raya miki ba zaki iya ba, to ba zaki iya ba ne har abada, a yadda na fahimce ki kin sha wahalar rayuwa kamin yau, idan kuwa haka ne be kamata ace wani ne yake fada miki yadda zaki tafiyar da ita ba, ai babu wanda ya san kalar talkamin da suka dace da kafarki, ina nufin babu wanda yayi tafiyar da kika yi a hanyar rayuwar ki saboda kaddarar kowa dabam, idan babu mai sonki shin ke ba zaki so kanki ba? Kar tsoron sherin wani ya hana ki gina rayuwarki, ki tsaya da kafarki irin tsayin da ba za a iya kallon idonki a fada miki wata maganar ba, ki sakawa ranki zaki iya, ki yarda da kanki Emily, idan baki da kowa to ke ki zamewa kanki kowa mana, ki gina labarinki, ki yi taki duniyar ki cikata da zuri'arki" Tasmia ta karfafa mata guiwa ta zuba mata kalaman da wani be taba tsaya ya tsara mata su a cikin kanta ba, hakan ya tsayar da zubar hawayenta a yanzu tunaninta ya karkata ta inda bata yi zato ba. Karar shigowar sako ne ya sauka a wayarta sai ta sauke kanta kasa tana duba wayar. Kina ina? Ta karanta sakon na Vito. Kamin ta dago ta kalli Tasmia dake zuba mata kalamai. Ki fara mafarkinki daga yanzu, kar kowa ya sake baki tsoro, karki yarda zuciyarki ta fada miki ba zaki iya ba, tsoron cutarwa wasu ta hana ki cika burinki, ita rayuwar duniya ciki take da kalubale babu mai kaiwa karshenta sai wanda ya barta, ke kadai kika girma babu kowa a kusa da ke! To taya zaki bari wani ya milke ke a yanzu? Wani be kamata ya rubuta labarinki ba, ke ya kamata ki aje alkamin da kanki... Ki rufe tawadar sai ki bada damar a karanta... Ta karasa tana share mata hawayenta tare da yi mata murmushin karfafa guiwa. Emily ta yi murmushi still hawaye a idonta. Ke ce mutum ta biyu da na gani musulma mai zuciya mai kyau, daga wacan mutumen da ya taimaka min lokacin da zan haifi Fatima sai kuma ke, amman duk sauran daga masu gorin addini sai masu cin amana Haka muke mu musulmai cikin akwai na gari akwai bata gari, kamar dai kowane addini, idan kina son zaman lafiya da kowa da kuma fahimtar rayuwa, ki kalli addinin da mutane suke yi, da kuma abun da ya koyar, ba wai rayuwarsu ba" "Haka ne" Ta amsa tana share hawayenta. "Toh yanzu zaki iya shigowa ki sha ruwa?" Emily ta yi murmushi. Wata kila wani lokacin" "Shikenan tun da haka kika zaba, amman yanzu zaki saka min number ki zan saka miki tawa, ni da ke mun zama yan'uwa daman ni bani da kawa a nan kawata daya ce kuma sarkin kishi ce saboda mijinta bana son zuwa gidanta, ina zaune a gurin wata yayata, ke kuma daman na taba sauke ki a gidanki, amman asali ni yar Kaduna ce" "Amman ke me ya kawo ki nan" "Bautar kasa" Emily ta daga mata kai alamar gamsuwa, sannan ta saka mata numberta ta karbi nata number. Ta mike tsaye Zan tafi wata kila yarana suna bukatar gani izuwa yanzu" "Hakan yana da kyau, muje na rakaki" Tamia ta rakata har gurin motarta sannan ta yi mata sallama tana daga mata hannu har ta yi nisa. [4/26, 5:40 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 35 · 0% Book details