Sashe 128
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
haifa bayan duk wahalar daukar ciki da nakuda, saboda kawai ba ta aure aka samu yaro ba sai ka jefar? Ko a ina suke aje tausayi da kaunar da uwa take da shi ga yayanta lokacin da suke aikata haka? Kuma baka san wane hali yaronka zai tashi ba, baka san ya rayuwa zata kasance masa ba, kalli dai wannan yarinyar, yanzu ai ta daukarwa kanta hakkin yarta, wannan kiwon da Allah yake cewa ya bawa iyaye na yayansu ka ga matan da suke jefar da yayansu ba su sauke wannan nauyi ba, kuma sun jefa kansu da yayan a ciki bala'i da bakinciki, Allah dai ya shirya mana zuri'a" Aliyu ya bude ido yana kara jin tausayin Emily ya kama shi. "Amman ta hanyar banza ta same ta ko kuma dai kuskure aka samu?" "Shi ne ban tambaye ta ba" "To miye amfanin bayyana akanta a yanzu? Kuma a irin wannan lokacin da take cikin matsala? Kawai sun kunno mata wuta ta rasa ma ina zata saka kanta? Ban tashi tare da ita ba, amman dan zaman da muka yi ina jin tana yawan maganar iyayenta amman ban yi tunanin haka abun zai zo ba" "Allah dai ya saka idan ta huce ta dawo, idan kuma ta zabi tafiyar ne Allah yasa ta fada hannun kwarai" "Ameen" Ummi ta bude abincin zata fara zuba masa ya dakatar da ita. "Ummi karki zuba abincin nan, ba zan iya cinsa a yanzu ba" Ummi ta yi kamar bata ji ba ta zuba masa ba da yawa ba. "Ka daure da kai ka ci" Ya karba yana kallon mahaifiyarsa, sai kuma ya saki murmushi kadan yana jindadin da shi ta shi uwar ta kasance a tare da tare. Ya fara cin abincin yana tuna wasu kalamai da Emily ta fada masa lokacin da ya kawo ta gida daga gurin aikinsu. "Yarinyar ta yi kokari, ban san irin rayuwar da mahafiyarta ta gani ko ta ji ba daya saka ta jefar da ita, amman dai ita Emily ta tsaya tsayin daka akan yayanta, daga wanda ya mutu har wannan Fatima babu wanda bata sha wahala gurin rainon ciki da haihuwarsa ba, amman bata gudu ta bar ko daya ba, har London da yake da lalura ma, wata kila saboda ta san yadda ake ji ne idan babu kowa na su a kusa da su, saboda ita sa dandana dacin haka, ita kadai sai irin mutanen da suka tashi a irin yanayinta suke iya fahimtar yarenta, amman dai abun da na sani Emily Jaruma ce, ma manta ban fada mata wannan ba" Ya kai abincin a bakinsa ya tauna ya hade amman baya jin dandanonsa ko kadan, kawai dai yana ci ne saboda ya ranta ran Ummi. TURHAN POV. Ammy na tsaye balcony tana kallon Turhan da ya fito motar abokinsa Manir ya doso entrance cikin yanayin damuwa. "Sannu Manir an gode Allah yayi albarka" "Ameen sai da safe Ammy" Yaja motar ya wuce Ammy ta juya ta shiga falon ta zauna kusa da danta. "Ba wani labari ne?" Ya dago jiki a sanyaye, murya kamar ba tasa ba. "Babu, na yi report har gurin police, amman dai har yanzu ba ace an ganta ba, ni da manner mun zagaye rabin garin nan ba mu ganta ba, mun tafi har wata unguwa nemanta, muka kwatanta na nuna hotonta sai suka ce mana ta zo amman da dadewa kusan shekara bakwai da suka wuce, wai mahaukaciya ce sun fada mana irin rayuwar da ta yi a gurin da ciki, ina kyautata zaton bayan ta bar Sudan ne, saboda sunce tana tare da yaro" "Wata kila da cikin Fatima ne, ta fada min ta zauna a unguwanin duk suna mata daukar mahaukaciya" Turhan ya duba agogon falon dake nuna karfe 11pm ya sauke ajiyar zuciya. "Ammy na cutar da yarinyar nan, na gode da baki bar ni sai da na nemo ta, sai dai yanzu ban san wane hali zata fada ba, a ina take?" Ya soke kai kasa ya dafe cike da damuwa. Ammy ta kai hannu ta shafa kan danta. "Alhamdulillah, ka gane gaskiya shi yafi komai kyau ai, na jidadin haka, kuma In Shaa Allahu zata dawo, uwa ai bata iya tafiya ta bar yaranta, komai zai daidaita" "Ina fatan haka" Ammy ta sumbance shi, tana jin kaunar danta sosai ga kuma jikarta dake dakinta tana bachi abun burgewa. "Gobe zan bar garin nan da karfe 10am, saboda kiran da Abie yake min" "Toh Allah ya kaika lafiya ya tsare" "Amman ina son na tafi da Fatima Ammy" Ammy ta janye hannunta a jikinsa. "Aa, ba zan yarda ka sake tafiya da kowa ba, haka ka tafi da uwarta labari ya canja" Ya kalleta. "Wannan baya ne, Wallahi yanzu ba Emily ba ko dankwalinta na tafi da shi ba zan bari ya wulakanta ba, balle kuma Abunda ta haifa min" "Aa ka barta anan dai, kai ma zaka fi jin karfin dawowa" Baya son ya musa mata, dan haka ya amince ba dan ransa ya so ba ya mike tsaye yana sauke ajiyar zuciya ya haura sama, dakin Ammy ya fara shiga ya zauna bakin gadonta yana kallon Fatima dake ta bachi rumgume da teddy, ya matsa kusa da ita ya kai hannu yana shafa fuskarta, matar da ya wulakanta ya kaskantar ita ce yau ta ba shi farincikin da yake nema kuma wanda ba a siyarwa. "Wata mahaukaciya? Mai ciki? Ana tunanin cikin an mata shi ne ko kuma asiri aka mata, wacan shagon ta yi zama lokacin ba ayi gina a gurin ba" Haka yayi ta tuna yadda mutanen suka yi ta labarta masa Emily. Ya kai bakinsa ya sumbanci Fatima hawayensa ya zuba a kan fuskarta. [7/25, 8:28 PM] : https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 ABOKIN RAYUWA