Sashe 6
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Teburin dake office din ta nufa ta dora file din da Amal ta bata, tana karewa karamin office din da be karasa girman na amal ba kallo. Sannan ta nufi windows ta bude tana kallon kasa, iska mai dadi na shigowa office din. Ta dade tsaye a haka sannan ta matsa baya ta rufe, ta nufi gurin da durowar office din take ta fara budewa tana dubawa, kusurwar farko an rabata biyu ne da wani katako tsakiya, daga sama an dor Kur'ane daga kasan kuma Bible, doka ce ta sabon CEO na yanzu, aje Qur'ane mai fassarar turancin, da Bible a kowane office a kokarinsa na son tallata addininsa, ta dayan bangaren kuma gudun complain ya saka yake aje Bible din domin baya kowa hakkinsa, sai idan baka bujata sai ka yi magana a dauke. Risinawa ta yi ta rage tsawonta ta taba Bible din da hannunta na dama. Wani bangare na maganar da Momy ta yi mata ya dawo mata sabo a yanzu. _Emily karki bari yaron nan ya yaudareki, kar kyaunsa ya ja ki ga halaka, domin bayan kyaun ban ga wani abu da yake da shi ba, mun fi shi arziki a gidan nan, zaki samu miji mai kudi mai komai ba, zan inganta rayuwarki ni da mijina, please karki kunyata mu, abun kunya ne ace kina gidan Pastor kin bar mu kin bi musulmi, karki lalata rayuwarki da kananan shekarunki please Emily, ki rike wannan Bible din ki yi karatu bana son na sake jin maganar yaron nan, kin ji my beautiful Diamond Girl_ Ta dauke hannunta da sauri tana hawaye, ta rufe durowar ta juya ta zauna a gurin ta jingina da ita sai kuma ta fashe da kuka, jikinta na karma kamar wanda ta firgita. Hamza ka cuce ni... Ka cuce ni... Ka raba ni da matar da ta rike a matsayin a, kasa na butulcewa macen da suka rike ni da amana Ta girgiza kai.. Ta dayan bangaren ba laifinsa take gani ba, laifin zuciyarta ne data barta ta fada soyayya da mutumen da be san darajar addininsa ba balle ita. Wani irin duka ta kai kirjinta tana jin kamar ace zata iya ganin zuciyarta a fili ta yi mata duka. Tuna cewar ba a gida take ba ya saka ta natsu ta sassauta kukan da be gama fita ba, ta hade kanta da guiwa. Ta dauki lokaci tana rarrashin kanta sannan ta mike tsaye ta dauki file din ba tare da sake taba komai ba ta fice daga office din ta rufe kofar da key ta nufi hanyar da zata sadata da elevator. Babu abun da take a cikin elevator sai tunanin yadda rayuwa tayi da ita. Har ta isa first floor bata hankara ba sai da kofar ta rabe biyu, ta fita ba tare da ta lura da mutanen da suke tsaye suna kokarin shiga elevator ba. Daya daga cikinsu ya biyo bayanta a sirance har sai da ta yi rabin gate din dake da tsayi sosai. Excuse me Miss Ta juyo ta yi sai ta yi arba sa wani bakin mutum bayanta yana sanye da yellow t-shirt da black jean. Can i help you? Ya matsa kusa da ita. Kin shigo neman wani abu ne? Ko kina daya daga cikin team din Resrezor? No na fara aiki a nan ne Yaushe? A ina? Wane guri office dinki yake? Four floor hannun hagu office na biyu Nice to meet you, I'm William, ina 5 floor office na hudu Ta mika masa hannunta kamar yadda ya mika mata nasa. Emily Nice to meet you Emily, kin samu aboki yanzu Ta yi murmushi tana kallon sarkar Cross din dake wuyansa hakan sai ya saka ta ji dadi ganin kirista ne dan'uwanta. Har kin tashi ne? Okay Bye Ta yi murmushi ta juya ta cigaba da tafiyarta. Shi kuma ya tsaya a gurin yana kallon yadda wandon jikinta ya dame jikinta yayi mata kyau. Wow... Ya shafa kansa sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Ta isa gida da wuri saboda ta samu abun hawa da wuri, sai da ta sallame shi sannan ta kwankwasa kofar gate din. Mai gadin ya bude mata ta shiga tana amsa gaisuwarsa. Tura kofar falon ta yi ta shiga sannan ta rufe ta cire talkamin kafarta ta saka na falon sannan ta karasa ciki. Ganin kwalbar giya aje a tsakiyar center Table din dake falon ya karantar da ita V ya bar gidan cikin bacin rai, domin abu ne da ta sani, idan ransa ya bace giya yake sha ko marijuana. Da sauri ta jefar da Jakarta da file din hannunta ta nufi dakin da London yake ta bude gabanta na faduwa, ta duba dakin har bandakin baya ciki, hakan ya saka hankalinta ya kwanta domin shan abun maye ko drugs abu ne da bata son yana yi a gaban yaranta, wannan yana daya daga cikin dalilin da ya saka ta zabi raba gida da shi, ta zabi rayuwa ita kadai sai yaranta. Fitowa ta yi ta dawo falon ta dauke kwalbar ta shiga Kitchen ta tsiyaye ragowar barasar dake ciki ta fasa kwalba ta zuba a dustbin sannan ta wanke hannunta ta fito. A gurin da ta jefar da jakarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, tare da daga kanta tana kallon rufin falon zuwa gurin da katon plasma ta yake. Ta sani ahalin yanzu bata rasa komai ba sai kwanciyar hankali, Vito ya jika da kudin da bata jin akwai wata mace mai tarin dukiya irinta, ita kanta bata san adadin abun da ke account dinta ba, domin kowane sati sai ya saka mata kudi ita da yaranta London da Fadima duk kuwa da kasancewar karamar yarsa Fadima bata son shi, amman be taba kula haka ba saboda yana matukar kaunar mahaufiyarta. A cikin gidan da take rayuwa gidane da ko wucewa kawai ka yi a gaban gate din sai hankalinka ya tashi saboda kyaunsa, shi kansa nasa gidan be kai nata kyau ba, ya zuba mata kayan more rayuwa daga sutura har abubuwan ado na kawata falo ko daki, ga mayan motoci da ya zuba mata a cikin gidan, ga Nannyn da ya dauka mata mai kula da yaronta, ya saka yarta a makarantar kudi ta yayan manya, London kuma da ya kasance Autism ya biya ake karantar da shi a gida. Bayan kudin da ya biya aka yi mata aiki, ya kaita waje ta yi karatu. Amman duk da haka tana jin ta rasa wani abu a tare da ita, she felt something is missing inside her. Ji take bata cika ba har yanzu, tana jin akwai abun da ta rasa kuma bata san miye wannan ba, sai dai ta san dalili daya da ya saka take son tsayawa sa kafafuwanta, wannan sirri ne da ba zata iya budewa kowa shi ba. Good Afternoon Ma Cewar Chidimma bayan ta shigo falon. Emily ta kalleta da irin fuskar nan na wanda tunani be gama sakin kansa ba. Chidimma, a gaban London V ya sha alcohol dazun? Aa bayan na shiga dakin Landon ne na canja masa tufafi saboda za su fita tare Ta sauke numfashi a hankali. Okay please duk yadda za'ayi karki bari yarana su ga lokacin da Vito yake shan giya, balle har hannunta ya kai gurin Okay Ma zan kiyaye Ki shirya musu wani abu ni zan yi bachi Tana fadar hakan ta mike tsaye ta dauki jakarta da file din ta haura sama ta shiga dakinta ta aje jakar da file din a kusa da gadonta ta kwanta, tunani ya fara kawo mata ziyara kamin bachi yayi gaba da ita. ALIYU POV. Dagowa yayi a hankali ya kalli kofar office din da aka turo. Mutumen ya karaso gaban teburin cike da girmamawa ya bude masa daya daga cikin files din da suke hannunsa. Nan zaka saka hannu Sai da Aliyu ya gama abun da yake a computersa sannan ya kalli file din ya saka hannu. Ranka ya dade cikin sabin ma'aikatan da aka dauka har da turawa? Cewar mutumen dake tsaye gabansa, shi dai be ce komai ba, har sai da ya gama saka hannu a duka files din. Na ganta zata fita dazun Aliyu ya sake dubansa ba dan ya fahimci inda zancensa ya dosa ba. Baka ga sabin ma'aikatan na mu ba Ba ni nake da hakkin ganinsu ba, ban san suwaye aka dauka ba Wata baturiya ce fara kyakkyawa har ta fika haske ga blue eyes Aliyu ya dan yi jimmm alamar nazari can kuma sai yayi murmushin da ya kara masa kyau. Ka ganta kenan? William, na ganta and what? Tana da kyau, ga fari duk yadda aka yi wannan yarinyar baturiya ce ko half cast, na gode da ka dauketa, and finally kirista ce yar'uwata Ka godewa Amal aikinta ne not mine, ni ban san su waye aka dauka aiki ba ma Ya aje zaren zancen a daidai lokacin da wayarsa ta ringing. Kallon wayar yayi yana murmushi. Shiyasa ake daudararku koda yaushe kyaun kuke bi ba hali ba Ya amsa kiran ya kara wayar a kunnensa, at the same time da William yake fadar. Ka rantse da Allah ka na musulunci cewar ka taba ganin yarinyar da ta fita kyau? Ni fa rudewa na yi na kasa rike kaina sai da na yi mata magana Da sauri Aliyu yayi saurin yi masa alama da hannu na yayi shiru ya yi tafiyarsa. William zip up his mouth yayi ta tafiyarsa. Hello yar kyakkyawata Na'am ya aikin? Alhamdullahi ya cikin? Ban sani ba Ya saka dariya daman da neman magana ya saka shi tambayarta. Miye laifina dan na tambaya? Ni dai ban sani ba, kawai dai na kira na fada maka Gwaggo ta kira tace Anty Sa'ade ta haihu Maa shaa Allahu, me muka samu? Irina ce aka samu Ki ce irinki marar jin magana ko? Ya fada yana wani abu da ido kamar tana gabansa. Ba zaka daina ba ko? Na daina yar shawalwalar yarinyar yar dirarar yar black beauty na kyakkyawata Ta yi dariya. Bye sai ka dawo Okay mai ciki Yana fada ya kashe wayar da sauri yana dariya, sannan ya aje wayar ya maida hankalinsa gurin aikinsa. TURHAN POV. Ya aje mug din tea dake hannunsa. Yadda kasan yarinyar nan ta