Sashe 114
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 5 Ummi na falo tana ta gaisawa da mutane yan'uwa da abokan arziki da suka zo mata jaje sai ga Mama Barakat ta shigo falon da sallamata tare da rakiyar yarinyarta ta biyu. Ummi na ganinta ta dan daure fuska kadan domin ta san zuwanta ba zai wuce saboda Kameela ba, sama sama suka gaisa da Ummi sai Ummi ta maida hankalinta gurin sauran baki bata sake bi ta kan Mama Barakat ba har sai da Mama Barakat ta gaji da zama ta ce. "Hajiya gurinki na zo" Ummi ta maido da hankalinta gurinta sannan ta mike tsaye ta nufi wani dakin baki dake falon ta shiga tana fadin. "Bismillah Hajiya Baraka" Ummi ta fara shiga ta zauna sai ga Mama Baraka ta shigo ta zauna kan kujerar dake dakin. "Na katse ki kina da baki, na tafi asibiti ai aka ce kin zo gida kuma ba su yarda na shiga na duba Aliyun ba" "Eh ana son ya huta ne, kuma saboda abun da ya faru da shi ya saka ake ba shi tsoro dole a san suwa suke shiga da fita" "Allah sarki, Allah ya ba shi lafiya kuma ya tsare gaba, mu ma a gari muka ji abun da yake faruwa" "Ameen Ya Rabbi" Daga haka sai shiru ya biyo baya, Mama Barakat bata sake cewa komai ba hakan ya saka domin ta yi tunanin wata kila ta zo nan ne amadadin mahaifiyar Kameela, dan haka Ummi ta tari hanzarinta tun kamin ta fara magana. "Hajiya Baraka Allah dai ya sa ba kin zo maganar Kameela ba ne, domin dai yanzu Aliyu yana bukatar hutu da kwanciyar hankali, kuma iya hakuri ni dai na yi a matsayi na uwarsa na dauke ido iya yadda zan iya, yanzu kan abun ya wuce duk inda ake tunani ba kuma zan yarda ta kashe min ana ba saboda kishinta na banza. Abun ya kai har ta saka masa guba kin ga ai ba so ba ne ba kuma kishi ba hauka ne" "Subhanallahi, guba fa kika ce Hajiya" "Da bakinsa ya fada min, shi ne dalilin turo ta gida da yayi ai, amman be fadawa kowa ba sai a yanzu da ta kai shi makura, kin ga yanzu ko za su zauna da junansu ni ba yarda zan yi ba, ba zai yiyu su da aure ni da zaman zullumi da fargabar me zai faru ba" "Ban taba ji wannan, amman Kameela bata yi ma kanta adalci ba, Subhanallahi, ni ba ma zancen ta ya kawo ni ba, Wallahi ba dan kowa na zo ba sai dan yarinyar da aka ce saboda ita Aliyu ya saki Kameela, shiyasa na tafi asibiti aka ce baki can na tambaya dan Allah ita Emily tana tare da shi ne na kwatanta musu ita suka ce min kun taho tare" "Emily? Toh Allah yasa ba daga mata hankali za'ayi ba, domin yarinyar nan tana cikin damuwa, kuma kamar amana take a gurina" "Haba Hajiya ni ma fa Uwa ce, ta ina zan nemi daga hankalin wata ya? Magana kawai nake son yi da ita, saboda ina tunanin kamar ita ce yarinyar da aka taba hada mu da ita a lokacin da muka je Abuja, na zo da ita har Kaduna sai ta gudu bata tsaya ma na taimaka mata ba" "Allah sarki Ashe kin santa" Nan Hajiya Barakat ta labarta ma Ummi farkon haduwarsu da kuma dalilin haduwa. "Toh ki haura sama, tana nan daki na farko hannun hagu" "Toh na gode Hajiya" Mama Barakat ta tashi tare da Ummi suka fito Ummi ta koma gurin Mutanenta Mama Barakat kuma ta nufi upstairs ta haura sama ta bi hagu da ita kamar yadda Ummi ta fada mata, dakin farko ta fara turawa a hankali ta leka sai ta hango Emily zaune kan gadon Aliyu tana rutsar kuka a hankali marar sauti. A take zuciyar Mama Barakat ta kara karyewa daman ta shigo gidan zuciyarta cike da rauni, ta shiga ciki gaba daya ta maida kofar ta rufe karar rufe kofar ya saka Emily ta kalli kofar sai ta yi hanzarin takaita kukanta ta sauke kanta kasa. Mama Barakat ta karasa cikin dakin ta zauna bakin gadon tana kallon Emily babu shiri hawaye suka zubo mata, yadda Emily ta takure guri daya ya bata tausayi sosai. "Ba lallai ki gane ni ba, sunana Mama Barakat, mun tana haduwa da ke a lokacin da kika bar Sudan Mrs Deborah ta zo da ke, sai tace na zo da ke Kaduna saboda kin fada mata a nan kike, kamin ayi bincike ba ki ma zauna a gidana sai kika gudu ko kin gane ni?" Emily ta kalleta da kyau ta daga mata kai, daman tun farkon shigowarta ta ga alamar kamar ta taba ganinta. Cikin kuka Mama Barakat ta ce. "Meyasa kika gudu? Me yasa baki tsaya ba? Wata kila da yanzu baki shiga cikin wata damuwa ba, baki yarda da ni ba ne a lokacin? Na yi tunanin ke musulma ce a lokacin?" Emily ta kalleta hawaye na sauko mata. "Gaba daya ni a yanzu ban fahimci rayuwa ba, ban gane me take nufi da ni ba, daga wannan sai na fadawa wannan, idan har iyayena ko yan'uwana ba za su iya rike ni tun a lokacin da ban san komai ba, bana tunanin akwai wanda sai rike ni na samu mafita, bayan barin gidanki abubuwa da yawa sun faru, a lokacin na samu gata kuma ina da yarana har biyu, sai ga shi kuma rayuwa ta sake juye min ta kawo ni nan, babu gatan babu uwa ba uba ba babu yaran, dayan ya mutu dayan an karbe, ni yanzu na kasa fahimtar komai" Ta fashe da kuka, Mama Barakat ta matsa kusa da Emily ta rungumota ta kwanto da ita jikinta ita ma ya fashe da kuka mai karfi wanda ya fi na Emily shiga zuciya da sosai rai, ta rumgume Emily sosai tana shafa kanta. Emily ta lafe a jikin Mama Barakat daman tana neman wanda zai rumgume ta kamar haka a yanzu, sai duk ta ji kewa da son kasancewa da tata uwar duk da yake bata taba sanin ya dadinta yake ba, amman ta sani idan har akwai iyaye a tare da ita ko yan'uwa na jini wasu abubuwan za su zo mata da sauki. "I Need my own parents, ni mace ce kawai mai son iyayenta da yan'uwanta a kusa da ita, why all this? Me na yi musu? Me na yi ma rayuwar? Me yasa kaddara take ta juya ni haka? Na gaji na gaji na gaji" Tana maganar tana kuka mai ban tausayi ta takure sosai a jikin Mama Barakat kamar zata shige jikinta, bankarewa Mama Barakat ta yi ta daga kai sama tana ta yaki da numfashi da kuma kukan dake son sakata ihu, hawaye suka rika sauko mata ta gefen ido wasu na bin wasu. Sai da ta kai ruwa rana tsakanin kukanta da numfashinta sannan natsuwarta ta samu daidaituwa, ta maido idonta akan Emily ta shafa kanta. "Na samu labarin abun da ya same ki a yanzu nw ta gurin Kameela saboda sakin da Aliyu yayi mata na abu...." Mama Barakat bata kai aya ba Emily ta daga daga jikinta da sauri ta matsa baya. "Fita dakin nan" Mama Barakat ta girgiza kai da sauri. "Ba ki gane ba ne, bana goyon bayan Kameela ina tare da ke ne..." "Ki fitar min daga nan, bana son Kameela bana son duk wani abin da ya shafe ta, fita yanzu nan" Mama Baraka ta mike tsaye ta dauki jakarta kamar mai tsoro jikinta har rawa yake. "Tohm, zan fita amman idan kina bukatar wani abu ko taimako zaki iya tuntuba ta, kuma zan kasance kusa da ke daga yanzu In Shaa Allahu, idan kina bukatar wani abu ki fadawa Aliyu zai fada min yana da number wayana" Ta nufi kofa tana yi tana juyo ta kalli Emily har ta fice, sai da ta tsaya ta share hawayen ta sannan ta sauko jiki babu karfi murya kuma ta sauya ga ido ma be isa ya karyata cewar ya zubar da hawaye ba. Ta sauko tana ta masa kasa da ido bata son hada ido ta mutane saboda bata son kowa ya gane ta yi kuka, amman hakan be hana Ummi tambayar lafiya ba bayan ta tambaye ta sun gana. "Eh mun yi magana da ita" "Allah yasa dai lafiya, yanayinki kamar ya canja Hajiya Barakat" "Lafiya kalau, dan Allah zan iya samun number mahaifiyar abokin Aliyu nan a gurinki? Domin na kira Aliyu be daga ba, na manta sunan abokin nasa dai amman wanda aka kaiwa yarinyar ta Emily" "Oh Turhan? Eh ina da number mahaifiyarsa" Ummi ta kai hannu ta dauko wayarta ta kamo number ta karanta mata, Mama Barakat ta saka sannan ta yi mata godiya ta yi mata sallama ta fice tare da yarta wacce ta rakota. Fitar Mama Barakat mutane suka ragu har Ummi ta samu damar amsa waya daya daga cikin mutanen da suke kiranta, sannan ta haura sama ta yi wanka ta sauko domin shiryawa Daddy wani abu kamin ya iso, daman bata yarda mijinta ya ci abincin kowa sai ita, sai idan bata gida ko kuma wani babba uzuri ya sha gabanta. Tana Kitchen tana tsaka da girkin ne ta ji sallamar Ammy, sai ta rage wutar gas din ta yi kasa sannan ta fito. "Maraba da Hajiya Maijidda, yau Ammy ce a gidan na mu" "Ni ce Ummi, fatan mun same ku lafiya" "Toh Alhamdulillah, ya gidan ya kwana biyu" "Sai godiya, ya Aliyu da jiki? Ashe haka abu ya faru? Tohm Allah ya saukewa ya tsare gaba" "Ameen Ameen, ashe kun ji" "Eh ai kin san abu irin wannan yana saurin yado, balle kuma wayarsa tana gidanmu gurin Fatima, to yawan kiran da ake ne nake amsawa ta nan na ji" "Oh ashe wayar tana tare da ku, ikon Allah to yarinyar take?" "Tana nan lafiya kalau" "Maa Shaa Allah, tohm bari na duba girkina" "Tsaya dai tukuna Ummi na zo nan saboda mu tattauna abubuwan da suka faru" Ummi ta koma ta zauna. "Toh kamar me kenan?" "Haba ki daina yin kamar baki san komai ba mana, Aliyu be fada miki abun da ya aikata