Sashe 116
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 5 Cikin kuka da shesshekar kuka Emily ta karasawa Ammy labarin irin zaman da ta yi a Sudan da kuma rayuwar da ta biyo bayan zamanta a can, yadda ta hadu da Vito ta canja addini har zuwa haduwarta da Aliyu da irin rokon da ta yi masa na kar ya sanar da Turhan inda take, Emily bata boye mata ba, ta fada mata har auren nw ta yi ne saboda ita ba dan tana son Turhan ba. Ammy yaja numfashi da nauyi ta sauke hawaye na sauko mata kuka take sosai tata rayuwar take tunawa, yadda abubuwa ta yi zama da mahaifin Turhan. "Zuciyata ta raya min dole akwai abin da yake faruwa da ya saka kika gudu kuma kika bar min wannan sakon, amman ban taba tambayarsa wane irin zama kuka yi da juna ba, ni dai damuwata na yadda za a gano ki ne, wannan dalilin ya saka na daga hankalin Turhan na sauya masa fuska, na yi duk yadda uwa zata yi idan ta rasa yarsa, kin san saboda me? Saboda na gane shim Turhan mai biyayya ne a gareni? Kuma saboda ya nemo ki, ban manta lokacin da kika fada min baki da kowa ba, ina yawan tuna wannan, kuma ina jin wata kila idan na taimake ki zan iya samu aljannata ta nan, ashe ma akwai jinina a tare da ke, na aura miki Turhan ne saboda ni da ke mu samu mafita, ke ki samu miji mai nagarta mai kulawa, ni kuma na samu ana da zuri'arsa a kusa da ni, amman na yi kuskure, na jahilci ana, na yi zaton zai riritaki ne, ashe yayi miki rikon da kadan ya banbanta da wanda mahaifinsa yayi min" Ammy ta kai hannu zata taba Emily sai Emily ta matsa tana hawaye. "Baki fahimce ni ba ne Aisha, amman har gobe baki da wata uwa sai ni, ban yi nufin cutar da ke ba, na hada aurenki da Turhan ne saboda ina tunanin zai so ki, na duba kyanki a lokaci da yadda siffarki ta banbanta da yayan hausawa, wai ina zaton haka zai daga kimarki a gurinsa, sama da ace bakar fata na aura masa, na so ki kamar yar da na haifa a cikina, har gobe ni uwarki ce" Emily ta kalleta. "Zan tabbatar da hakan ne kadai idan kika saka anki ya sake ni!!! Idan kika yi haka zan tabbatar kin dauke a matsayin a!" Ammy ta hade yawu da karfi ta yi jimmm na dan lokaci kamin ta sake hade yawun a karo na biyu ta daga kai. "Zan tabbatar miki da haka Aisha, ba zan so yarki ta tashi da iyaye a rabe ba, ke kin san zafin haka, haka kuma na so ki da jinina na yi nufin yanzu mu kyautata gareki, amman zan shure komai saboda farincikinki zan miki yadda kike bukata" Ammy ta mike tsaye ta dauki jakar har ta fara tafiya sai kuma ta juyo. "Zan roki alfarma daya, karki cusa tsanarmu a zuciyar Fatima, haka kuma ba zan iya shiga tsakanin uwa da a ba, ba zan iya yanke hukunci akan Fatima ko Turhan ba, amman dai a tsakaninku ni na hada kuma zan raba, na barki lafiya" Ta juya ta cigaba da tafiyarta har ta isa bakin kofar ta bude ta fice, ta sauko kasa kenan ta hadu da Ummi da zata hauro sama. "Kin fito?" Ammy ta kalli Ummi ido cikin ido. "Eh na fito, Turhan zai saki Aisha zan tabbatar mata da cewar tabbas a ya na dauke ta, idan ya sake ta sai Aliyu ya aureta, na barki cikin amincin Allah" Ammy ta nufi kofa ta bar Ummi tsaye da mamaki tana kallonta har ta fice. Ummi ta haura sama ta tura dakin Aliyu da Emily take ta leka sai ta hangota tana kuka. "Ke haka zaki zauna kullum kuka kuka? Shiga ki wanke fuskarki ki fito muje kitchen" Emily ta mike tsaye ta shiga bandakin ta wanke fuskarta ta fito Ummi ta rike mata kofa ta fito suka sauka kasa, Kitchen din suka nufa ba dan ran Emily ya so ba sai dan Ummi ta bukata, a tare suka karasa aikin sai da suka jera komai a dinning sannan Ummi ta kalleta ta ce. "Kina fifita farincikin wasu akan naki, kina fargaba tunkarar wasu da abun da yake zuciyarki, shiyasa kika cutar da kanki, ko da yake ta wani bangaren ba laifin ba ne, kin tashi ba tare da kowa ba, duk wanda ya rasa iyaye ko ya tashi a maraya farincikinsa ragagge ne, a kullum yana tsoro ko fargabar rasa farincikin wani fiye da nasa, ko da yaushe kina jin ke baki da amfani wasu ne masu amfani, karki sake tsorata ko cilasta kanki abun da ba shi kike bukata ba, aikim nan da muka yi ranki be so ba ni na sani, amman kin kasa fada saboda kar raina ya bace" Emily bata ce komai ba idonta dai ya cika da hawaye. Ummi ta dauki cup ta zuba ruwa "Shiga dakin ki wanka, Nafisa zata kawo miki wasu tufafin ki saka kamin a siyo miki irin wadanda kika saba sakawa, idan kin ci abinci sai ki kwanta ki huta" Emily ta juyo ta fara tafiya, sai Ummi ta aje cup din hannunta ta fasa shan ruwa ta kira sunan Emily. "Emily" Ta sake juyowa, Ummi ta karasa kusa da ita ta rumgumeta, sai Emily ta rike ta fashe da kuka sosai, Ummi ta rika shafa bayanta tana jin tausayinta sosai karamar uwa ce da takw bukatar uwa a kusa da ita, kuka sosai Emily ta yi har ta karya zuciyar Ummi da tausayinta, Ummi ta zubar da hawaye tana mamakim yadda wasu uwa ko yan'uwan suke juyawa abun da aka haifa baya har ya rasa gata, alhalin ba su san halin da yaran suke samun kansu ba. Sai da Emily ta samu natsuwa a kafadar Ummi sannan Ummi ta share mata hawayenta. "Shiga ki huta, za a kawo miki abinci" Ta daga kai ta fice daga Kitchen din ta haura sama, Ummi ta kalli Nafisa daya daga cikin yan matan da take riko ta ce. "Ki zuba abinci ki kai mata, a fadawa Kulu ta shirya mata wani abu mai ruwa ruwa ko zata iya sha, wacan abincin kuma ki kaiwa Aliyu idan kin je ki fada masa sai Daddynsa ya iso za mu zo" "Tohm Ummi" Daga haka ta haura sama, Nafisa ta debi abincin ta kai dakin Emily sannan ta sauko ta fita harabar gidan neman Kulu, bayan ta sanar mata umarnin Ummi ta sake dawowa falon sai ta samu Ummi na jiranta. "Ungo ga wannan tufafin shigar mata da shi, ki je ki kaiwa Aliyu abinci yanzu nan" "Tohm" Ta karbi tufafin ta shigar da shi dakin Emily sannan ta fito ta saka mayafinta ta dauki abinci ta fice, Direban da ya kawo Ummi ne ya dauke ta zuwa asibitin bayan sun isa ya rika mata kayan har gurin dakin da Aliyu yake ba abar shi ya shiga ba dan haka yace ta fadawa Aliyu yana gaishe shi, ta amsa da Toh ta shiga ciki. Ta shiga ciki sai ta same shi zaune akan kujera yana tasbihi da alama sallah ya gama. "Sannu Yaya Aliyu ya jikin?" Ya daga mata kai sai da ya shafa addu'a sannan ya amsa. "Alhamdulillah" "Ga abincin ka, Ummi tace na kawo" "Ni zan iya cin abinci yanzu na sha tea ma babu jimawa, maybe zuwa anjima zan iya ci" "Tace a fada maka sai Daddy ya iso za su tare" "Okay, Ina Emily?" "Tana can gida tare da ita aka maka girkin ai" Aliyu ya kalli cooler abinci mai kyau da tsada da Ummi ta siya gurin Khadeeja Candy. "Zuba min abinci" Nafisa ta bude Warmers din ta fara zuba masa soyayyar shimkafa da kaza sai kamshi take. "Yauwa Khaleefa yace yana maka sannu da jiki" "Wane Khaleefa?" "Direba?" "Da shi aka zo daga Abuja?" "Eh shi ya kawo ni yanzu" Ya karbi abincin ya fara ci yana taunawa a hankali. "Idan kin tafi ki fadawa Khaleefa nace ya je kauyensu ya huta na kwana biyu har sai an neme shi, ita kuma Ummi ki fada mata na bawa Khaleefa hutu" "Ka kore shi kenan?" "Aa ai ba zan hana shi hanyar cin abincinsa ba, but for now bana son Emily ta ganshi ranta ya bace, yaje ya huta za a rika biyansa har sai idan Ummi ta bukaci a daina tun da Direban ta ne ba nawa ba" "Okay" "Idan kin koma ki shiga gurin Emily make sure ta ci abinci please, kuma ku rika janta da hira kar a wareta, ko nuna mata banbanci ku rika janta a jiki Please" "Okay" Ya kalli wayarsa dake kan gado tana ringing, Nafisa ta dauko ta miko masa ganin sunan Mama Baraka ya saka shi kallon Nafisa ya ce. "Zaki iya tafiya, Muktar yana nan zai min komai idan ina bukata" "Okay Allah ya baka lafiya" "Ameen" Ya amsa ya aje wayar kan cinyarsa ya cigaba da cin abincin a hankali. TURHAN POV Yana harabar gidan yana video call Fatima a hannunsa sai waving take yi ta gaban wayar, ganin direban Ammy ya saka shi sauke wayar ya nufeta Fatima na hannunsa. Ammy ta fito motar cikin wani yanayi da ke bayyana damuwarta amman hakan be hana da ta kalli Fatima ta yi murmushi ba, ta kai hannu ta karbeta daga Turhan kamar wata yar jaririya, Turhan ya karbi jakar Ammy ya bi bayanta suka shiga falon. Sai da ta fara zama sannan ya zauna Ammy ta sumbanci goshin Fatima ta sumbanci hannunta ta shafa kanta tana murmushi. "Tafi can dakina dake sama ko kuma gurin wayar da Aliyu ya baki zan yi magana da Dadynki" Fatima ta juya ta kalli Turhan dake murmushi ita ma ta yi murmushin jindadi ambatar daddynta da Ammy ta yi ta sauka kan cinyar Ammy ta nufi upstairs, daga Ammy har Turhan binta suka yi da kallo sai da ta haura, sannan Ammy ta kalli Turhan. "Kana kama da mahaifinka sosai, ko kadan ba ka yi kamada ni ba, a kamanni da hali duk baka rago shi ba" Turhan ya fadada murmushinsa yana zaton Ammy zata yabi mahaifinsa ne. "Shi ma