Sashe 131
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 WATTPAD https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy Page 5 Turhan ya zube a gaban mahaifinsa ya gaishe shi, mahaifinsa yayi kamar be san da shi a gurin ba, bayan mintunan da suka bata a zaune wata kalma bata shiga tsakaninsu ba, Turhan ya yankw shirun ta hanyar sake mika gaisuwarsa ga mahaifinsa a nan ma be tanka shi ba. Bayan tsawon lokaci mahaifin ya mike ya shige wata turakar tashi, Turhan ya tashi ya koma bangarensa ya samu balarabiyar matarsa kyakkyawa kamar shi tana zaune cikin bahon wanka tana shuda jikinta da kumfan shower gel mai kamshi. Ya karasa kusa da ita fuska babu wata walwala ya sumbanci goshinta kamar yadda ya saba, cikin farinciki da zumudi ta mike tsaye ta rumgume shi tana masa barka da zuwa. "Ban yi tsammanin dawowarka yanzu ba, ya Ammyn take?" Ya kalleta kawai yana murmushi a zahiri a badini kuma yana hango dalilin Ammy ne aura masa Aisha, tun da yake da matarsa bata taba sha'awa tafi gaishe da mahaifinyarsaba, ko a waya sai idan shi ya hada su take gaisawa da ita, ya taba mata tayin tafiya Nigeria sai ta nuna bata da bukata be sake maimaita bukatar hakan a gareta ba, kuma a wacan lokacin baya ganin illar hakan sai yanzu da ya fi fahimtar muhimmancin mahaifiyarsa... Ya sake ta juya ya fice hakan sai ya bata mamaki domin be saba ganin jikinta a haka ba ba tare da nuna shaukinsa akai ba, amman yau tambayar ma be amsa ba, a take ta wanke jikinta ta daura tawul ta dayan kuma ta daure kanta ta fito daga Bathroom din ta bullo corridor domin babban bandakin dakinsu ba a daki yake ba a mahadar hanyoyi ne dake tsakanin dakunansu. a ranar dai kam Turhan be samu magana da mahaifinsa domin baya amsa ba. Karamin falon ta fara leka bata ganshi ba sai ta dawo corridor ta shiga dakinsa. "Turwhan... Kana lafiya kuwa?" Ta karasa inda yake tsaye yana cire rigarsa tana kallonsa. "Wata kila gajiya ce, amman idan na huta zan mu wata magana" "Tana da muhimmanci ne har ka bata rai haka?" "Zan ki iya hada min wani abu na ci?" "Shaghala (Mai dafa abincin) zata hada maka" "Shukuran" Ya saka bathrobe ya fice ya barta a dakin, tana mamankin yanayinsa a yau. Da dare ma sai da ya koma bangaren Mahaifinsa nan ma be yi magana da shi ba. Haka ya dawo bangarensa ya zauna a inda suka saba cin abincin shi da matarsa ya samu an jera abinci a kasan wani farin kyalle da aka shimfida ta zauna ya hade kafafuwansa yana kallon kayan marmari da ka'ida ce kullum sai an aje tare da sweet kala kala. Be ankaro ba ya ji an zauna kusa da shi matarsa ce fuskarta dauke da murmushi tana kamshin EOS Khumra Al Dufra Perfume Oil. Ya juyo ya kalleta tana sanye da thobe (or toob / toub / ), wata kafaya ce ta al'adar larabawan Sudan, sai ya sakar mata murmushi ya kama hannunta ya rike. "Kana cikin damuwa ina iya ganin haka daga gareka, ina lura da irin wannan yanayin a duk lokacin da ka dawo daga Nigeria, amman na yau na musamman ne" "Na kan dawo da damuwa ne saboda neman mafitarta wata hanya ne, a yanzu kuma na samu karshen ta amman ta kasa bullewa da ni" "Ina gane ko wace kalma da yaren larabci amman ban da tsarke magana a cikin wata magana, fada min Habibi me ya same ka?" Ya juyo ya fuskance ta da kyau. "Ina fatan zaki fahimce ni kuma zaki min uzuri, lokaci yayi da ya kamata ki san komai..." Sannu a hankali Turhan ya yi mata shimfidar da zata mikar da ita zuwa cikin ajinsa har ta dauki karatunsa, tun da ya fara bata ce masa uffan ba har ya kai karshen littafin data kasa fahimtar haruffansa balle ta haddace karatun ciki. Ya fada mata ya aure wata mata matar kuma ita ce wanda ya zo da ita a matsayin baiwa haka kuma ya sake ta a yanzu amman zai dawo da aurensa da ita, haka zalika yana da ya a tsakaninsu, sannan ya fada mata yawan zuwan da yake Nigeria har ya dade yana zuwa nemanta ne. Da farko zancen ya rikice mata ne har ta rasa muhallin dorashi kamin hankalinta ya janyo tunaninta bayan ya nuna mata hoton Fatima. "Mabsoot bikhibalak" Ta furta tana jefar da hannu idonta ya fara tara hawaye. "Ka ci amanata Turwhan, taya zaka yi aure bayan idona? Saboda bana haihuwa? Ko kuma saboda mahaifiyarta bata so?" "Ki zargi komai ban da mahaifiyata, domin bata taba nuna miki kiyayya ba, matar da baki taba sha'awar gani ba?" Ta tsaya cak tana kallonsa kamin ta mike tsaye ta taba masa. "Barakallahu fika Turwhan" Ta juya sai yayi hanzarin mikewa tsaye ya rike ta. "Idan har zaki ji babu dadi wannan abun da na aikata ki yi tunanin yadda matar da na wulakanta zata ji? Kuma na yi ne ba dan kai na kadai ba har da ke?" Ta juyo da karfi. "Idan har baka sonta taya ta haihu da kai? Bayan duk wannan yanzu kuma kana fada min zaka dawo da ita? A tunaninka zan iya zama da kai bayan duk wannan abun da ka yi min? Balle kuma har zaka zauna da matar da bata wuce matsayin mai kula da gidana ba? Aure ya kare tsakanina da kai. "La la la, khalas al-mawdu intiha. Ana ayza talaaq" Furta cewar sai dai ya sake ta ya karya masa guiwa sai dai be karya zuciyarsa ba domin a yanzu Fatima kawai yake hange. Ya kama hannunta ya rike cikin sigar rarrashi ya ce. "Za mu iya fahimtar juna mu gyara komai, ki yi uzuri, ki karbe ni tare da yata" "Ba zan karbi uzurinka ba, kuma har abada ba zan taba son yar wata ba, har karshen rayuwata, Lihaddy akher nafas fi Ta furta hakan har sau uku tana hade hakora, kalmar ba zata taba son yar wata ba har karshen rayuwarta ya saka Turhan ya saki hannunta domin Fatima yarsa ce, ba yar Aisha kadai ba, be ce ya shirya rabuwa da ita ba, ko rusa aurensa ba, domin ba zai yarda ya maimaita irin wacan kuskuren da ya aikatawa Aisha ba, sai dai kuma hakan ba shi yake nufin ya jure a ciwa yarsa ko mahaifiyarta mutuncin ba. Ta kalli hannunta daya saki ta kalleshi fushi ya dauketa ta fara shure kayan abincin da abinci dake ciki tana ihu tana la'antarsa da kalmomi marasa dadi. Kamin ta fara bin sitting room din ta fara hargitsawa tsabar bala'inta be iya kwana a gidan ba sai fita yayi ya kwana a hotel, washe gari ko da ya dawo be same ta a gidan ba, ya samu ta yi ma gidan barna duk wani abu mai glass sai da ta fasa shi hatta kwalbar turare bata bari ba. Wanka yayi ya canja tufafi sannan yayi ma khadimansa su gyara bangaren, ya fito ya nufi fadar mahaifinsa ko'ina ya bi kallonsa yan'uwansa suke, sauran Khadiman gida kuma sai ya sauke ido ake satar kallonsa, kowa yana mamaki da abun da matarsa ta fada jiya cikin ihu da hayaniya. Yau ma da ya shiga mahaifinsa be tanka masa ba. "A gafarce ni, na san ina da tarin laifuka" Bayan kamar Minti biyu mahaifinsa ya kalleshi. "Na yi zaton ba zaka zo ba ai, saboda ban isa da kai ba" "Ban isa ba, kai kayi kira na kasa amsawa, da baka isa da ni ba da ba za a kawo maka rokon abun da a cikin aikata shi babu adalci ba" "Wata wuta ce aka ce ta kama a wani gida, aka roki na kasheta, da na bincika dalilin tashinta Sai aka fada min har da ana a gurin assasata, shin hakan gaskiya?" "An riga ni sanar da kai tashin gobarar data haifar da hayakin sanar da duniya abunda ake ciki ne, amman ina da wannan nufin a yanzu da nake ganin lokaci ne daya dace kowa ya san komai" "Aka ce ka yi aure? Tatsuniya ce ko kuma dai ana kokarin kunna fitina a cikin masarautar ne?" Turhan ya natsu Sosai ya sanar da mahaifinsa yadda auren ya afku da kuma yadda boye lamarin har zuwa yau. Yayi zaton zai fuskanci fushi da natsa daga gurin mahaifinsa ne sai gashi ya tsinkayo mahaifinsa na murmushin kasaita ya kalleshi cike da alfahari. "Wani lokacin akan dora mana nauyin abun da ba za mu iya sauke ba, sai da hikima da yawa, na yaba da kokarinka na boye auren kuma na jidadin da yarka take hannunka, jininmu baya zama a ko'ina sai a kusa da mu" Turhan ya kalli mahaifinsa cike da damuwa. "Be zama lallai Fatima ta zauna kusa da mu ba, idan mahaifiyarta ta zabi, zama a Nigeria ina tunanin ba ni da zabi da ya wuce na bi ra'ayinta domin gyara laifin da na aikata" Mahaifinsa ya sake dubansa. "Baka aikata laifi ba, ko mace bata cancanci auren dole ba balle kuma kai, baka bukatar zama da matar da baka so kuma bata cancanta ba" "Ta cancanta, saboda kyauta ce daga gurin mahaifiyar da bata jidadin zaman gidan miji ba, mahaifiyar da bayan danta da yi ma kyauta bata da wani, mahaifiyar da aka hanata ganin danta na tsawon shekaru, aka hana ta shayar da shi, na wofintar da Aisha ne saboda tsoron kallon da za'ayi min, da kuma tunanin kamar ni laraben mutum na fi wata fatar matsayi, bayan kuma har a gurin Allah ba haka ba ne, ada can bana son Aisha, amman a yanzu ina jin zan iya mutuwa ita ta rayu, ta ba ni sanyin idaniyar da ban samu ba a gurin matar da nake ganin ta fita matsayi, Ya Abiy ina son Aisha so mai tsanani, ina son yarta son da be da misali, ita ce ta maida ni uba, wannan shaukin ba zai taba gushewa ba, na aikata abun da na aikata ne saboda son zuciya, amman da na runtse ido ban ga kyau a makanta ba, anya idan mahaifiyata aka yi ma ko yata, zan iya jurewa? Amsar ita ce aa, ko ban