← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 177

Sashe 123

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ta ji suna maganar wani abun ta gudu? Tun da har ga shi Ummi da kanta fadi cewar ko dai ta ji abin da suke tattaunawa ne? Ko kuma so take ta koma gida ta dauke Fatima what if duk wannan shiri ne? Ya juya motarsa ya kama hanyar gida be samu natsuwa ba sai da ya faka harabar gidan ya fita da hanzari ya shiga falon ya nufi stairs kamin ya karasa ya ji muryar Ammy a kitchen tare da Fatima, ya juyo ya da sauri ya nufi kitchen din sai da yayi arba da sanyin idaniyarsa sannan hankalinsa ya kwanta, ya sauke numfashi a hankali har da shafa kirjinsa, ya kalli Ammy Ammy ta kalleshi tana karantar yanayinsa alamar ba lafiya ba, domin idonsa ma sun sauya. Fatima ta zo da gudu ta rumgume shi tana masa oyoyo, sai ya duka ya dauke ta ya rumgume ya lumshe ido yana jin wani irin kaunarta a ransa, da ace zuwan da yayi yanzu ya tarar bata gidan wata kila da sai yayi karamar hauka, domin ya san idan Emily ta dauke ta abu ne mai wahala kamin ya sake ganinta ko sanin inda take, wata kila ma zata iya barin kasar gaba daya. Ya fito Kitchen din ya dawo falon ya zauna rumgume da yar gudaliyarsa, Ammy ta biyo bayansa ta zauna a dayar kujerar sannan ta tambayeshi. "Me yake faru? Ya ka shigo haka a rikice" "Wai Aisha ta bata" "Ta bata kamar ya?" "Haka suka fada min, daga gidan nake na bi bayanta ne sai na samu Ummi ta fada min wai su ma nemanta suke, hankalinsu a tashe yake kuma har wani na cewa ya ganta a hanya amman be san inda take ba a yanzu, ni kuma na tafi tashar da na sani na bincika sun ce ba su ga wata mace mai kamanin taba, daga baya sai na ji tsoron ko ta zo ta tafi da Fatima ne" "Ai Fatima ta dawo gida kenan Turhan da yardar Allah, ita kanta Emily zata dawo ai uwa bata iya rabo da danta, kawai dai tana son ta tashi hankalin mutane ne gaba daya rayuwar yarinyar nan ya canja" "Wata kila kuma wani abun suka shirya ita da Aliyun, ita kanta Ummi bata sani ba, ko kuma dai ta sani amman..." Ya mike tsaye ya sauke Fatima daga jikinsa. "Ina zaka je? Karka koma gidan nan Turhan karka kuskura ka ce zaka je ka yi ma Ummi rashin mutunci" "Ba gidan zan koma ba, ba da ita zan yi magana ba, ba zai yayu na zauna hakan nan ba tare da ni nemanta ko sanin halin da take ciki ba, What if taje ta shiga wani hali again? Saboda Fatima bata kusa da ita, kuma sun zugata ke kuma kin cilasta min na sake ta, sakin nan fa bata shirya masa ba" "Kai da ba wani sanin gari ka yi sosai ba ina zaka je nemanta?" "Duk inda zan shiga dai ba zan bata ba Ammy, gashi Abie ya kira ni dazun yace na bar duk abin da nake na dawo gobe, ba ni da enough time dole na nemeta a yau, dan Allah ki kula min da Fatima" Ya nufi kofa Ammy ta bishi da kallo for the first time ta ji tausayin danta tausayi na hakika ya kamata, Fatima ta tambaye ta me yake faruwa da halshe turanci, Ammy ta bata amsa da babu komai ta rika hannunta suka koma kitchen din, Fatima na bata labarin makarantar su da zamansu da Vito. Hanyar gidansu Aliyu, Turhan ya sake komawa yana tafiya yana kallon gefe da gefe ko zai ga Emily amman ko mai kama da ita be gani ba, sai zuciyarsa ta raya masa wata kila ba guduwa ta yi ba, ko ta tafi gurin Aliyu ne sai suka yi tunanin ko ta gudu, ba mamaki ta tafi ta fada masa abun da ya faru ne, ya juya kai yana jin kamar ya shafe tarihin Aliyun nan ya huta, Aliyun nan ya masa kaya, a take ya juya motar ya daga wayarsa ya kira Ammy ya tambaya ko a wace asibiti aka kai Aliyu, Ammy ta fada masa kuma ta kwatanta masa yadda zai gane amman duk da haka sai da ya hada da tambaya sannan ya samu isa asibitin ya tambaya aka nuna masa jerin rukunan da dakin Aliyu da ire irensa suka, yayi mamaki na ganin police a bakin kofar ya dan tabe baki wato har wani tsoro ake ba shi kamar wani dan sarki. Da fari hana shi shiga suka yi, sai ya bukaci su fadawa Aliyun cewar Turhan ne da kansa ya zo ganinsa kuma magana yake son yi da shi, bayan mai aikan ya shiga Turhan ya matsa baya yana dan shan kamshi daman kuma daka ganshi kasan ya fi karfin rainin wayo, zuwansa a nan ma ba dan Emily ba, domin Aliyu ne ya kamata ace ya kawo kansa gareshi ya nemi yafiyarsa kuma ya wanke kasa, sai ga shi shi ne ya zo da kansa, but saboda Emily ne if not because of her be jin ko sawunsa zai bari ya biyo bayan Aliyu balle kuma shi da kansa. "Bismillahi ka shiga ciki" Sai da yayi musu wani kallo na rainin wayo sannan ya doshi kofar ya murda ya tura ya shiga ciki. UMMI POV. Ummi ta shiga ciki ta dauki wayarta ta kira Aliyu ba dan ta labarta masa halin da ake ciki ba sai dan ta bukaci number Emily a gurinsa. A ka'ida idan Ummi ta bukaci abu gurin Aliyu baya musa mata baya kuma mata tambaya har sai ya aiwatar, dan haka be tambayi me ya faru ba sai bayan ya tura mata number. "Na turo, amnan me yasa kike neman number ta Ummi ba tana gidan ba?" "Aa ta fita ne tace zata je ta yi magana da Turhan ne, shi ne nake son sani ko ta isa kuma sun yi magana ko kuma yaya?" "Ummi kika barta ta tafi?" "Ita ta bukaci zuwan kaga kuma idan aka hanata sai ta ji ba dadi ai, amman ba ita kadai ta tafi ba na hadata da direban da zai maidota idan ta gama" "Okay" Ya kashe wayar, Ummi ta gwada kiran Number Emily da Aliyu ya turo mata, ta kuma aka yi sa'a wayar da shiga har ta fara ringing, Mama Barakat na jin wayar ta shiga ta mike tsaye kamar zata shige cikin wayar daman ta ci kuka na labarin da ta bawa Ammy ga kuma kukan yadda zata fuskanci Emily, ga na tashin hankalin batan Emily na rashin ganinta ba ba su ba a yanzu, ita kanta bata raba dayan biyu ko dai Emily ta ji abin da suke tattaunawa kai ko kuma sakin ne be mata dadi ba, domin Ummi ta kira direbanta ne ta tambaya halin da ake ciki bayan tafiyarsu gidansu Turhan sai ya fada mata ai har sun ta dawo Emily ta sake fita, a nan suka fito falon a rikice sai suka yi arba da takardar mai dauke da rubutun Larabci, Ummi ta dauka ta karanta bata gane larabci gaba daya ba, amman dai ta karanta sunan Aisha da Turhan dake jiki ga kuma kwanan wata. A nan ta saka masu aikin gidan su fita dubo mata Emily, a wannan halin ne Turhan ya shigo ya same su. [7/19, 5:10 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy ABOKIN RAYUWA
Chapter 123 · 0% Book details