← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 177

Sashe 173

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 7 Kin dade kina sha awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba? Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na yarki? To, ga sau i ya iso! ADASHE NE NA GATA! Ki zuba ku i, ki auki abin da kike so daga: Sutura da zannuwan gado Kayan kitchen Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu) Talkami da jaka Zanen gado Frames (flowers decoration ko standing ones) Console mirror Boxes na Lefe ko na traveling. Warmers iri-iri Food flask iri daban-daban Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so! i ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa. Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati. Akwai sharudda da ka idoji. Domin arin bayani, ki/ka tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660 Ko ta hanyar WhatsApp Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1 Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t Thank you "Kasan jiya da muka je Asibiti" "Uhm" "Likitan tace kowa ta fadawa mijinta idan ta koma gida" "Mee" "Wai akwai wani sabon Technology da ya shigoo" Tana fada tana cin gauta. Shi kuma hankalinsa yana kan system din da yake tabawa. "Tace wai akwai allurar da ake yi ma mace bayan kwana biyu sai ta dawo a debi jininta sai a sakawa mijinta" "Tooo saboda me?" "Wai saboda idan lokacin haihuwa yayi sai shi yayi nakudar ba sai ta yi ba, shi zai ji zafin" Sai a lokacin ya kalleta yana dariya. "Saboda ba ni da gata?" "Aa ita ce tace kowa ya fada idan miji zai iya sai yayi" "Yanzu dai ba dan kin raina capacity na ba ta ina za a saka min nakuda dan Allah? Shi kenan ni ban da gurin kai kara idan an taba ni?" Ta kyalkyale da dariya. "New Technology ne fa" "To ba za a fara da ni ba, ina namiji ina nakuda abun ai ba zai bada kala ba, amman kuma da kin ga jarumta kamin ki motsa ido na haihu" Ya aje system din yana dariya itama dariyar take. Ya nufo inda take zaune ya dauke ragowar gautan da ta ci ya kwashe hancin ya zuba a plate ya kakkabe mata jikinta ya dauke plate din ya sumbanceta. "Allah ya sauke ke ki lafiya" "Ameen" Ya nufi kitchen ya aje plate din ya dauko mata ruwa da cup biyu ya zuba mata daya daya ya zubawa kansa. "Qalbin kin matsawa riguna lamba" Ya fada yana kallom t-shirt dinsa dake jikinta, domin tun da cikinta ya girma kullum kayansa take sakawa. Ta sha ruwan ta mika masa cup. "To ya zaka yi? Laifin waye?" "Na wa" Ya fada yana lankwafe kai kamar wani maraya. Ya aje cup din sannan ya koma ya cigaba da aikin da yake da system dinsa yana mata hira sama sama saboda baya son ta ji kamar ya kyaleta duk kuwa da aikin dake gabansa. Hannu ta kai ta shafa katon cikinta a hankali tana kallonsa, a yanzu kuma me zata roka? Me ye Allah be bata ba? Miye ta raba ba a maye mata gurbinsa da shi ba? Ita ce yau ake yi ma lele ake taraiyarta kamar yar Gold. Wannan ne cikin farko da ta raineshi da soyayya ubansa da kulawa kamar dan da daga shi ba za a sake haihuwa ba a duniya. Aliyu ya bata kulawa, ta soyayya ta kauna, ta tararaiya ta tausayi, ta kyautatawa, ya dauke mata nauyin komai, idan zata yi ma sai ya hana sai idan be gani ba, domin ta saba wahala da ciki sai ya zama aiki be mata illa bata jin nauyin aiki da ciki, amman Aliyu ya sauya kalar jikinta ta zama wata shagwababbiya kamar ba ita ba. Zama da tashi duk rikata yake idan zata yi, motsi kadan sai yace me take ji? Me take so? Bata san ta yi kwadayi da zaben abinci ba sai da ta auri Abokin Rayuwarta. Tun cikin na wata uku Aliyu yake lelenta da abun ciki har cikin ya tsufa, ta bangaren Ummi ma duk bayan kwana biyu sai ta kira, da Emily ta gane amfanin haka sai ta rika rikata da kanta ta gaishe ta. Idan tana kwadayin wani abun na dabam Mama Baraka zata aiko mata. Duk wani motsi nata yana kam idon Aliyu, a yanzu ta san ta yi aure, a yanzu ta san me ake nufi da aka aure mai sonka fiye da wanda kai kake so, a yanzu ta san ribar hak'uri tana da yawa, ta san amfanin wanda yayi hakuri sakamakonsa mai kyau ne. Cikinta na wata takwas aka yi auren Misra da Kameela da mahaifinsu ya hade, banbancin kawai na Event ne, domin Kameela bata yi komai ba bayan henna day, Misra kuma ta yi duk wani event daya kamata budurwa ta yi. Haka Emily ta sake jiki aka rika komai da ita a nan ta kara sanin dadin yan'uwa da kuma muhimmancisu, kusan komai za'ayi sai an nemi shawararta sai an sakata a ciki. Each and every minute sai Aliyu ya kira ya tambayi lafiyarta wanda kusan shi ne abun da ya fi kowane yi mata dadi, tana son kulawa kuma ta samu a gurin Abokin Rayuwa na har abada. Auren Kameela da wata daya Emily ta haifo kyakkyawan yaronta, bayan kwashe awani tana nakuda, ta yi sa'a cikin be so mata da wani laulayi sosai ba, wata kila saboda ta saba da wahala ne, wata kila kuma wannan daga jinin ubansa ne. Amman gurin nakuda bata sha da sauki ba, sai dai daga karshe ta haihu lafiya aka fito da yaron fari kyakkyawa kamar ita. Sau daya Aliyu ya karbi yaron ya duba ya mikawa Mama Baraka ne sake bi ta kansa ba sai da aka fito da Emily daga dakin haihuwa sannan hankalinsa ya kwana. Daki daya aka ware mata saboda ta samu hutu kamin a sallame su. Aliyu ne farkon mutumen da ya shigo dakin ya nufo inda take kwance ya shafa kanta cike da tausayi kamar zai zubar mata da hawaye. "Sannu... Allah ya miki albarka, ya raya abun da ya ba mu, ya ba mu ikon masa tarbiya da daukar nauyinsa, ya baki lafiya i love you so much" Ya sumbance ta sai shafa kanta yake kamar zai cinyeta. Idonta ya cika da hawayen farinciki, ta haihuwa lafiya kuma zagaye da yan'uwa da mijin dake ta daukin zuwan ansa duniya. Shi ne namiji na farko da ya nuna mata tsantsar kulawa da soyayya ya tsaya a kanta har ta haihu kuma ya rika yaronsa yayi mata godiya. "Na gode da ka kasance a rayuwata" Ya share mata hawayen sai sake mata kiss Mama Baraka da sisters dinta da yan'uwansa suka turo dakin sai ya daga ya janye hannunsa daga jikinsa. Mama Baraka ta mika masa yaron ya karba ya ciro wayarsa ya kira Ummi video call. Tsabar farinciki Ummi ta ji kamar ta baro Abuja a ranar ta zo Kd dama tana son yara tana son zuri'a balle kuma ta Aliyun da yake kamar abokin shawararta. Rabonta da ganinsu tun cikin Emily na wata shida lokacin da suka zo wani meeting na siyasa ita da mijinta. The following day aka sallami Emily daga asibitin bayan sun yi mata dinki saboda ta samu kari. A gidanta aka dawo da ita, saboda Aliyu yayi yarjejeniya da Mama Baraka tun kamin ta haihuwa cewar a bar masa matarsa a gidansa ba zai yarda akaita gidan Mama Baraka ba. A dole ya amince domin mai son naka shi ma naka ne. Aka dawo da Emily gidan Aliyu, yan'uwansa da suke cikin garin Kaduna na bangaren Daddynsa da na Ummi suka yi ta zuwa barka suna kawo masa alheri daman wacan haihuwa abun be zo da rai ba, ba a yi masa kyauta ko biki ba sai a yanzu. Yayansa kusan kullum sai ya kawo matarsa ta wuni a gidan sai dare ya dauke ta su koma, saboda tana da kyakkyawar fahimta da Emily ba kamar Kameela ba. Abinci mai kyau Emily take babu ruwanta da yaro sai idan za ta ba shi nono, wata yar danginsu Aliyu ce masu karancin rufin asiri aka bar mata tana goyon yaron, mai masa wanka dabam ta shirya shi, ta gasa mata cibiya. A yanzu ne Emily ta san wasu al'adu na jego da haihuwa, domin a baya ita kadai take haihuwarta cikin wahala a yanzu kuma tari da yan'uwa da mijinta a kusa da ita. Ana sauran kwana biyu ayi suna Ummi ta dira a Kaduna a gidanta, abun ka da yan siyasa har abun da be kai ya kawo na yi ake, sai barka ta koma gurin Ummi ana hadawa da abubuwan alheri, daman kuma wani abun biki ne dole ita ma zata rama musu. Kusan ita ta tsara yadda komai zai guna na cikin saboda Emily bata da kawaye, sai sababin makota da kuma yan'uwan miji da yan'uwanta da suka zame mata kawaye. Ranar suna yaro ya ci sunan mahaifin Aliyu Mudallab aka yi masa alkunya da Abulkhary. A ranar Emily ta ga biki ba ji ba, ta san miyen dadin yan'uwa miye yan'uwa da kuma abokan arzikin, ta san dadin haihuwa a cikin dangi ba a gurin bare ba. Ta samu alheri sosai kusan duk abun da aka bawa Ummi na biki tun daga tufafi da kayan jarirai sai da ta kawo mata su, bayan ta yi mata nata kayan barka irin wanda take yi ma matar yayan Aliyu a duk lokacin da ta haihu. Mama Baraka ma ta yi mata nata domin Abulkhary ne jikanta na farko gashi kuma tana kokarin kyautatawa Emily. Dr A-B ma be yarda an barshi a baya ba, duk kuwa da kasancewar be samu zuwa ba saboda shi ma yana ta shirye shiryen nasa auren ne, amman ya saka wata online vendor ta shirya ma Emily kayan barka daga Kano aka aika mata Kada. Uban yaro kam daman tun kamin a haihu yayi booking kayan barka gurin wata cousin dinsa dake siyar da kayan yara, da sharadin idan mace ce ga budget dinsa da zai biya haka ma namiji yayi payment tuntuni ana haihuwarta da kwana uku aka
Chapter 173 · 0% Book details