← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 177

Sashe 146

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

labarta musu gaskiya maganar ba kawai ta ce saboda Kameela tana da zafin kishi ne. Mamasu ta amsa mata da far'a kanen kam sai kallonta suke. Ta kai har kasa ta gaishe da mamansu sannan ta tambaya Tasmia ko tana ciki, maman ta tambaya ko lafiya ta amsa da babu komai tana dariya. Sai aka nuna mata dakin da Tasmia take, ta nufi dakin ta shiga da sallama tana yaye labule. Ita kanta Tasmia ta yi mamakin ganinta har tana tsoro domin bata san da me ta zo mata ba. "Yan bautar kasa wato kun gama babu ko labari babu ziyara?" "Ke da wacce kika zo? Ni da ke fa kai ta san kar ne" Tasmia ta fada sannan ta tashi zaune da kyau kar a shammace ta. Kameela ta tabe baki. "Ni da alheri na zo miki, ba sheri ba" "Koma da wacce kika zo ni daidai nake da ke" Kameela ta zauna ba tare da an mata tayin zaman ba. "Ke dan Allah ki bar abin da ya wuce ya wuce mana, ni ma yanzu ina cikin tawa matsalar mafita nake nema shiyasa na rugo a guje na zo gurinki" Tasmia dai kallonta kawai take. "Dan Allah ki ba ni aron hankalinki kuma ki natsu sannan kuma ki fahimce ne" "Ina jinki" Kameela ta yi shiru na lokaci can kuma sai ta ce. "Emily ce matsalar, amman ba zan fada miki komai ba sai idan zaki taimaki kanki ki taimake ni" "Zan taimake ki ba tare da sanin me ya kawo ki? Hajiya ki fada min damuwarki kawai ba wani noke noke" Kameela ta rage murya ta marairaice ta fara karanta mata damuwarta sannan ta koro da labarin Emily. Tasmia dai sai saurarenta take har ta kai aya. Kameela ta juya makullin motar dake hannunta tana kallon Tasmiya bayan ta gama bata duk labarin Emily da kuma abun da ya faru. "Tohm yanzu ni miye nawa a ciki? Har kike ba ni wannan labarin?" "Tasmiya aurena fa ya mutu?" "Na san aurenki ya mutu mana, abun duniya ai baya boyuwa na ji tun kamin na dawo garin nan kuma yanzu gashi kin kara fada min, dalilin da zai kawo ni cikin matsalar ne ban sani ba" "So nake ki taimaka min, ni biyanki ne ma zan yi Wallahi, na san da can kina son Aliyu ai ki yi duk yadda zaki iya ki dauke hankalinsa daga gurin kafirar nan, ni da ta aure shi Wallahi gara ke ki aure shi" Tasmia ta yi dariya "Wato Kameela kin dauke ni marar hankali marar wayo ko? Ke ce mai wayo? Bayan duk abubuwan da suka faru yanzu ni kike son na zame miki tsanin hawa? Miyasa ke ba zaki yi yakin da kanki ba?" "ba zaki gane ba ne, gaba daya baya saurare ni yanzu ya juya min baya kamar ba Aliyuna ba, daukar yarinyar da na yi na kaita gurin Turhan har Aliyu ya sake ni ni sai nake ganin kamar ba banza aka bar ni ba, Wallahi idan Aliyu ya auri kafirar nan an gama da ni gaba daya, uwarta ta yi kishi da uwata ni kuma na yi kishi da ita? Da dai ita ta aure shi kara ke" Tasmia ta tabe baki. "Ni yanzu ina da wanda zan aura masa Kameela, kuma mijinki mai wuyar sha'ani da shegen wayon tsiya" "Ai mataki zamu dauka ko ta halin yaya, idan kika ba ni hadin kai ma har acit sai mu watsa mata fuskar ta lalace daman ai kyau ne yake jansa" Tasmia ta yi murmushi a nan ta gane Kameela so take ta jefata a matsala. "Ki yi kishi da ita taya? Ai ke ba Aliyu kike aure ba, kuma tun da kika ga ya sake ki saboda ita ya nuna miki ta fiki muhimmanci kenan, haka ya buga min warning lokacin da muke can fa saboda ita, kin san mijinki dan duniya ne duk inda aka juya sai ya gane mutum, dama kin hakura domin yadda kika cika idda abu ne mai wahala ya maida ke, balle kuma kin ce har mahaifiyarsa bata sonki a yanzu, yo daman Kameela uban waye zai so ki? Kin ga yanzu ni dake ai mun zama daya, wai ke uwar gori kin ce ban da aure ko? To yanzu ni da ke waye shegen? Ni Wallahi Emily ma tausayi ta ba ni da kika ba ni labarinta, daman tun da na ganta ganin farko na fahimci tana cikin damuwa, kuma na kulla abota da ita, sai gashi son zuciya ya dauke ni na so cutar da ita ashe da na shiga uku, ni yanzu na bibiye mijinki kamar wata karuwa? Ko an fada miki karuwanci naje can ba bautar kasa ba? Kuma ni yanzu na samu wanda zan aura, kuma idan ba ki bi a hankali ba duk abun da kika fada min sai na fadawa Emily da Aliyu" Kameela ta fusata. "Tasmia idan ke ba karuwa ba ce wacece ke? Dan ubanki nan kika bar garin nan kika tafi har Ph bautar kasa da kika je kuma kika kama hanyar gida baki zauna inda kowa ke zama ba, kika dinga bibiyar mijina wai saboda kin yi kwantain, yanzu saboda kin samu damata na zo har shegen gidanku neman shawara zaki fada min magana, kutumar ubanki Tasmia, idan kin fasa tausayin Emily ko fada mata abun da na fada Allah ya tsine miki albarka" Tasmia ta yi mata sowa da baki.... "Oohhhhhhhhh an dai ji kunya, ke da kika takama kin fi karfin mijinki yau ke ce namiji ya gagareki, kike raba ni saboda ki samu shiga, ke yanzu dan Allah baki ji haushin kanki ba ma? Kim san kina Aliyun uban waye ya saka ki hauka? Kanki farau kishi mahaukaciya yar marasa tarbiya.." "Ubanki ne shegiya mai warin talauci, kuma muna nan dake zaki gan ni da Aliyu, ni da shi mutu ka raba ne takalmin kaza dan ubaki Zubairu" Tasmia ta rufeta da duka suka fara kaiwa juna naushi sai da kanen Tasmia da mamansu ta shigo aka raba su. "Lafiya" "Mama ki bar ni na ci uban yarinyar can, ganin take saboda suna da kudi zata iya taka kowa? Muma na ao muna da rufin asiri yar iska, daman ina rike da ita a zuciyata, idan ba ke wawuya ba yaushe zaki yi fada ni kuma yanzu ki wanko kafa ki zo wai na taimaka miki ke dakikiya ko.? Kara da Aliyun ya sake ki ai, kuma da yardar Allah sai ya auri Emily ke kishiya uwarki kishiya" "Ke ce yar iska marar tarbiya, mai bibiyar mazajen mutane, ko yanzu wa san mijin wa kika kwato? Muna nan da ke Aliyu ba zai auri Kafira ba, haka kuma ba zai auri yar iska irinki ba" Mama ta rufe baki. "Aa ahhhhh kin ga wannan.... Amm... Kameela kike da suna ko? dan Allah kama hanya ki tafi bana son fitina, ba alfahari ba ni dai yarana ba su da abokin fada, kuma ba zan su ki yi abun da zai saka mu da ke mu yi ta nadama ba, dan Allah yafi kin ga karfi ma ba daya ba, daman tun farko na ganki na san ba lafiya ba" Ta dauki makullin ta dake can karshen kofa ta fice tana ya huci sai zagi take jefowa Tasmia idan ta yi yunkurin ramawa Allah Mamanta ta hana. Kameela ta fito rai a bace ta shiga motarta ta juya kamin mai gadin ya bude mata gate ya daga masa hankali da horn kamar zata tashi gidan. [8/8, 9:58 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 146 · 0% Book details