Sashe 62
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2 The following day ya shirya ya wuce Abuja gurin mahaifiyarsa daman zuwansa kaduna saboda Kameela ne, ya fara sauka a nan idan ya ganta suka gaisa aka masa binkonta zuwa gidansu dake Kaduna sai ya dauke ta su tafi Abuja gurin Ummi su mata kwana biyu sannan su sannu dawo garin da yake aiki a yanzu wato Part hartcour, sai dai a yanzu ta yi nasarar ata masa rai yayi tafiyar da be shirya ba. Ya sauka Abuja around 12pm Ummi ta aiko sabon direbansu ya dauki Aliyu daga Airport zuwa gidansu dake Wuse II, kamin su karasa gidan Kiran Kameela ya shigo wayarsa a karo na 32 bayan sako goma sha daya da ta aiko masa, be amsa kiranta ko daya ba haka kuma be mayar mata da amsar sakonta na Sms ko WhatsApp ba, har Instagram dinsa sai da ta bishi tana masa be amsa ba, domin a duka sakwaninta babu wanda ya nuna ta yi nadamar abun da ta yi sai dai ta bashi hakurin bata masa rai da tayi wani gurin kuma tace wai yanzu saboda wata banza yake mata wulakanci, wani sakon kuma tace ya bata mamaki, a na karshen kuma nanatawa take wai zai jawa Emily bala'i idan be rabu da ita ba. A katafaren gidan Direban ya faka ya fito ya budewa Aliyu mota, Aliyu ya fito yana kallon yadda aka kara gidan na mahaifinsa kamar ba za a mutu ba. Sannan ya wuce ciki, falo biyu ya wuce sannan ya isa wani madaidacin falo wanda be kai na farkon sa na biyun girma ba, kanwarshi ta zo da gudu ta tarbe shi ita da wata cousin dinsa, Aqeel kuma ya mika masa hannu suka yi chop knuckle, Ummi ta dan tabe baki kadan tana kallonsa. "Yaushe rabonka da gidan nan?" Ya nufeta ta zauna kusa da ita yana dariya. "Irin Welcome din nan ma na uwa da a ba zan samu ba? Ina shigowa sai a fara min da tambayoyi" Ummi ta yi murmushi kadan, tayi ma direban da ya shigo da akwatin Aliyu sannu. "Hajiya ga wannan ina za a aje?" "Bar shi a nan Khaleepa Ladi zata shigar masa da shi ciki" "Toh Hajiya" Ya amsa sannan ya juya ya fice. "Ummi haka aka kara gyara gidan nan, wato ku babu ruwanku duniya ta muku dadi ko?" Ummi ta watsa masa wani kallo har tana karkatawa dan ta samu ganinsa da kyau. "Ahhh Toh so kake ta yi mana zafi? an hamayya! Ko ka bi jam'iyar matarka? Kasan fa kai yanzu ruwa biyu ne, kana nan kana can ba gane kanka ake ba, karka mana zagon kasa" Duk suka fashe da dariya har Aliyun, daman haka yake da mahaifiyarsa idan suka hadu ita da shi kamar abokan wasa ko yaya da kanenta, sam ba zaka ce a da uwa ba ne. Sai da suka gama wasa da dariya da Ummi sannan ya shiga ciki yayi wanka ya fito ya dawo dakin Ummi, already ya samu Ramla ya kawo masa abinci a dakin Ummi, abu ne da suka sani idan zai ci abinci duk inda Ummi take zaune a nan yake ci, a daki ne ko falo ko bangaren mahaifinsa, shi dai burinsa ya ci abinci kusa da mahaifiyarsa yana ci yana hira da ita. "Sai yaushe Daddy zai dawo?" Ya tambaya bayan ya kai spoon biyu bakinsa. "Daddynka yanzu ganinsa sai da ticket, ko ya shigo ba samun ganinsa zaka yi ba" Yayi murmushi "Ummi wai ni korata kika yi a gidan nan ko sadakata aka ba da, na ga tun da na so kike min wulakanci" "Daman kai dan gidan nan ne? Ai mun yafe ka tun da muka aurawa Kameela, yaushe rabonka da gidan nan, babu ruwanka da labarin mu komai ake kai baka ma sani ba, yanzu ma ba dan ka samu matsala da Kameela ba ba zaka zo ba" "Yanayin aikin ne ai Ummi kin san ba mu da hutu kullum, kuma daman na yi nufin daga Kd na dauko Kameela mu zo nan mu kwana biyu wannan mu koma, sai gashi notin kanta daya ya cire" Ummi ta tabe baki. "Allah dai ya kyauta, dazun ma ta kira ni tana fadin wai ka mata fada kamar zaka daketa, saboda wata matar abokinka Turhan kuma matar ma kafira ce miye miye... Ni ban ma gane kan zancen ba, wai yanzu kuma fushi kake da ita" "Shareta kawai Ummi ba zaki ganin kan zancen ba" "Kishin yarinyar nan yayi yawa, kuma ba komai ya sa yayi yawa ba sai damar da ka bata, akwai abubuwan da ake takawa mace burki a kansu, amman kai komai ta yi sai ka biye mata saboda kana sonta, wannan ba so ba ne, abun da kake mata yanzu tana wuce gona da iri shi iyayenta suke mata da sunan so alhalin ba soyayya bace lalata mata tarbiya ne suke yi" "Ummi da kin tashi magana sai ki ce Kameela bata da tarbiya, Kameela tana da tarbiya kawai dai zafin kishi ne yake damunta" "Na ji tana da tarbiya, iyayenta fa? Ai komai kyaun farin tuwo a akar tukunya ya fito, kuma kamar kumbo ne kamar korensa duk yadda za'ayi dole Kameela sai ta samu matsala domin barewa bata gudu danta yayi rarrafe, idan bata maka abun haushi ba iyayenta za su maka, kuma duk yadda aka yi sai ta dauki hudubarsu, uwa ba wasa ba ce Aliyu, idan za'ayi aure ba tarbiyar yarinya kawai ake dubawa ba har da iyayenta ana son a duba su waye iyayenta" Be sake cewa komai ba har ya gama cin abinci, domin abun da be yarda da shi ba shi ne mahaifiyarsa ta zauna tana zagin matarsa, hakan zai dasa kiyayyarta a zuciyar mahaifiyarsa, wanda ba zai so haka ba, even though dai Ummi ba wani yin Kameela take cancan ba, amman ya san bata tsaneta ba, haka kuma ko da wasa ba zai yarda ya budewa matarsa damar maganar mahaifiyarsa ba, kowa matsayinsa dabam. Ya gama cin abinci a daidai lokacin da motar Daddynsa ta faka harabar gidan, sai dai be san shigowarsa ba domin gidan ba irin gidan da ake jin fita ko shigowarsa mota ba ne, musamman dakin Ummi da baka sanin wainar da ake toyawa idan kana ciki sai ka fito. Aliyu ya aje spoon din da ya gama cin abinci da shi kenan, kiran Daddy ya shigo masa ya sanar masa ya dawo. "OK Daddy gani nan zuwa" Ummi ta kalleshi. "Wato na yan siyasa mahaifinka yayi min ko? Daga ganin sabuwar jam'iya sai ya tsalleke ya koma can ko? Ai tafiya zaka yi a bar ni da shi" Aliyu ya kai tsaye yana dariya. "Allah ya bar mana ke Ummi, yanzu miye laifin Daddy dan ya nemi ganin dansa?" Ummi ta yi murmushi. Aliyu ya fice shi ma yana murmushin. Wani abun da ya kara bata masa rai a game da Kameela shi ne sanar da Daddy da ta yi bayan Ummi, kuma ko kadan hakan be masa dadi ba, domin a ganinsa abun be kai ace iyaye sun ji ba, ta sanar da iyayenta hakan be mata ba sai ta sanar da na shi. Nasiha Daddy yayi masa akan zamankewar aur e ya fada masa wai sai yayi hakuri da matarsa kowa hakuri yake. A tare suka yi Sallah Isha'i a harabar katon gidan dake da matsakaicin masallaci a ciki, Aliyu ya jagoranci Sallah daya daga cikin jami'an tsaron da suke gadin gidan yayi masa ladanci, Daddy da sauran ma'aikatan gidan kuma suka shiga sahun mamu, bayan an gama sallah ne Aliyu ya juyo yana gaisawa da kowa yana musu alherin da abun da ke aljihunsa, har ya kai gurin sabon direban da aka dauka domin shi dai be taba ganinsa cikin ma'aikatan gidan ba, ko da yake gidansu kullum cikin canje canjen ma'aikata yake ba shi kadai ya gani bakuwar fuska ba, amman rabin fuskarsa ta fi tsaya masa a rai, domin rabin kawai ake iya gani dayan gefen a kone yake har zuwa hannunsa na hagu, yayi baki sosai ya alamar wuta ko mai ta kone jikinsa domin fatar kafadarsa ra hagu zuwa wuyansa a hade take, jikinsa ya zama two color. Kwanan Aliyu biyu a gidan kullum suna haduwa gurin sallah gidan, kuma a kullum sai yayi musu alheri, daman duk lokacin da ya zo a gidan ko gidansu na Kd haka yake da kowa har ya koma, a ranar da zai koma Ramla ta fito masa da akwatinsa falonsa dai daga cikin masu aikin gidan ta dauki akwatin ta fitar da shi waje sai direban ya karba ya saka mota. Aliyu na zaune falonsa yana duba agogo hannunsa Ummi ta sauko rike da cup tana sanye da Filafil Swiss Lace dan 530,000 da ta siya gurin Khadeeja Candy. Cup din hannunta ta mika masa ya dago daga kishimgiden da yake ya karbi kofin ya leka ciki sai ya ga ruwa kadan, be tsaya komai ba ya kai kofin baki ya shanye addu'ar dake ciki. "Ita wannan addu'ar idan an sha ana shafawa ko sha kawai ake? Na shanye duka da" Ummi ta yi murmushi irin na su na manya hakwaranta biyu na makka na bayyana. "Baka tsaya ka ji yadda ake shan ba ka shanye" "Ai na san ba saki ba ni abun da zai cutar da ni ba, kuma kin saba min Ummi tun ina yaro kullum sai kin tofa min addu'a a ruwa kin ba ni, kamar dan siyasa" "Ba sai dan siyasa yake da makiya ba, wani baka sanin makiyinka sai ranar da girkin ya i dadi, wani ma sai an hadu gaban Allah gurin rabawa kowa abun da ya aikata zaka ga wani ashe ya ci da guminka ko ya cutar da kai kai baka ma sani ba, dan haka ka rike addu'a da addu'a zaka fi karfin komai, kullum idan zaka iya kamin ka ci komai ka karanta fatiha da ayatul kursiyu ka tofa a ruwa ka sha, Allah ya tsare min kai ana, ko baka siyasa ai kai dan masu siyasa ne" Ya kwanta jikin mahaifiyarsa yana jin tsananin kaunarta. "Sai ni Aliyu dan