← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 177

Sashe 142

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

corner da yake ibada a dakin ya fara sallah. Daman Larabawa sukan ware wani bangare a dakinsu da suke shimfida Carpet su aje qur'ane ana saka turare domin ibada. Be daga daga carpet din ba har aka yi sallah asuba. Bayan ya gama sallah bachi mai nauyi ya dauke shi, be farka ba sai da ya ji yatsun Ammy cikin kansa, ya bude ido ya kalleta sai ta yi murmushi tana cigaba da shafa kansa. al-khayr y Ammy" Ya furta da murmushin karfin hali, ta amsa masa cike da kauna irin ta uwa da mil shinu y walad ? All h yi ak l walad ? Keif lak?" Ya daga kadan ya kwantar da kansa kan ciyarta. "Babu dadi Ammy" "Ka raya dare da damuwa ko? Ni ma jiya na ji babu dadi saboda Fatima bata gidan, amman dai yau za mu tafi gidan" Ta sauke kansa. "Kwanta ka samu bachi, kana da bukatar kuzari ana, Allah ya maka albarka" Ya lumshe ido bayan ya amsa da Ameen, Ammy ta tashi cike da tausayin danta da kuma bacin ran halin da yake ciki ta fice dakin. [8/6, 11:10 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 142 · 0% Book details