Sashe 177
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigo, ta zauna can nesa da shi ta zauna, haka take a duk lokacin da yake magana da yarsa saboda tana kishin Fatima ba yarta ba ce, kuma tana kishin duk wani abu da zai dauke hankalin mijinta daga gareta. Ta jira har sai da ya gama wayar sannan ta koma kusa da shi ta tsaya tana murmushi. "Rufe idonka" Ya kalleta cike da shauki, yayi murmushi ya rufe idon kamar yadda ta bukata. Ta kama hannunsa ta saka masa abu a hannu, ya lakaba abun sannan ya bude idon. Wasu yan mitsitsinan kayan yara ne irin na yar tsana amman na jarirai. "Da leek.. laken testanna tis a shuhur." "Wannan domin kai ne, amman ka jira sai nan da wata tara" Turhan ya kalleta ya sake kallon kayan, kamin tunaninsa ya ba shi abun da ya dade yana tsammani daga gareta. Wani irin tsalle Turhan yayi ya dauke matarsa yayi sama da ita yana juyawa. Kamin ya sauke ta tambayeta. "Kina ciki da gaske?" Ta daga mishi kai tana hawaye. Sai ya sake rumgumeta "Wallahi ana ba ibbik shadeed.. Enti addayteeni al-farha al-bat kunt bafta alaiha, khalleetini mabsoota li-daraja ma ba at mihtaaja ay farha taanya." "Wallahi ina kaunarki.. Kin ba ni farinciki da nake nema, kin faranta min baya na rasa wani farinciki. Alhamdulillah ya Rabbi, Alhamdulillah Allah A lokacin ne ya gane rokon da yayi a saudi be tafi a banza ba, rasa Emily ya samu wani farinciki ta inda ya cire rai da samu, ada yayi zaton Fatima ce kadai yarsa, ashe ba iya haka farincikin zai tsaya ba. Da Ammy ta samu labari kamar ta zuba ruwa kasa ta sha tsabar farinciki, kusan duk wanda ke masarautar ya taya Turhan murna da farinciki a lokaci da cikin ya bayyana. Wani irin kula na musamman da tarairaiya kamar kwai Turhan ya shiga yi ma matarsa. Ko da baya son ya shirya kula da abun cikinta balle kuma yana kaunar matarsa tun asali a yanzu ne ma kaunarta take ninkuwa. Ba ma kamar lokacin da ta haifa masa yan biyu mace da namiji, kamar mahaukaci haka ya zama tsabar farinciki macen aka saka mata sunan Ammy namijin kuma ya saka masa sunan da matarsa ta zaba. Sai da suka yi kwari sosai sannan ya cilastawa matarsa shiryawa suka tafi Nigeria a tare aka kaiwa Ammy da Fatima yaran suka gani. Da ya ji labarin Emily na da wani cikin gurin yarsa, sai da zuciyarsa ya sosu, har kullum ba zai cire rai da fatan rabuwar auren Aliyu da Emily ba, yana ji a jikinsa komai daren dadewa Aliyu zai juyawa Emily baya. Ammy ma haka take saka rai saboda tana ganin Emily da Aliyu sun musu butulci. EMILY POV Emily ta saba da ciwon zuciya. Duk wanda ya zo mata a baya sai ya bar ta da hawaye da raunukan da ba sa ganin ido amma zuciya tana ji. Auren farko ta zame mata yaudara, na aure na biyu ya zame mata jinya. Lokacin da ta daina tsammanin farin ciki, sai ta ha u da Aliyu. A farko ta auke shi ma kamar sauran mutanen me, ya shimfida mata soyayya sai ta hau ya juya baya. Sai dai lokaci ya nuna mata kuskuren tunaninta. Aliyu bai tsorata da raunukan da take auke da su ba. Ya tsaya mata kamar likita ga mara lafiya. Ya saurare ta ba tare da gaggawa ba, ya rungume ta ba tare da sharadi ba, ya nuna mata cewa akwai wanda zai iya sauya ciwon zuciyarta ya mayar da shi farin ciki. A hankali Emily ta fara murmushi inda ta saba zubar da hawaye. Zuciyarta ta bu e kamar furanni da suka ji ruwan sama bayan dogon fari... *** Tana tsaye a Kitchen tana juya miyar dake kan wuta Aliyu ya shigo, bayanta ya kaiwa duka kadan sannan ya juyo da ita tana dariya ya sumbance ta. "Me kika girkawa haka kamshi har office ya tarar da ni" Ta yi dariya. "Kuma fa yau ba da kai na girka ba" Ya hade rai. "Kai kin ma isa?" "Kai haka kake da kyau daman?" Ya kai mata mitsika a kumatu "Miyasa kika raina ni wai? Kin san fa ni oganki ne" "A baya ba, a yanzu kuma Abokin Rayuwa" Ya rumgume yana murmushi ya shafa katon cikinta. "je ki huta bari na zuba abincin ai yayi ko?" Ta daga mishi kai. "Baka siyo min komai ba?" "Na siyo mana, wani mai nama na gani yana soyawa na cire masa zuciyata na ce ya soya min na kawo miki" Ta chakuli cikinsa tana dariya, shi ma dariyar yayi ya kashe gas din, ya dauki cooler da aka siya mata gurin Khadeeja Candy ya fara zuba miyar. Falo ta dawo ta zauna ta bude ledar kayan cikin dake ta kamshi tana fara ci, tana jin kaunar mijinta, a yanzu ta gane ba dukkan soyayyar gaskiya ake samunta cikin sau i ba. Wata soyayyar sai da jinya, sai da yaudara, sannan daga arshe Allah ya kawo maka wanda zai goge komai ya mayar da ke sabuwa. Aliyu ya zama wannan kyauta, Wani lokaci idan ta tsaya gaban madubi, sai ta dubi fuskarta dake cikin madubin tan a tambayar kanta Shin ni ce waccan Emily da ta sha kuka da hawaye a baya? Ni ce waccan yarinyar da ta yi ta fadi-tashi a soyayya, ta rasa uwa, ta rasa gata? Madubin ya kan nuna mata fuskar mace, amma cikin zuciyarta hotunan rayuwarta take gani, yadda ta yi ta neman wanda zai tsaya mata, yadda ta sha karya da yaudara, yadda ta sha jin kalmar ki yi hakuri ba tare da wani ya share mata hawaye ba. Amma yanzu abubuwa sun canza. Wani haske ya bayyana a rayuwarta, hasken da bai zo da wuri ba, sai bayan dogon lokaci. Duk jarabawar da ta sha, duk fuskokin da suka juya mata baya, duk hawayen da ta kwanta da su, sun zame mata darasi guda, hakuri wanda shi ne makullin kowane sauyi mai kyau. Da farko, hakuri ya yi mata nauyi. Amma da ta dage da shi, sai ta ga riba. Ta gane cewa bayan wuya akwai da i. Ta dandani zafin lokaci, amma kuma tana kan dandana za in sakamako. A yanzu idan ta kalli kanta a madubi, ba kawai tana ganin mace ba, tana ganin arfi da jarumtarta, tana ganin mace da ta yi tafiya kan wuta ta jure har ta kukanta ya sauya zuwa murmushi. tana kallon wata karamar yarinya da zama uwa, yar'uwa, a kuma mata ga mutumen da ya san darajarta, mutumen daya sauya lafiyar rayuwarta, ya canja tunaninta ya sabunta duniyar da abubuwan da bata sani ba, bata saba ba kuma bata taba tunanin za ta samu ba. Emily ta sha taskon rayuwa, an haifeta ba da aure ba, kuma mutane suka ora mata nauyin da ba nata ba. Ta taso cikin hawaye, cikin rashin gata, har sai da zuciyarta ta gushe daga neman farin ciki. A Lokacin da Khaleefa ya yaudareta, ta yi zaton soyayya ba gaskiya bace sai ta karyata gaskiyarta, da Turhan ya juya mata baya, dan zaren farinciki daya rage mata sai ya tsinke, duk da irin hallacin da ta yi wa mahaifiyarsa, ya kasa ganin darajarta. Amman a yau dukansu su biyun sun rasata, bayan doguwar jinyar cin amana da kowanensu yayi a zuciyarsa. Idan cin amana tana da rana Khaleefa ya gani, idan butulci yana da ciwo Turhan ya fi kowa fahimtar haka a yau, yana dauke da ciwon kaunarta gashi ta masa nisa, Khaleefa kuma be isa ko kusa da ita ya tsaya ba. Emily ta samu gata a wajen Aliyu, wanda ya rike ta da gaskiya, wurinsa ta san da in addinin Musulunci, a wurinsa ta gane cewa soyayya rahama ce, gata ce. Ta tashi daga matar da ake wulakantawa zuwa wanda ake alfahari da ita. Ta zama uwar a a gidan Aliyu, kuma mata ga mutumen da ya fahimce ta tun farko, ya girmamata, ya so ta, ya bata gata, ya mantar da ita damuwa. Asalinta be hana ta zama abar so a gurinsa ba. Rayuwa ta karantarta ita duk inda aka haife ka da aure ko ba aure ba kai halittar Allah ne mai daraja, kuma ba laifin ka ba ne... Na gyara miki rubutun gaba aya my Lady , na ha a da abin da kika bu ata, tare da arin salo mai kyau da an jan hankali ga masu karatu: Godiya ga Allah da Ya bani ikon fara wannan littafi har na kammala shi cikin nasara. Alhamdulillah. Wannan littafi na sadaukar da shi ga Big Sis Habiba Muhammad I love you more than words can ever express. Masu karatu zan so jin daga gare ku Wane darasi kuka koya daga cikin littafin? Wace angare ya fi burge ku? Kuma da me za ku fi tunawa da littafin Abokin Rayuwa? Kada ku manta, ni ce Khadeeja Candy mai siyar da kaya masu kyau da inganci a farashi mai sau Khadeeja Candy Store https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t Sai mun ha u a littafi na gaba mai suna GUMBAR DUTSE, in sha Allah. I love you all dearly ina yi muku fatan alheri fiye da yadda kalmomi za su iya bayyana. $b%d%f% $d%f% Calibri Calibri SimSun Times New Roman Times New Roman Light Light DengXia Cambria Math Cambria Math !%),.:;>?]} $([{ _GoBack SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO CM5 TECNO LD7 WPS Office 03563c64bb4a4d76a9c24e6828d3886a