Sashe 127
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 5 Tana jefar da wayar ta cigaba da tafiya, a yanzu ta yi giving up akan rayuwarta da duk wani abun da ya shafe ta, ta sha wahala iya wahala, daga karshe kuma burinta da mafarkin da take da shi ya rushe. Jin tsayawar motar bayanta be saka ta juyo ba har sai da ta ji an fisgota an juyo da ita da karfi. Wani mutum ta gani wanda bata sani ba, ya rike ta gam sai ga wasu maza biyu sun fito daga motar wacce ta kasance ta jigila ma'ana motar haya, dukansu suna sanye da kayan gida ne. "Ke ce Emily?" Dayan dake rike da ita ya tambaya, sai ta daga kai ko kadan babu tsoro ko faduwar gaba a tare da ita, domin a yanzu ta shirya ko da mutuwarce tana ra'ayin a mutuwar. "Kina tare da wani a nan ne?" Ta girgiza kai. Sai ya ciro wayarsa ya kira. "Mun same ta" Yana fadar hakan ya amsa da "Okay Sir" Sai ya kashe wayar. "Su waye ku?" "Jami'an farin kaya ne" "Me aka ce na yi?" Yayi shiru be ce mata uffan ba kuma be sake ta ba duk kuwa da irin kokarin da take na kwatar kanta. Sai da wayarsa ta sake ringing ya daga yayi magana. "Abunda muke gani dai babu wani rauni ko matsala a tare da ita" Ya saka Hands-free ya mika mata. "Emily ki shiga mota za su taho da ke" "Waye wannan?" "Sunana Adam Bello" "Dr A-B, suwaye dan nan me aka ce ana yi?" "Baki yi komai ba, na kira baki daga ba, sai na sake kira na ji kina waya bayan kin fada min kina neman taimakona, shiyasa ni kuma na nemi taimakon Babana aka yi tracing dinki" "Na nemi taimakonka a dazun saboda ina tunanin kamar walwata ta tabu, amman yanzu na samu lafiya, bana son taimakon kowa bana son kowa kusa da ni" "Emily ko da tsiya ko da arziki za su zo da ke, dan haka ki bada hadin kai su zo da ke ta arzikin zai fi" Ya katse wayar, mutumen dake rike da ita ya sake ta ya nuna mata motar da suka shigo, ta nufi motar ta dayan ya shiga ta shiga dayan ya shiga aka saka ta tsakiya sannan guda ya shiga front seat direba yaja motar suka yi gaba. Headquartersu suka tafi da ita suka bata guri mai kyau da abinci, bayan sun dauki Information dinta, amman ruwa kawai ta iya sha, shi ma saboda makoshinta yana bushewa ne, daman bata ci komai ba ya tafi gidansu Turhan. Da dare yayi suka dauke ta daga nan suka sakata wata mota mai kyau da ac aka kaita gidan wani babban mutum, suka tarbe ta da hannu biyu a nan ma suka bata masauki mai kyau aka kawo mata abinci, shi ma ta kasa cin komai, bata raina kanta ba sai da dare yayi bachi yaki zuwa mata sai tunani gashi ta gagara kuka, gaba dayan rayuwarta sai da ta tuna shi a dare, yadda Khaleefa ya latsata ya yaudareta, zaman da ta yi gidansu, fitowarta haihuwar London, haduwarta da Ammy aurenta da Turhan zaman da ta yi a masarautarsu, dawowarta wahalar da ta sha da cikin Fatima, haduwarta da Vito yar rayuwar jindadin da ya bata mai hade da duka da kangin na zaba mata abokan mu'alama, haduwarta da Aliyu, mutuwar London, yadda ta rasa Fatima har zuwa yau da Fatima ta zabi ubanta sama da ita, wanda shi ya fi komai yi mata ciwo, da karya zuciyarta. Ba'ayi wani dare da yafi kowane tsayi a idon Emily kamar wannan daren da bachi be rabi idonta ba, tunani be barta ba, kuma hawaye ba su ziyarce ta ba, kamin safe kanta ya cika yayi mata nauyi kamar wanda aka hurawa iska ciki, idonta ma sun yi nauyi sosai kana kallonta kasan bata samu runtsawa a daren ba. Misalin karfe takwas wata yarinya wacce ta fi kama da mai aiki ta shigo gidan ta ce mata ta shirya za a zo a dauke ta karfe 8:30, Emily ta daga mata kai kawai, babu jimawa yarinyar ta dawo ta kawo mata ruwan tea da kayan hada shayi sai bread. "Na a gama hada abun karyawa ba, amman ki ci wannan saboda za ku tafi" Nan ma Emily ta daga kai kawai, saboda bata son yawan magana ko musu, yarinyar ta fita Emily ta kalli kayan da aka kawo ta dauke kai har lokacin bata ji tana sha'awar cin wani abu ba, gaba daya bata jin yunwa cikin ya daure jikinta ne kawai take ji babu karfi sai kuma ciwon da kanta yake. Misalin karfe takwas da rabi yarinyar ta sake shigowa tace ance ta fito. Emily ta mike tsaye ta bi bayan yarinyar suka fita tare, yarinyar ta rakata har harabar gida, har lokacin masu gidan masu farka ba, sai yan aiki ne suke ta kai da kawo. Mutumen da ya kawo ta jiya ne ya dawo ya dauke ta a wata motar ta dabam ba wacan ba, sai da ta shiga cikin motar ta tarar da wani a mazaunin direba, dayan ya shiga front seat suka damka mata duk abun da ya kamata sannan suka nufi airport da ita, suna yin farkin a harabar airport din ta fashe da kuka tunawa da zata tafi ta bar yarta, idan akwai abun da take kauna a duniyar nan be wuce Fatima ba, saboda ita ce kadai sanyin idaniyarta, sai dai tunawa da ita kanta Fatimar bata bukatarta ya saka ta takaita kukanta ta share hawayenta ta duba ticket din hannunta. Da kanta ta bude motar ta fita mutanen suka mata rakiya har ciki, ba su bar gurin ba sai da jirginta ya daga zuwa Abuja, a jikin Window ta zauna ta jingina tana jin kamar jirgin ya juya ta koma ta dauko yarta ko da da karfi ne. ALIYU POV. Duk inda ake saka ran za a samu Emily kamar tasha ko unguwanin dake kusa da su, sai da Ummi ta aika aka bincika mata ana cigiya amman ba a samu ganinta ba, a nan hankalin Mama Barakat ya kara tashi ta sha kuka sosai kamin Ummi ta iya rarrashinta har ta samu karfin guiwar tafiya gidanta, daman yaranta tun gabanin ta yi magana da Ummi ta ce su tafi gida. Ummi bata samu tafiya Asibiti da safe ba sai aikawa ta yi aka kai masa abinci da tufafin da zai canja. Da dare ta dafa masa abun da ya fi so wato sinar da miyar kaza ta tafi masa da shi hadi da watermelon juice. Ko da ta shiga ya same shi zaune yana karatun qur'ane a wayarsa. Direban da suke tare ya aje abincin ya yayi masa ya jiki Aliyu ya amsa masa da kai, bayan ya fice Ummi ta zauna tana murmushi. "Maa Shaa Allah, jiki dai Alhamdulillah alamar sauki yana ta bayyana" Aliyu yayi murmushi ya yi addu'a yayin da ya kai karshen aya ya fita daga app din. "Ummi barka da rana" "Barka dai ya jikin?" "Alhamdulillah" "Haka ake so, wayar nan taka zan karbe ta gaskiya na aje har sai ka samu sauki tukuna" "saboda me?" "Saboda bana son ta dauke maka hankali, zan kawo Kur'ane sai ka rika karatu da shi" Ummi ta bude abinci zata fara zuba masa. "Saboda Emily ne?" Ta kalleshi. "Kamar ya? Ka yi magana da ita ne?" "Na yi magana da ita, ta fada min Turhan ya sake ta, kuma Fatima ta zabi ubanta tace ba zata bita ba, and lastly ta fada min wai wata mata ta bayyana a matsayin mahaifiyarta, kumq ta fada min zata shiga duniya" Ummi ta maida plate din ta aje. "Taya ka samu magana da ita? Mun yi ta kiranta bata daga ba, daga baya kuma muka ji wayar a kashe har yanzu wayar a kashe take" Yanayin fuskarsa ya sauya sosai. "Kamin ta kashe layin na kirata mun yi magana, Ummi me yasa kuka bari ta fita gidan?" "Babu wanda yasanta fita, satar kafa ta yi bayan dawowa daga gidansu Turhan ta gudu saboda ta ji muna magana da Hajiya Barakat, kai ma kasan da sanina dai ba zan bari ta gudu ba, ko dan ma gudun tashin hankalinka, amman ya zan yi tun da haka ta zaba ma kanta?" "Haka dai rayuwa ta zaba mata, ba zata tana zama guri daya ba, sai ranar da wani ya gina gida mai cike da burinkanta da mafarkan da ta dade tana yi, tana guduwa ne saboda tun tashinta bata san wani gida da zata rike a matsayin nata ba, ta kasa aminta da kowa ne saboda duk wanda ta raba sai ya cuceta, ko da kuwa ya taimake ta da farko, shiyasa take kallon kowa haka yake a yanzu, bata da wasu yan'uwa da idan wani ya nunata da yatsa zata juya taje garesu, ita kadai take rayuwarta fadi ta shi duk ita kadai take abun ta, Emily fa ko kawa bata da a yanzu, ni da ke ba za mu gane ba, saboda mun tashi da yan'uwa da iyaye, amman a idon wanda ba shi da kowa yana kallon duniya colorless ne" "Amman yanzu ai ta samu uwa, sai ka ga yadda Hajiya Barakat take ta kuka gwanin ban tausayi" "Daman ta fada min wata daga dangin Kameela ce take ikirarin ta haife ta, amman da gaske ita ce mahaifiyarta?" "A yadda ta fada min dai, ita ta haife ta, amman a zahiri kam ba hadi domin Emily bata kama da ita" Sai a lokacin Aliyu ya cika da mamakin jin cewar Mama Barakat ce mahaifiyar Emily, dazun tunanin tafiyar Emily be bar shi ya sararara ba balle yayi wani tunanin, sai a yanzu ya tuna labarin da ta ba shi cewar matar da ta zo da ita daga Kaduna sunanta Mama Barakat kuma ta tafi da ita gidanta amman bata tsaya ba ta gudu. "Amman da gaske bata hanyar aure aka haifeta ba? Kuma da gaske jefar da ita ta yi?" Ummi ta daga mishin kai cikin yanayin damuwa. Aliyu ya jingina ya rufe ido yana fadin. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un" "Wallahi, ni ma ta ba ni tausayi, wasu iyayen basa da tunani ne kawai, taya zaka jefar da abun da ka