← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 177

Sashe 130

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kaduna har zuwa nan, ya kamata mu san da wa muke zaune a nan" "Yeah amman ba yanzu ba, she's Cristian" "Matsalar bata addini ba ce, idan kana son mu'amala, kawance ko aure musulma ko wanda ba musulma ba, wannan ba matsala ba ce, matsala shi ne mu san wacece ita" "Zan iya baki labarina idan kina so" Dr A-B ya mike tsaye da sauri ya koma kusa da Emily ya zauna tana hawaye ya rumgume ta. "No ba yanzu ba" Momy ta kalleshi kamar bata jidadin rungumar da yayi ma Emily ba ta mike tsaye. "I'm sorry Son bana nufin bakanta mata, kuma karki dauki hakan a matsayin wani abu, as long as my only son was the one bought you here you're welcome" Dr A-B ya bata rai alamar be jidadin Momy ta yi ba, ita kuma bata sake cewa komai ba ta koma dakinta. Emily ta daga kai ta kalleshi. "Ya zan yi da rayuwa? Ji nake kamar zuciyata zata tsaya" Ya kara rumgume ta. "Ya isa haka" Ta share hawayenta ta raba jikinta da na shi. "Zan iya komawa dakin da ka sauke ni" "Yeah" Ya bita da ido har ta fita falon, sannan ya mike tsaye ya shiga dakin da Momynsa take. Tana fitowa falon ta fara saukowa kasa tana hawaye madadin ta tsaya hawa na biyu inda ya sauke ta sai ta sauka kasa gaba daya tsabar hankalinta baya jikinta, ta shiga wani dakin dake falon na farko tana shiga ta ga ba nan ba ne ta fito ta bude dayan dakin nan ma ba sha ba ne nan ma kuka ya ci karfinta ta durkusa tana kuka, laifi take dorawa kanta domin da ace bata biyewa so ba da yanzu Khaleefa be kaita ya baro ba domin shi ne silar faruwar komai. "Ba haka ake tarbar bako ba, abun da kika yi a yanzu kin kara jefata ne a damuwa kuma baki san iya halin data shiga ba, ba ita ta nemo ni ba ni nake ta kokarin shiga rayuwarta" Ta aje littafin dake hannunta. "I didn't ask her to leave, i didn't say she's not welcome, all what i asked her is who she is, ya kamata musan idan ya cancanci duk abubuwan nan da kake mata, kuma ya kamata mu san da amintacciya muke zaune" "Kina da gaskiya, amman ba a irin wannan lokacin da yanayin ya kamata ki yi wannan maganar ba, kina ganin ganin yarinyar nan kin san akwai damuwa a tare da ita, ni na san yadda damuwa take, ta kan saka mutum ya hauka ko ya fita hayyacinsa, wani ma baya iya bayyana matsalar sa saboda yana jin kamar ba za a fahimce shi ba, tun farkon haduwana da yarinyar nan Allah ya hada wata alaka mai karfi a jinina da nata, na ji ta yi min ta kwanta min a rai, and duk lokacin da zan sake haduwa da ita sai na karanci damuwa a tare da ita, shiyasa nake ta shiga rayuwarta saboda ma taimaka mata" "Aikinka shi ne duba masu damuwa ka ba su magani not to take their responsibility" "I thought you want me to get married? Ko da yaushe kina fadar kina son na canja, why all this now?" Ta yi shiru kawai tana kallonsa. Sai ya juya zai fice. "I'm sorry Son I'm sorry, bari na yi magana da ita a falo" "Already ta sauka, ba sai kin yi ba i will talk to her" "Bari na sauka da kaina na yi magana da ita" Ta mike tsaye ta aje littafin dake hannunta fice daga dakin ta fito falonta, ta sauka hawa na farko Dr A-B yana biye da ita, shi ya fara shiga dakin ya duba ya duba be ganta ba, ya leka bandaki bayan yayi knocking nan ma bata ciki sai ya fito ya duba sauran dakunan da suke jere da nan bata cikin ko daya ya sake sauka kasa gaba daya ya ya bude dakunan dake falon na kasa, yana bude daki na biyu ya same ta kwance a kasa tana hawaye. "Emily" Ta dago da sauri ta kalleshi tana jin zuciyarta na mata wani mugun ciwo. "Na manta dakin ne I'm sorry" Ya karasa inda take ya rikota ya mikar da ita tsaye, sai Momy ta karasa kusa da ita. "I'm sorry, bana nufin bata miki rai, ki yi hakuri na yi kuskure, amman ina fatan zaki fahimce ni bari na rakaki dakinki" Ta kama hannun suka fara tafiya. TURHAN POV. Shiru yake a jirgi har suka sauka, saboda ya bar zuciyarsa a gidan Ammy be tafi da ita ba, wato Fatima ko da ya bar gidan ma tana bachi bata san ya tafi ba, sai sumbantarta yayi ya dauki hotonta ya tafi shi ma baya son ta ga tafiyarsa tace zata bishi Ammy ta hana. Ya sauka airport din yayi waya aka zo aka dauke shi kamar yadda aka saba, sai dai abun da be saba ba shi ne fara ganin mahaifinsa bayan sauka gida, a yadda al'adarsa take idan ya dawo yana shiga bangarensa ya huta ne sannan ya fito gaishe da mahafinsa, amman wannan karon motar na isa masarautarsu ya umarce direban ya faka harabar fadar mahaifinsa, yana jin kamar ba shi da natsuwa idan be ji dalilin kiran da mahaifinsa yake masa ba. Ko da ya shiga fadar ya samu mahaifinsa da baki, haka ya zauna har sai da mahaifinsa ya samu sarari sannan ya doshi can cikin fadar bayan ya saka an sanar masa da bukatarsa ta son ganinsa. Kamin ya karasa Ammy ta kira wayarsa ta fada masa Fatima ta fara kuka saboda be dawo ba, ta mata karya cewar ba nesa ya tafi ba. "Kuka take ne?" "Eh tana tashi bachi dakinka ta fara lekawa ta fito baka ciki sai na fada mata ka tafi ka dawo, tun dazun take tambaya yanzu kuma ta fara kuka" "Bari na kira Video Call sai ki ba ni na yi magana da ita" Ya katse kiran ya kirata FaceTime sai ta kara masa Fatima dake kuka yayi magana da ita yana rarrashinta Ammy na fassara mata har ya samu ta yi shiru. Ya tabbatar mata da gobe zai dawo. "Idan ka dawo ba zaka sake tafiya ba?" "Eh, ba zan sake barinki ba Fatima na yi alkawari, i love you" "I love you too" "Zaka zo tare da momy? Zamu zauna a nan?" "Eh, zamu zauna a tare Fatima zamu zama Family daya" "Okay bye" Ta masa waving shi ma ya daga mata yana jin kamar yayi kuka domin yana matukar son yarinyar nan fiye da komai, sai da ya maida wayar aljihu sannan ya kunna kai a karamar fadar mahaifinsa cike da amsar tambayoyin da ya san mahaifinsa zai masa. _________ Ayi hakuri, muna biki ne. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [7/27, 8:34 PM] : https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 ABOKIN RAYUWA
Chapter 130 · 0% Book details