Sashe 2
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* To my big sis, Hajiya Habiba Muhammad, words are not enough to express your worth and my love for you. I pray that Allah grants you the highest place in Paradise, fulfills your desires, and answers your prayers. I'm speechless You're even more than I imagine Wallahi. I dedicate this book to you, Hajiya Habiba Muhammad. You mean more than words can express you are everything I could ever ask for in a big sister. You treat me like your own little sister I LOVE YOU deeply I couldn't introduce myself without mentioning you, Salma Ahmad Isah I cherish you Salma, nasan ke ma kin san haka. If anyone is looking for another version of me, they ll find it in you. NOTE... Labarin nan ya zo da sabon salo akwai abubuwa da yawa a ciki, sai mun taru mun yi hakuri sannan zamu iya isa gurin da nake son muje. Na san halinku abu kadan ku fara attacking mutum. Na fara rubuta labarin tun kamin na rubuta Hurriya, wani gari, da kuma taki zaman aure, amman Allah be ba ni ikon kammalawa shi ba sai yanzu, Allah ya ba mu ikon amfana da darasin da ke ciki.. Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye Page - 1 Bismillahir Rahmanir Raheem. Kai na daga sama ina kallon bakin hadarin da ya fara saukar da ruwa, iska mai karfi na kadawa kamar zata tashi gari. Mamy.. Mamy... Ahhhh ahhhh ahhhh Kasa na dawo da kaina na kalli saitin da dana yake, wanda ya kasance autism, sai ihu yake yana murza ido da nake kyautata zaton kasa ce ta shigar masa. Hawaye ne suka sauko min tare gumi, duk kuwa da kasancewar iska ne yake kadawa ko'ina, amman zafin nakudar yar da zan haifa ya tare duk wani jindadi da zai rabeni a lokacin. A hankali na dafa kangon dake gabana na jingina sai kuma na sulale kasa na zauna, sai ruwan sama ya fara saukowa, ana ya fara ihu na fitar hankali, nakuda ta sallamomin da gaggawa, gani ya fara min nisa, numfashina ya fara yin sama... Babu kowa a tare da ni, babu wanda yace Emily, ki yunkura zaki iya, babu mai fada min haka ake yi ba haka ake yi ba, ba ni da gatan da wani zai damu da ni balle ya kai ni asibiti, zan iya haihuwa da kaina ko sai an sake fasa ni CS kamar wacan karon? A haihuwar ana London haihuwata ta fari. Jin wani azababben zafi ya ratsa marata zuwa cinyata ya sakani ihu da dukanin karfina, a gurin da babu mai cetona. Sannu miya same ki? Ko haihuwa ce? Me kike yi a nan? Wacece ke? Na ji wata sabuwar murya, idanuwana suka yi arba da wata bakuwar fuska dake duke a gabana yana leken tawa fuskar, saukar ruwan sama da kuma zafin nakuda, ba su ba ni damar tantance waye tsugune a gabana ba. Na mika hannayena duka biyu na riko hannayensa ina numfashi daker, azabar nakuda ta hana ni magana. Subhanallahi... Christen ce ke? A kokarinsa na zare hannunsa daga nawa agogon hannunsa ya zame ya tsaya a hannuna sai na jimke agogon da karfi ina nishi mai karfi. Am... Akwai wanda kika sani nan kusa? Na girgiza kai alamar aa, to ni a kaf duniyar ma wa na sani balle kuma a kusa da ni. Okay zan kai ki asibiti yanzu nan... Danki ne wacan... Kai kawai nake iya daga masa, ni dai burina a taimake ni a raba ni da abun da nake ji a yanzu. Da alama maji karfi ne, domin cak na ji ya daga ni yana istigifari. Astagafullah Allah ka yafe min ba da niya na taba ta ba Ya saka ni a motarsa, be damu da lalacewar da jikina yayi ba, be damu da ihun da ana yake kamar zai fasa kunne ba, be damu da banbancin addininmu ba, be duba talaucina da arzikinsa ba, haka ya ja motar da karfi yana tukin yana min sannu, yi hakuri mun kusa karasawa asibitin, kai kace ni din yar'uwarsa... *** *** Karar bude kofar dakin da take ciki ne ya dawo da ita duniyar tunaninta. A hankali take shafa tsadaden agogon dake hannunta mai ruwan zinari, hawaye masu zafi na sauko mata. Emily... Ta daga kai ta kalli mai kiran sunan nata ta cikin madubin dake gabanta. Da sauri ya karaso kusa da ita ya tsaya yana kallonta, a cikin kallonsa akwai tashin hankali, akwai kauna, akwai tsoro, akwai fargaba da suka rufe shi lokaci daya saboda ganin hawayenta. Risinawa yayi kasa a yayinta take zaune agaban madubi mai cike da kayan kwalliya. Fari ne, mai yalwatacciyar bakar fuska mai kama da bakin hadari, kallo daya zaka masa ka fahimci annuri da far'a ba su da muhalli a fuskarsa, sai dai kuma shi din kyakkyawa ne, namiji ne mai kirar mazaje. Sarkar Cross ce a wuyansa irin wadda ke wuyanta, banbancin tashi da nata tata karama ce tashi kuma babba ce wanda ta cika kirjinsa dake dauke da zanen tattoo. Dubansa ya kai kan agogon dake hannunta a take ya kara hade rai. Har zuwa yaushe zaki daina dauko agogon nan dake tuna miki rayuwar baya? Ta kalleshi da idanuwanta masu matukar kyau da daukar hankali, da bakin da yayi daidai da tsarin fuskarta ta furta. Har zuwa lokacin da zan iya manta alheri Ta maida dubanta a gurin agogon da take jin kamar shi din ya taimaki rayuwarta, a lokacin da mutuwa ta so ta kusantota. Ko waye mai wannan agogon, yana da kirki, yana da tausayi, yana da kyakkyawar zuciya, shi din ya banbanta da sauran musulmi Zabura yayi kamar zai dake ta cikin ihu ya rufe ta fada. Babu banbanci tsakaninsu, babu banbanci tsakanin ko wane musulmi, kin gwada daya kin gwada biyu kin gani, baki bukatar wani ya baki labari, miye a cikin kanki? Meyasa kika kasa manta rayuwarki ta baya? Kina da komai yanzu, baki bukatar kowa I'm here for you and I Love you Ya rumgumeta daga tsayen da yake sai ta fashe da kuka ta rikeshi sosai. Bayanta ya shafa yana maida numfashi a hankali tare da rarrashinta. Kina da duk wani abun da kike mafarkin samu a yanzu Babe, kina da Luxury Home and Cars, kina da komai Babe Dagowa ta yi daga jikinsa ta share hawayenta ta bude aljihun madubin ta saka sarkar ta mike tsaye ta shiga bandanki ta wanke fuskarta, ta cikin madubin dake bandakin take kallon kanta. Ta canja, hallitarta ta sauya, halinta ya sake, kyauta ya ninku, kyaun jikinta ya bayyana. You can do this Emily, you have to do this, ke din a yanzu Emily ce ba wacan Emilyn ba, ke din a yanzu Emily ce, ba Aysha ba, jaruma ce baki bukatar kowa a kusa da ke Ta fadawa kanta domin karfafawa kanta guiwa, daman waye zai karfafa mata? Idan ba ita din kanta ba, turawa suka ce when you have no one to push you push yourself. Takawa ta yi baya tana cigaba da kallon kanta sannan ta dauke idonta ta kalli kofar bandakin, ta sauke ajiyar zuciya ta nufi kofar ta bude ta fita. Gaban madubin ta sake zaunawa ta fara shirya kanta, har ta yi kwalliyar ta gama Vito be ce mata komai ba yana zaune ya dora kafa daya saman daya, wayarsa a hannunsa sai dai duk abun da take jajayen idanuwansa suka kanta. Gurin da ta ware tufafin da zata saka ta nufa ta dauka ta nufi wani karamin daki ta canja tufafin sannan ta fito tana gyara gashinta dake hade da gashin doki attachment. Kin yi kyau Ya fada yana nufar gurin da take tsaye, ta yi kyau kam iyakar kyau, kyaun da ya wuce ayi mata kallo daya a dauke ido, yadda aka tsara hallitar fuskarta da kirar jikinta, kai kace ma ita ta yi kanta. Ban san miyasa kika dage sai kin yi aiki ba, ban san manufar da kike son cin ma ba, na wadata ki da kudi, ban san miya hana zuciyarki natsuwa da hakan ba, arzikin da zaki je nema a wani gurin be taka kara ya karya na arzikin da na aje miki a nan ba, amman dai ko miye, zan goya miki baya saboda ina sonki ina son farincikinki sosai Magana yake yana zagayeta kamar mai tantance komai na jikinta. Ba arziki nake nema ba, so nake kawai na yi rayuwa irin na sauran mutane, ka canja ni kuma na canju, na watsar da komai ina rayuwa ne irin na mutane, karka ji tsoro Ya tsaya daidai fuskarta har numfashinsa yana gauraya da nata. Vito be san tsoro ba, amman shi tsoro ya san Vito shiyasa idan ya gan ni yake boya, you belong to me karki manta wannan Ya sumbance ta. Wish you all the best, fatar ki fara aiki a sa'a i love you, good luck on your new Job Ya mata murmushi kadan ya shafa fuskarta sannan ya dauke hannunsa ya fice. Tsaye ta yi a gurin na wasu dakiku, sannan ta busar da iskar bakinta ta nufi wayarta da jakarta ta dauka ta fice daga dakin zuwa bangaren da anta yake. TURHAN POV. Baka tafi ba har yanzu? Ya mike tsaye yana kallonta idanuwa a raunace fuska dauke da damuwa. Ammy... Sai kuma ya kasa furta komai saboda yadda ta tsare shi da wani kallo irin na horo daga uwa zuwa ga danta. Zamanka ba shi da amfani a nan, kasan ba zan taba barinka ka kwana a gidana ba, toh ba amfanin bata wuni Ya bude baki sai kuma ya maida ya rufe a hankali ya taka zuwa kusa da mahaifiyarsa. Ammy I'm sorry, na yi nadama kin sani, na tuba ki yi hakuri ki yafe min Ya durkusa kasa ya rike hannayenta. Me zan yi ki yafe min Ammy? Me zan yi ki yarda na yi nadama? Nadamar ka ba zata gyara abun da ka bata ba, ni ban kullace da komai ba, kawai alaka ce irin ta da na yanke Ammy mi