Sashe 75
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
kina karkashin ikona dole ne na san a duk halin da kike ciki" Ta juyo a fusace "Wai duk wannan gatan da wannan kulawar da ka ba ni ka bani ne saboda ka yi iko da ni? Ka juya ni yadda kake so? Da zarar na yi abu sai kace ina karkashin ikonka bauwa ce ni? Nawa ka biya ka siye ni?" "Babu kudin da zai siye ki a duniyar nan Emily, ina kulawa da shiga da fitarki ne saboda ke Matata ce" "I'm not your wife, ni ba matarka bace ba matar kowa ba ce, and i need another maid bana son Chidimma" Chidimma ta kalli Vito tana girgiza masa kai idonta na cika da hawaye. "Dan Allah karku koreni aikin nan da shi kadai na dogara da shi nake komai na rayuwata" Emily ta dauke kai ta fice rike da abincin, motarta ta koma ta shiga ta dauki hanyar asibitin domin kaiwa Tasmia abun karyawa, bayan bacin ran Aliyu na zarfinta da abun da bata aikata ba, yanzu kuma Vito ya kara mata da shi. Ta faka motar a harabar da aka tanada domin aje ababen hawa sannan ta fito rike abincin ta nufi cikin asibitin, tana tafe ranta da fuskarta a bace kamar zata yi kuka. "Da alama kin fini tsada, shiyasa baki nemi ni ba" Ta karkato kadan ta kalli gefenta sai ta yi arba da fuskar likita daya taba bata katinsa saboda rashin lafiyar London, tare da wani likita a gefensa. "Hi" "Hi, ashe kin gane ni" Ta yi murmushi. "Wacan karon na manta ban tambaye ki ba, are you married? Kar mijinki ya fasa min kai" "No" "Cool, ya mai jikin?" "Ai ya rasu" Ta fada cikin wani yanayi marar dadi idonta na son tara hawaye. "Ayyah... I'm sorry" Ya fada cike da tausayawa. Ta sauke kanta kasa ta cigaba da tafiya har suka isa gurin da zai shiga. "This Way Ma'am" Ta kalli hanyar da zai bi. "No ni nan zan bi, akwai wata kawata da bata da lafiya ita na kawoma abinci" "Toh kuma ba zaki so mu gaisa ba" "Mun gaisa a nan ai?" "Asibitin tana da mutane da yawa, ba zai yayu na siyar da ke ba, ni ma akan hanya nake nan da minti arba'in zan bar garinku" Ya fada yana kallon agogo hannunsa. "Da alama baki san waye Dr A-B ba ki zo kawai ku gaisa" Likitan dake tare da shi ya fada, a yanzu kuma Emily bata da wani zabi daya wuce ta yi abun da ya kamata even though bata san makasudinsa na son hakan ba. Da suka jera suna tafiya yake fadar. "Daman alamu sun nuna min baki da aure, amman na yi tunanin mutumen da ya saka aka nemo ni na duba yaronki shi zaki aura" "Aa" "Kin yaudare shi k enan" "Aa ni bana soyayya da kowa, babu zancen aure a gabana ba zan sake yin aure ba balle na yaudari wani" Ya dan tabe baki kadan. "Ihhh da Alama yan'uwa rijalu sun dandana miki gubar soyayya, kin huta ai, ni ma dai ba a dandana min gubar ba amman soyayya bata burge ni, shiyasa mutane har mamaki suke wai ina da shekara 37 na doshi arba'in kuma ban yi aure ba" Ya bude mata kofar Office din da za su shiga sannan ya tsaya. "Ladies First" Sai da ta fara shiga sannan ya shigo, kana ganin Office din ka san ba na shi ba ne, amman a haka yayi mata gurin zama. [6/3, 8:23 PM] ABOKIN RAYUWA